You are here: HomeAfricaBBC2021 08 12Article 1331077

BBC Hausa of Thursday, 12 August 2021

    

Source: BBC

Mutum 790 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Maaikatan laafiya cikin kayan aiki Maaikatan laafiya cikin kayan aiki

Alkaluman baya baya nan na hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa sun nuna cewa mutun sama da 790 ne suka kamu da cutar korona a daukacin kasar .

Bayanan da ta walafa a shafinta na Facebook hukumar a ranar Laraba sun nuna cewa mutun 574 ne suka kamu da cutar a jihar Lagos, sai jihar Ribas nada mutum 83 ya yinda jihar Ondo ke da mutum 31.

Sauran sun hada da jihar Ogun mai mutun 31 da jihar Oyo mai mutum 23 sai jihar Delta nada mutum 10 ya yinda birnin tarayyar Abuna na da mutun 10.

Jihar Ekiti na da mutum 7, Edi na binta a baya da mutum 6, sai jihar Osun nada mutum 4 ya yinda Anambra da Bayelsa nada mutum 2 kowanensu, sai jihar Flato nada mutum 1.

A cikin baya baya nan ba a samu wani da ya harbu da cutar a jihohon Kano da Nasarawa da kuma Sokoto ba

A halin yanzu adadin wadanda aka tabattar cewa sun kamu da cutar a daukacin kasar ya kai dubu dari 179,908 m ya yin da an salami sama da dubu 166 daga asibiti

Read full article