BBC Hausa of Sunday, 2 July 2023
Source: BBC
"Na samu nasarar karɓar haihuwar sama da jarirai 10,000. Dukkan su haihuwa ce da aka saba a al'adance, kuma ba a taɓa samun mutuwar jariri a wajena ba."
Kathija Bibi ce ta bayyana hakan a lokacin da take waiwaye a kan aikin da ta kwashe shekara 33 tana yi na taimakon mata a lokacin da suka fi buƙatar taimakon.
A lokacin da take aiki, Ƙasar Indiya ta yi ƙaurin suna wajen yawan mace-macen mata a lokacin haihuwa, inda adadin mutuwar a ƙasar kadai ya kusa da matsakaicin jimillar na duniya.
Haka kuma ta kasance mace mai shauƙin ganin 'yan mata sun samu 'yancin da suke buƙata ba tare da ana wofantar da su ba.
Kathija ta kasance mai ɗauke da juna biyu a lokacin da ta fara aiki a Cibiyar Lafiya ta gwamnati a Kudancin Indiya a shekarar 1990.
"A lokacin ina ɗauke ne da cikin wata bakwai… amma duk da haka ina taimakon wasu matan. Haka kuma na yanke hutuna na bayan haihuwa cikin sauri, inda na yi wata biyu kawai."
Kathija ta ƙara da cewa, "Na san damuwar da mata suke shiga a lokacin da suke naƙuda. Hakan ya sa na ci burin ganin ina kwantar musu hankali da ba su tabbaci."
Nas din wadda tsayinta ya ɗara mita 1.5, tana da natsuwa sosai. Asibitinta yana birnin Villupuram ne mai nisan kilomita 150 a Kudu da Chennai, a Jihar Tamil Nadu. Ba ta da kayan aikin yin tiyata, wanda hakan ya sa take aika masu juna biyun da ta gano akwai matsala cikin gaggawa zuwa babban asibitin yankin.
'Yar gado
Kathija ta samu ƙwarin gwiwa ne daga mahaifiyarta, Zulaika, wadda ita ma nas ce da ta yi aiki a ƙauyen.
"Tun ina ƙarama nake wasa da allura. Haka kuma tun ina ƙarama na saba da asibiti."
Tun tana ƙarama ta fahimci muhimmancin aikin da mahaifiyarta ke yi na taimakon mata marasa ƙarfi.
A lokacin, ba a cika samun asibitocin kuɗi ba, sannan kusan dukkan mata suna ta'allaka ne da asibitin karɓar haihuwa mallakar gwamnati.
"Lokacin da na fara aiki, likita ɗaya ne kawai da nas biyu, sai mataimaka guda bakwai," in ji Kathija. "Aikin sai ya kasance yana da wahala a farko-farkon zuwana. Aikin ya sa na gaza ɗaukar ɗawainiyar yarana yadda ya kamata. Na kuma daina iya gudanar da wasu ɗawainiyar gida. Amma waɗannan ranakun na farko-farkon ne suka taimaka min wajen samun nasara."
A shekarar 1990, adadin mace-macen mata wajen haihuwa a Indiya ya kai mutuwa 556 a cikin duk haihuwa 100,000.
A shekarar kaɗai, an samu mutuwar jarirai 88 a cikin haihuwa 1,000.
Ƙididdigar kusa-kusa na gwamnati ta nuna cewa ana samun mace-macen mata wajen haihuwa guda 97 a cikin haihuwa 100,000, ita kuma mutuwar jariran ya kai mutuwa 27 a cikin haihuwa 1,000.
Kathija ta ce an samu wannan nasarar ce saboda yadda gwamnati ta mayar da hankali ta hanyar zuba kuɗi wajen inganta cibiyoyin lafiyar karkara da kuma ilimantar da mata.
Ta kasance gaba-gaba wajen gudanar da waɗannan ayyuka na gwamnati.
A kullum Kathija takan karɓi haihuwa ɗaya ko biyu, amma tana yawan tuna ranar da ta fi shan wahala. "Ranar 8 ga Maris ta shekarar 2000 ce ranar da na fi shan wahala a rayuwata."
Ranar ta dace da Ranar Mata ta Duniya, sai ta ga mata suna ta gaishe ta a lokacin da take shiga asibiti.
"Sai na samu mata biyu a ɗakin karɓar haihuwa suna jirana. Bayan na samu nasara sun haihu lafiya, sai ga wasu guda shida sun shigo."
A lokacin mataimakiya ɗaya kawai Kathija ta samu, amma tuni ta bar batun wahalar da ta sha a ranar. "A daidai lokacin da nake ƙoƙarin tashi daga aiki a ranar, ina tuna yadda 'Na rika jin kukan jarirai. Jin wannan kukan ya faranta min rai. A lokacin akwai wasu a waje suna jira, ganin yadda 'yan uwansu suka sauka lafiya ya jefa su cikin farin ciki."
Nas din ta bayyana cewa ta taimaka wajen haihuwar tagwaye 50 da 'yan uku ɗaya.
A farkon shekarun 1990 ne wata mai ciki babba ta zo tana kuka. A lokacin Kathija ta sha ko tagwaye ne, amma kuma babu na'urar ɗaukar hoton ciki a asibitin nata.
"Mintuna kaɗan bayan haihuwar na farko, sai matar ta sake haihuwa." A lokacin da Kathija ta je wanke jariran, sai mahaifiyar ta fara ihun zafin wani naƙudan.
"Sai na shiga mamaki saboda ban taɓa karɓar haihuwar 'yan uku ba, kuma ban shirya ba'' in ji ta. " Kuma a lokacin ba zai yiwu ba a tura su babban asibitin yankin saboda yanayin da take ciki."
Sai Kathija ta fara shafa kan matar a hankali domin ta kwantar mata da hankali har jaririn na uku ya fito.
Hukomomi a yankin sun tabbatar da tarihin da Kathija ta kafa na karbar haihuwa 10,000, har karramawa ta musamman Babban Minista ya mata.
Zafi da rashi
Kathija ta ce yanzu matan masu hannu da shuni sun fi zuwa asibitocin kudi, sannan akwai wata dabi'ar zaɓar a musu tiyata da mata ke yi da kansu.
"A zamanin mahaifiyata an samu mace-mace wajen haihuwa. Yin tiyata ya taimaka wajen tseratar da wasu," in ji Kathija. "A lokacin da na fara aiki, mata suna matukar fargabar a musu tiyata, amma yanzu wasu da kansu suke cewa a musu tiyata."
Ta ga zahiri a lokacin da surukarta za ta haihu, inda ta bukaci a yi mata tiyata kawai a cire jaririn duk kuwa da cewa za ta iya haihuwa da kanta.
"Har yanzu ina da tunanin da na karba haihuwar, da ba sai an yi tiyata ba. Amma ba na zargin likitoci ko ma'aikatan lafiya. Ina tunanin akwai haihuwa da dama da ba sai an yi tiyata ba, domin za su iya haihuwa da kansu idan suka samu kulawar da ta dace."
A daidai lokacin da tattalin arziƙin mutanen karkara ya inganta a tsakanin shekara 30 da suka gabata, shi ma ya zo da tasa matsalar. "A da ba a cika samun ciwon sukarin masu juna biyu ba. Amma yanzu ya fara zama ruwan dare."
A wani yanayi na sauyi da mamaki, yanzu maza da kansu suke rako matansu asibitin."Na ga abubuwa masu kyau da marasa kyau. Wasu maza ko ziyarar matan ba sa yi idan ta haifi mace. Wasu matan za ka ga suna kuka sosai idan sun haifo mata a karo na biyu ko na uku.
A shekarun 1990, an samu labaran zubar da ciki saboda kasancewa abin da za a haifa mace ce, ta yadda dole gwamnati ta hana likitoci bayyana wa iyayen jinsin 'ya'yansu.
Gwamnatin Tamil Nadu ta kuma assasa shirin 'Cradle Baby Scheme' domin kula da yaran da iyayensu suka ce ba sa so. "Amma yanzu lamarin ya canja," inji Kathija.
"Iyali da dama suna son haihuwar 'ya'ya biyu ne kawai, amma babu ruwansu da zaɓin ko mace ce ko namiji."
Mijin Kathija ya rasu shekara bakwai da suka gabata. Yarinyarta tana aikin injiniyar kwamfuta, namijin kuma Injiniya ne a Dubai. Surukar Kathija, Monisha kuma ta nuna tana son ta ga ta karar da sauran rayuwarta ne tare da jikokinta.
Kathija ba ta da tsayayyen shiri lokacin da ta yi ritaya a ranar 30 ga Yuni tana da shekara 60, amma ta san cewa za ta yi kewa.
"Ina matukar sha'awar jin kukan jarirai," in ji ta.
"Na san duk macen da ta san zafin nakuda, suna manta komai da zarar sun ji kukan jarirai. Ganin wannan farin cikin shi ma abu ne da ba zan manta da shi ba. Na ji dadin duk lokacin fa na kwashe ina aikin."