BBC Hausa of Tuesday, 28 March 2023
Source: BBC
Julian Nagelsmann yana daga cikin wanda ake cewar zai maye gurbin Antonio Conte a Tottenham in ji wani rahoto.
The Daily Mail ta wallafa cewar shugaban Tottenham, Daniel Levy na son tattaunawa da tsohon kociyan Bayern Munich, don yi masa tayin kwantiragi.
Ranar Juma'a Bayern Munich ta kori Nagelsman, sannan ta maye gurbinsa da Thomas Tuchel, wanda Chelsea ta sallama a kakar nan.
Ranar Lahadi Tottenham ta raba gari tsakaninta da Conte, tsohon kociyan Chelsea da Inter Milan.
Kociyan ya yi hira da 'yan jarida, bayan tashi wasan Premier League da suka yi 3-3 da Southampton ranar Asabar, kuma Tottenham ce ta fara cin 3-1.
Conte ya ce 'yan wasan suna da son kansu, ba sa saka kwazo a karawar da ke da kalubale, sannan ya caccaki Tottenhma ita kanta.
Kawo yanzu kungiyar ta nada mataimakin koci, Cristian Stellini, wanda zai ja ragamar Tottenham zuwa karshen kakar bana.
Wasu kuma na cewar Mauricio Pochettino ne zai sake komawa kungiyar.
Dan kasar Argentina ya horar da Tottenham tsakanin 2014 zuwa 2019, wanda ya kai kungiyar wasan karshe a Champions League a 2019.