You are here: HomeAfricaBBC2022 04 04Article 1506773

BBC Hausa of Monday, 4 April 2022

    

Source: BBC

Najeriya: An cika mako guda da kai harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja

Jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa hari Jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa hari

An cika mako ɗaya da kai harin jirgin ƙasan zuwa Kaduna daga Abuja, wanda ya yi sanadin mutuwar fasinjoji, da sace wasu waɗanda har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadinsu ba.

Makusanta da dangin fasinjojin na ci gaba da zaman zullumi, yayin da a karshen makon nan hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta kasar ta tabbatar cewa fasinjoji fiye da 170 ne suka kuɓuta daga harin.

A lokaci guda kuma, hukumar ta ce jami'anta na ci gaba da aikin gyaran titin jirgin ƙasan mai zuwa Kaduna daga Abuja.

Cikin wata sanarwa, hukumar ta ce sun kai kayan aiki da ma'aikata wajen da aka kai harin in da ake ci gaba da aikin gyaran layin dogon.

A cewar hukumar, a ci gaba da kokari ta hanyar kiraye-kirayen waya, an tabbatar da fasinjoji 170 na nan lafiya.

Yayin da fasinjoji 21 ne, 'yan uwansu suka bada rahoton sun bata.

Jirgin kasan dai na dauke da fasinjoji 362, in ji hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasan.

To sai dai kuma babu wani karin bayani game da fasinjoji fiye da 180, kuma sanarwar ba ta bayyana cewa ko fasinjojin bata suka yi ko kuma suna hannun 'yan bindiga ba.

Hukumar kula da sufurin jirgin kasan ta ce taragan da suka fadi sakamakon harin, kawo yanzu an tayar da wasu daga cikinsu tare da dorasu a kan layin dogon da aka gyara.

Sanarwar ta ce, da hadin gwiwar jami'an tsaro, hukumar kula da sufurin jirgin kasan bisa umarnin shugaban kasa, na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da ceto wadanda suka bata sakamakon harin.

Karin bayani

Harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin din da ta wuce da daddare ya tayar da hankalin ƴan Najeriya tare da sanya fargaba a zuƙatan mutane da dama.

Wannan batu ya zama matsalar tsaro ta baya-bayan nan mafi muni da ta faru a Najeriya da kuma ta ɗimauta mutane.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama jigo mai sada miliyoyin mutane da arewacin ƙasar daga babban birnin tarayya Abuja da kuma kudanci.

Hakan ne ya sa mutane suka fi raja'a da bin jirgin ƙasan ganin yadda ya zama wata hanyar sufuri da mutane suke ganin ita ce mafi tsaro, fiye da bin hanyar mota, yayin da jirgin sama kuma ya yi tsadar da sai masu ido da kwalli ne za su iya biya.

Read full article