You are here: HomeAfricaBBC2023 01 29Article 1704203

BBC Hausa of Sunday, 29 January 2023

    

Source: BBC

Novak Djokovic ya lashe kofin Australian Open

Novak Djokovic Novak Djokovic

Novak Djokovic ya lashe kofin Australian Open karo na 10 a tarihi, bayan da ya doke Stefano Tsitsipas.

Wasan ya tashi 6-3, 7-6, 7-6 da kuma 7-5.

A yanzu dan kasar Serbia din ya kamo Rafael Nadal wurin cin manyan kofuna na Grand Slams, inda shima ya lashe na 22.

Dan kasar Girka Tsitsipas zai cigaba da jiran babban kofinsa na farko.

Djokovic zai dawo matsayinsa na farko da ya rasa a baya.

Ya rasa matsayin nasa a bara, bayan da ya ki amincewa a yi masa allurar rigakafin korona kafin ya buga gasar ta Australian Open.

Read full article