You are here: HomeAfricaBBC2022 04 25Article 1523525

BBC Hausa of Monday, 25 April 2022

    

Source: BBC

Paris St Germain ta lashe Ligue 1 na bana duk da sauran wasanni

Paris St Germain ta lashe Ligue 1 na bana Paris St Germain ta lashe Ligue 1 na bana

Paris St Germain ta lashe Ligue 1 na bana, bayan da ta tashi 1-1 da RC Lens a wasan mako na 34 ranar Asabar.

Lionel Messi ya fara cin kwallo a minti na 68, daga baya Lens ta farke ta hannun Corentin Jean saura minti biyu a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon PSG ta lashe na 10 jumulla iri daya da yawan na St-Etienne a lashe kofin babbar gasar tamaula ta Faransa a tarihi.

Tun kan a tashi wasan magoya bayan PSG suka fice daga filin wasan, inda suka yi bikin lashe kofin da suka yi a wajen filin tamaula.

A bara PSG ta biyu ta yi a Ligue 1, bayan da Lille ta lashe kofin da tazarar maki daya kwal tsakaninsu.

Sai dai kuma a 2021-22, PSG ta yi nasarar daukar kofin da tazarar maki 16 tsakaninta da Marseille ta biyu, kuma saura wasa hudu a karkare kakar nan.

Haka kuma kungiyar ta ci gaba da yin wasanni a Ligue 1 ba tare da an doke ta ba, wadda ta yi nasara a fafawa 15 a karawa 17 kawo yanzu.

Kenan Mauricio Pochettino, wanda ya maye gurbin Thomas Tuchel a PSG a Janairun 2021 ya lashe French Cup da Trophee des Champions a kakarsa ta farko.

Sai dai kocin na fuskantar matsi a kungiyar, wanda aka yi ta alakanta shi da komawa Manchester United, wadda ta sanar da daukar Erik ten Hag.

Ana jiran matakin da shugaban PSG, Naseer Al-Kaelaifi zai dauka, bayan da kungiyar ke fatan ganin kocin da zai daukar mata Champions League.

Real Madrid ce ta yi waje da PSG a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai ta bana.

Read full article