You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767608

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

    

Source: BBC

Pogba ya kara jin rauni a karon farko da Juve ta fara wasa da shi

Paul Pogba ya ji rauni a karawar farko da Juventus ta fara wasa da shi a kakar nan Paul Pogba ya ji rauni a karawar farko da Juventus ta fara wasa da shi a kakar nan

Paul Pogba ya ji rauni a karawar farko da Juventus ta fara wasa da shi a kakar nan, wadda ta doke Cremonese ranar Lahadi.

Pogba mai shekara 30 ya ji raunin a minti na 24 da fara wasa a gasar ta Serie A, inda dan kwallon Faransa ya rufe fuska yana kuka a wasan da Juve ta ci 2-0.

Shine karon farko da Pogba aka fara wasa da shi tun bayan fafatawar da ya buga wa Manchester United da Liverpool a Afirilun 2022.

A fafatawar ce ya ji raunin da ya yi jinya zuwa karshen kakar tamaula.

Bayan da ya koma Juve, Pogba ya ji rauni a gwiwar kafa a lokacin atisaye a kungiya, wanda bai yadda aka yi masa aiki ba don kada ya kasa zuwa kofin duniya.

Daga baya ya amince likitoci su yi masa tiyata, wanda ya fara motsa jiki a cikin Janairu, amma ya fama rauni da ya kasa warkewa a kan kari.

Ya fara buga wa Juventus kwallo ranar 28 ga watan Fabrairu.

Juventus ta ajiye shi daga buga Europa League, bayan wasa da Freiburg cikin Maris, daga nan Pogba ya kara jin rauni a wajen atisaye lokacin da zai yi bugun tazara.

Ya yi zaman benci a fafatawa da Sporting Lisbon ranar 13 ga watan Afirilu, wanda ya canji dan wasa karo tara jimilla, shine aka fara wasa da shi Cremonese ranar Lahadi.

Read full article