BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023
Source: BBC
Matakin da hukumar zaɓen Najeriya ta ɗauka na ɗage zaɓen gwamnoni da 'yan majalisun dokoki na jihohi ya ɗauki hankalin 'yan ƙasar da kuma shammatar jam‘iyyun siyasa.
Ra'ayoyin sun bambanta dangane da matakin na INEC na ɗage ranar zaɓe daga ranar Asabar 11 ga watan Maris zuwa 18 ga watan Maris na wannan shekarar.
Yayin da wasu jam‘iyyun ke cewa tura zaɓen gaba ya katse musu hanzari, wasu kuwa cewa suke za su samu damar ƙara shiri.
Ɗage ranar zaɓen za a iya cewa ta zo wa jam‘iyyun siyasar da ‘yan takarar gwamna ba zato ba tsammani.
Musamman ma ana saura kwana uku a yi zaɓe, kasancewar tuni da dama suka yi nisa a shirin da suka yi na tura wakilansu zuwa rumfuna a zaɓen gwamnan, kamar yadda hukukar zaɓen Najeriyar ta tsara tun da farko za a yi.
BBC ta tuntuɓi jam’iyyar hamayya ta Labour wadda ɗan takararta na shugaban ƙasa Peter Obi a zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu ya zo na uku a sakamakon da INEC ta fitar, amma kuma ya ce shi ya ci zaɓen tare da garzayawa kotu da nufin abin da ya ce sake ƙwato nasarar.
A ƙarar da ɗan takarar da jam’iyyarsa suka shigar sun ɓukaci hukumar zaɓe ta ba su dukkanin kayan da ta yi amfani da su wajen zaɓen domin su duba, kuma kotun ta umarci INEC ta ba su.
To amma kuma hukumar zaɓen ta katse mutsu hanzari inda ita ma ta shigar da ƙara ta nemi kotu ta ba ta damar sake daidaita na’urar BVAS domin shirya gudanar da zaɓen gwamnoni da yan majalisar jihohi, buƙatar da ita ma kotun ta ba ta.
Sai dai kuma batun bai wa jam’iyyar ta Labour wannan na’ura ta BVAS abu ne na taƙaddama kasancewar INEC ta ce hakan zai saɓa wa wata doka cikin dokokin zaɓen ƙasar domin a cikin na’urar za a iya ganin sirrin waɗanda suka kaɗa ƙuri’a a jam’iyyar da suka zaɓa.
A dangane da batun ɗage zaɓen BBC ta ji ta bakin shugaban jam’iyyar Labour ɗin na ƙasa Dakta Tanko Yunusa, inda ya zargi hukumar zaɓen ta Najeriya da wata maƙarƙashiya.
Ya ce, INEC ta yi hakan ne saboda abin da ya kira gagarumin maguɗin da ta yi a zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisun dokokin tarayya kuma tana son ɓoye gaskiyar lamari.
Ya ce hujjar da hukumar zaɓen ta bayar cewa ta ɗaga zaɓen ne domin ta samu damar sake daidaita na’urar BVAS da aka yi amfani da ita, yaudara ce:
‘’Domin tun da farko ai ba su ce za a sake daidaita na’urar ba bayan zaɓe, sai yanzu ne ana saura kwanaki a yi wasu zaɓukan za su faɗi haka?’’
Sai dai kuma shugaban ya ce, in dai har kamar yadda INEC ta ce za ta adana duk abubuwan da ke cikin na’urar ba matsala domin su dai suna da sakamakon zaɓensu a hannu na duk ƙasar baki ɗaya.
Ita ma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, wadda ɗan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar ya shigar da ƙara kan sakamakon zaɓen, wanda shi ma ya ce an yi musu maguɗi, dole kowa ya ƙalubalanci sakamakon ta bayyana matsayarta kan ɗagewar.
Shi ma dai Atikun da jam'iyyarsa ta PDP kotu ta ba su irin waccan dama da ta bai wa LP ta duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaɓen da ya gabata.
BBC ta tattauna da ɗaya daga cikin manyan masu magana da yawun jam’iyyar Mallam Ladan Salihu, inda ya ce ba shakka akwai yanayi da zai iya tasowa hukuma ta ɗage zaɓe.
Ya ce dalilai irin su barazana ga zaman lafiya da matsaloli na zagon-ƙasa idan aka yi hakan da kyakkyawar niyya to ba matsala.
To amma ya ce matsalar a wannan ɗagewar da aka yi su suna cikin wani hali na ga ba kura baya sayaki – ‘’domin idan ka ce ba ka yarda da ɗagewar ba sai a yi maka wata fassara, saboda haka ba ka da wani abu illa ka sa ido ka ga abin da ake nufi.
Mallam Ladan ya ce ba sa so su saki jiki ne kamar yadda suka yi a baya sun sa ran hukumar zaɓen za ta yi gaskiya da adalci sai suka gamu da saɓanin haka a cewarsa.
Ya ce za su zuba ido su gani ko da alamar lauje cikin naɗi, ‘’ idan sun ɗage zaɓen ne domin jam’iyya mai mulki ta samu dama ta shirya wani maguɗi ko wani abu za mu gani.’’
Ita kuwa jam’iyya mai mulki APC wadda ɗan takararta Bola Ahmed Tinubu ya ci zaɓen shugaban ƙasa, ta bakin ɗaya daga cikin masu magana da yawunta, Bala Ibrahim ta ce, ɗage zaɓen bai zo mata da mamaki ba kasancewar daman akwai ƙishin-ƙishin ɗin hakan.
Ya ce ko alama matakin ba zai sanyaya musu gwiwa ba duk da cewa daman sun shirya tsaf domin zaɓukan na gwamnoni da kuma majalisun jihohi.
Kan batun zargin cewa matakin ko wata dabara ce ta taimaka wa APC, ganin yadda sakamakon wasu jihohi na zaɓen shugaban ƙasa ya kasance, sai ya ce daman su burinsu ba wai su cinye duk ba ne.
‘’Burinmu ba wai mu cinye jiha ba ne gaba ɗaya, abin da ake buƙata ka samu kashin da ake so, bayan ka yi nasara a wasu jihohin.’’
Ya ce kowa da irin dabarun da yake yi kamar yadda suka yi a zaɓukan da aka yi na shugaban ƙasa haka wannan ma saboda ɗaga zaɓen ba za su karaya ba, za su san yadda za su ɓullo wa lamarin.
Sai dai wasu jam‘iyyyun kuma sun bayyana cewa ba shakkar a ƙara suke yi ba, amma ɗage zaɓen zai ba su damar ƙara shiri, kasancewar akwai wasu ɓangarorin da ba su taɓa ba a baya.
Irin wannan ɗage zaɓe ana jajiberensa, kamar yadda masana siyasa ke cewa yana ƙara wa jam‘iyyu da ‘yan takara ɗawainiya, saboda sukan kashe kuɗi mai yawa wajen hada kan wakilai ko waɗanda za su yi musu aikin sa-ido a rumfunan zaɓe,
Kuma kasancewar an ɗage zaɓen sai sun sake shiri na sake haɗa kan wakilan nasu a nan gaba.
A ranar Laraba 8 ga watan Maris, wato na saura kwana uku zaɓukan, da daddare aka fara yaɗa jita-jita cewa an ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohin da aka tsara yi daga ranar 11 ga watan Maris zuwa 18 ga watan.
Sai daga baya ne kuma hukumar zaɓen ta fito ta tabbatar da ɗagewar bayan jita-jitar ta karaɗe shafukan intanet.
A sanarwar da ta fitar ta ce ta yi hakan ne kamar yadda ta ce, bayan ta fahinci cewa ba za ta iya sake daidaita na‘urorinta na tantance masu zaɓe har a yi zaɓen a ranar Asabar 11 ga watan Maris ɗin ba.
Kamar yadda hukumar ta bayyana, ta yi jinkirin fara daidaita na‘urorin ne sakamakon ƙarar da wasu jam‘iyyun hamayya suka kai kotu, suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala kwanan nan,
Waɗanda a cikin buƙatun da suka gabatar a ƙarar, suka nemi kotu ta hana hukumar zaɓen taɓa bayanan da ke cikin na‘urorin.
Ana hakan ne sai ranar Laraba 8 ga watan na Maris ana saura kwana uku zaɓen, kotun ɗaukaka ƙara a Najeriyar ta yanke hukuncin amince wa hukumar zaɓen ta ci gaba da daidaita na‘urorin.