You are here: HomeAfricaBBC2021 10 13Article 1379416

BBC Hausa of Wednesday, 13 October 2021

    

Source: BBC

Raphael Varane: Dan wasan Manchester United zai yi jinya

Raphael Varane, dan kwallon Manchester United Raphael Varane, dan kwallon Manchester United

Mai tsaron bayan Manchester United, Raphael Varane zai yi jinya, bayan raunin da ya ji a lokacin buga wa Faransa tamaula.

Dan wasan ya ji rauni ne a karawar da Faransa ta lashe Natuions League, bayan da ta doke Sifaniya 2-1 ranar Lahadi.

Mai shekara 28 ya buga wa United karawa shida, tun bayan da ya koma kungiyar da taka leda daga Real Madrid cikin watan Agusta.

Tuni dai koci, Ole Gunnar Solskjaer ke buga wasanni ba tare da kyaftin Harry Maqire ba, wanda ke jinya.

United za ta ziyarci Leicester City a wasan mako na takwas a gasar Premier League da za su kara ranar Asabar.

Haka kuma kungiyar ta Solskjaer za ta fuskanci wasanni masu zafi da za ta kara da Liverpool da Tottenham da kuma Manchester City a Premier, sannan ta fafata da Atalanta a Champions League.

Read full article