You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837703

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

    

Source: BBC

Rashin cunkoso a titunan Legas asara ce ga Najeriya

File photo File photo

Birnin Legas ya zama daban, kacaniya da hayaniyar da aka san birnin kasuwancin na Najeriya da su sun ragu saboda cire tallafin man fetur.

Tun daga watan Yuni, farashin man fetur ya ninka sau uku, abin da ya jawo hauhawar kuɗin sufuri da kuma tilasta wa wasu ma'aikata yin aiki daga gida.

Akasarin mutane sun daina hawa motocinsu. Saboda ƙarancin fasinjoji, yanzu motocin bas masu launin ɗorawa da ake haya da su na jingine a tashoshi.

Tuni dogayen layukan mota suka ragu sosai a birnin.

Wannan birnin mai yawan al'ummar da aka yi hasashe sun kai miliyan 20 yanzu shuru yake, amma kuma hakan ba abu ne mai kyau ba.

Nutuswar da Legas ya samu ta sa ya yi rashi a ɓangaren tattalin arziki tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin bagatatan a ƙarshen watan Mayu.

Ya ce Najeriya mai arzikin fetur ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗin tallafi ba, wanda ke lashe biliyoyin naira duk wata.

  • Ko sauya mota daga mai amfani da man fetur zuwa gas na da illa?


  • CIre tallafi da kuma cire takunkumin canjin kuɗi ya jawo wa tattalin arzikin ƙasar matsaloli, duk da cewa masana na cewa matakai ne da suka dace, kuma babu inda lamarin ya fi ƙamari fiye da Legas.

    Da yawa daga cikin masu ƙananan sana'o'i sun daina, kuma wasu daga cikin mazauna unguwannin wajen Legas da ke shiga birnin don yin ayyuka a kullum sun daina zuwa.

    "A baya nakan kashe naira 600 wajen sufuri, sai ya koma 1,000. Zuwa ƙarshen wata sai ka ga na kashe albashina gaba ɗaya a kuɗin zuwa wajen aiki," a cewar wata mai aikin goge-goge, tana mai cewa dole ta sa ta ajiye aikin.

    Tana zaune ne a Ikorodu, wata unguwa mai cunkoso da masu ƙaramin ƙarfi ke zaune.

    A baya, tafiyar mai nisan kilomita 41 daga Ikorodu zuwa unguwar masu kuɗi ta Victoria Island kan ɗauki awa biyu zuwa uku a lokacin cunkoson tafiya aiki. Yanzu ba ta fi minti 45 ba zuwa 50.

    Sabbin alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa sun nuna cewa idan aka kwatanta da wata uku na biyu a shekarar 2022 da na 2023, gudummawar da sufurin titi ke bai wa tattalin arziki ya ragu da kashi 47 cikin 100.

    Ganin cewa alƙaluman sun duba wata ɗaya ne kawai tun bayan cire tallafin, akwai yiwuwar lamarin ya fi ƙamari.

    Za a fi jin wannan matsin a Legas, birnin da ke da gaɓar ruwa mafi cunkoso kuma wanda shugaban Najeriyar ke alfaharin ya gina shi da kyau.

    "Ya yi daidai da ya cire tallafin mai amma ba a lokacin da ya dace ba, ya kamata sai an gyara matatun mai," in ji wani farfesan tattalin arziki mai suna Uchechi Ogbuagu.

    Saboda matatun man Najeriya ba sa aiki, kusan dukkan fetur ɗin da ake amfani da shi a ƙasar daga ƙasashen waje ake shiga da shi.

    Najeriya na kashe kuɗaɗen da ba ta da su wajen ci gaba da biyan tallafin don rage farashin man a ƙasa baki ɗaya, a cewar wasu.

    Wasu ƙwararru da ma'aikatun gwamnati na ganin tallafin na amfanar masu kuɗi ne kawai sama da talakawa, yayin da 'yan adawa ke cewa cire shi zai jefa talakawan cikin matsi.

    Hatta waɗanda suke ganin ya dace a cire shi suna cewa ya kamata a yi hakan a hankali.

    Ƙungiyoyin ƙwadago sun nemi a gyara matatun, su kuma 'yan adawa na son gwamnati ta cire hannunta daga kasuwancin man.

    Wasu sun nemi a ba da tallafin sufuri - musamman ga amfanin gona - da kuma fargabar abin da za a yi da kuɗin tallafin da aka daina biya.

    "Cire tallafin yana raina kuma nan take na ce 'tallafin mai ya tafi ke nan'," in ji Tinubu game da yadda ya bayar da sanarwar cirewar a jawabin rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu.

    "Mun gaji da ciyar da 'yan sumoga, da ƙara wa mutane arziki ta hanyar biyan tallafi ga ƙasashe maƙwabta," kamar yadda ya bayyana a wani lokaci daban a Faransa.

    Yayin da farashin man ya tashi, masu ƙananan sana'o'i kamar kamfanoni masu kai saƙo a babura da ke ɗaukar dubban matasa aiki, dole ne su sake tunani.

    Wasu ma'aikatan sun rasa ayyukansu, yayin da wasu kamar Happiness Emmanuel suka koma aikin kai saƙo a keke.

    "Ina samun kuɗi sosai kuma ba shi da wuyar aiwatarwa," kamar yadda ya shaida wa BBC a wurin aikinsa da ke yankin Ikeja.

    Wasu daga cikin abokan aikinsa ma sun fara amfani da keke saboda mai, in ji shi.

    Hatta motocin bas-bas na haya da ake kira Bus Rapid Transport , waɗanda suka ƙara yawa da masu aiki da lantarki, sun fuskanci ƙarin fasinja da kusan kashi 30 cikin 100, a cewar mai magana da yawunsu.

    Ya ce hakan ya faru ne bayan rage rabin kuɗin da gwamnatin jihar ta yi.

    Kazalika, jihar ta fara aiki da sabon layin dogo a ranar Litinin, kuma sauƙinsa zai sa mazauna birnin su dinga hawa.

    Shugaba Tinubu ya sanar a farkon watan Agusta cewa sun adana fiye da naira tiriliyan ɗaya (dala biliyan ɗaya ko fan biliyan ɗaya) bayan cire tallafin.

    An ƙaddamar da bayar da bashin kuɗin karatu ga 'ya'yan marasa ƙarfi a jami'o'i, sannan kuma ana shirin ƙara mafi ƙarancin albashi.

    Haka nan, gwamnati ta fara raba kayan abinci na tallafi, za kuma a sauya motocin bas daga amfani da fetur zuwsa gas, inda wasu jihohin kuma suka ƙaddamar da amfani da motoci na lantarki.

    Wasu da dama na ganin biyan tallafin ba abu ne maras kyau ba idan har za a iya kare shi daga cin hanci da rashawa.

    "Tallafi, idan za a iya aiwatar da shi cikin nasara, zai amfani kowa da kowa," in ji Farfesa Ogbuagu.

    "Kowa na sayen fetur a kan farashi ɗaya. Talakawa ba su da talabijin da firjina masu yawa, amma kuma kuɗin sufuri zai ragu," a cewarsa.

    Tinubu ya tabbatar cewa babu wani shirin ƙara farashin man - wanda zai iya yiwuwa saboda yadda darajar naira ke faɗuwa - abin da ke nuna cewa tallafin ya dawo.

    Ba shi ne shugaban Najeriya na farko da zai iya sauya matakin cire tallafin mai ba, duk da cewa na baya sun fuskanci matsi kamar zanga-zangar ƙasa a 2012.

    An ɗan yi zanga-zangar a wasu jihohi game da matsin rayuwar, har ma ƙungiyoyin ƙwadago sun shiga, amma ba su yi wani tasiri ba.

    Akasari akan fara irin wannan zanga-zangar ne daga Legas kafin sauran jihohi su ɗauka.

    AMma wannan karon, birnin da ba ya barci yana fama da ƙarancin hayaƙi, na fili da na ɓoye.

    Read full article