BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023
Source: BBC
An tilastawa Lionel Messi ficewa bayan minti 37 da dawowa taka leda a Inter Miami a wasansu da Toronto FC- amma ƙungiyarsa ta yi nasara a wasan da ci 4-0.
Gajiya ta hana Messi buga wasan da Miami ta yi rashin nasara da ci 4-1 a Atlanta ranar Asabar kuma ana tunanin kyaftin ɗin Argentinan ba zai sami damar buga wasan ƙarshe na gasar US Open da za su fafata da Houston Dynamo ba.
Kociyan ƙungiyar Gerardo Martino ya ce ɗan wasan na fama da wani tsohon rauni.
Zakaran na Ballon d'Or sau bakwai bai samu damar buga wasan tawagar Argentina da Bolivia ba a makon da ya gabata.
Shi ma tsohon abokin wasan Messi na Barcelona Jordi Alba ya samu rauni a karawar da suka yi da Toronto kuma Martino ya ce ko shakka babu 'yan wasan biyu ba za su buga wasan da za su yi da Orlando City a ranar Lahadi ba.
Miami ba ta yi rashin nasara ba a cikin wasanni 11 da Messi ya buga tun lokacin da ya koma ƙungiyar da ke buga gasar MLS a watan Yuli, bayan da ya bar zakarun Faransa Paris St-Germain a ƙarshen wasan kakar 2022-23.