BBC Hausa of Monday, 12 June 2023
Source: BBC
Brahim Diaz ya sake komawa ƙungiyarsa Real Madrid a bana, bayan kaka uku yana wasannin aro a AC Milan.
Mai shekara 23, ya lashe kofin Serie A tare da Milan a 2021/21 sannan ya buga wasan daf da ƙarshe a Champions League a bana, inda Inter Milan ta fitar da su.
Real Madrid ta dauki Brahim a Janairun 2019 daga Manchester City, wanda ya dauki kofin La Liga a Santiago Bernabeu a kakar 2019/20 da Spanish Super Cup a 2020.
An bayar da shi aro ga AC Milan a cikin Satumbar 2020, inda ya yi kaka uku tare da cin ƙwallo 18 a dukkan fafatawar da ya yi wa Milan.
Ya fara taka leda a matashin dan wasa a Malaga, daga nan ya koma Manchester City, ya fara taka leda a Ingila a karawa da Swansea a EFL Cup a 2016/17 yana da shekara 17.
A kakar 2017/18 ya fara buga Premier League da FA Cup, wanda ya bayar da gudunmuwar da City ta lashe lik da League Cup.
Haka kuma ya ɗauki Community Shield a dai Manchester City.
Ƙungiyoyin da ya buga a matakin ƙwararren ɗan wasa: