You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1761032

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

    

Source: BBC

Real Madrid za ta dauki Copa del Rey na 20 ranar Asabar

Yan wasan Real Madrid Yan wasan Real Madrid

Real Madrid da Osasuna za su buga wasan karshe a Copa del Rey ranar Asabar a Estadio La Cartuja.

Real Madrid na fatan lashe kofin bana, kuma na 20 jimilla, ita ce ta uku a yawan daukar shi, bayan da Osasuna ke fatan daga na farko a tarihi.

Kofi na uku a bana da Real Madrid ke fatan dauka, bayan European Super Cup da Club World Cup.

Real da Osasuna sun tashi 1-1 a La Liga a bana ranar 2 ga watan Disambar 2022 a Santiago Bernabeu.

A wasa na biyu da suka kara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, Real Madrid ce ta yi nasara cin 2-0 ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 a gidan Osasuna.

Wannan shine karon farko da kungiyoyin za su kara da juna a wasan karshe a Copa del Rey, amma karo na 40 da Real za ta buga wasan karshe a gasar.

Karon karshe da Real ta lashe Copa del Rey shine a 2013/14, bayan da ta doke Barcelona 2-1, kuma karkashin Carlo Ancelotti a Estadio Mestalla.

Osasuna, wadda ta fitar da Athletic a zagayen daf da karshe a bana, za ta buga wasan karshe karo na biyu, wadda ta yi rashin nasara a hannun Real Betis da ci 2-1 a 2004/2005.

Real Madrid ta kai wasan karshe a Copa del Rey a kakar nan, bayan doke Cacereño 1-0 a zagayen kungiyoyi 32.

Daga nan Real ta ci Villarreal 3-2 a zagayen kungiyoyi 16 - Real ce ta fitar da Atlético da kuma Barcelona.

Barcelona ce kan gaba a yawan daukar Copa del Rey mai 31, sai Athletic Bilbao mai 23 da Real Madrid mai 19. Atletico Madrid 10 ta lashe.

Read full article