You are here: HomeAfricaBBC2023 04 10Article 1746947

BBC Hausa of Monday, 10 April 2023

    

Source: BBC

Real na atisayen yadda za ta ci Chelsea a Champions League

Yan wasan Real Madrid a training Yan wasan Real Madrid a training

Real Madrid na yin atisayen yadda za ta ci Chelsea a Champions League ranar Laraba.

Chelsea za ta ziyarci Real Madrid, domin buga wasan farko a quarter finals a Santiago Bernabue.

Da sanyin safiyar Litinin 'yan wasan Real suka motsa jiki a shirin da kungiyar ke yi na kare kofin da ta lashe a bara na 14 jimilla.

Sun fara da guje-guje daga nan aka raba su rukunnai domin wasa da lailaya tamaula a tsakaninsu.

Daga nan aka raba filin zuwa rabi 'yan wasa suka taka leda, daga karshe aka karkare da gwada gola da cin fenariti da bugun tazara.

Real za ta buga wasan, bayan da Villareal ta doke ta 3-2 ranar Asabar a Santigo Bernabue a wasan mako na 28 a La Liga.

Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona ta daya, wadda za ta karbi bakuncin Girona ranar Litinin.

Ranar Asabar Chelsea ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Wolverhampton a karawar mako na 30 a Premier League.

Chelsea tana mataki na 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 39.

Read full article