BBC Hausa of Wednesday, 12 April 2023
Source: BBC
Tsawon mako biyu a baya-bayan nan, dubban likitocin asibitocin kuɗi a Rajasthan suka yi zanga-zangar nuna adawa da wata muhimmiyar doka da ke tabbatar da 'yancin samun kulawar likitoci ga al'ummar jihar ta arewacin Indiya su miliyan tamanin.
Zanga-zangar ta durƙusar ayyukan lafiya a asibitocin kuɗi, inda asibitocin gwamnati suka cika maƙil da marasa lafiya.
A ranar Talata, gwamnatin jihar ta ce ta cimma yarjejeniya da likitocin, abin da ya sa suka janye yajin aikin da suke yi.
Abin da ya harzuƙa masu zanga-zangar shi ne wani tanadin a cikin dokar, da ke tilasta wa asibitocin gwamnati da na kuɗi, su bai wa mutum kulawar likita ta gaggawa, kuɗin kuma sai daga bisani gwamnati za ta biya. Likitocin sun ce ba a fayyace bayanai game da, ta yaya, da kuma daga ina kuɗin za su fito ba.
Adadin jihohin Indiya suna da tsare-tsaren inshorar lafiyarsu da ke bai wa masu ƙaramin ƙarfi 'yancin samun kulawa a asibitocin gwamnati da wasu asibitocin kuɗi da aka ƙayyade.
A 2018, an ƙaddamar da wani shirin inshorar lafiya na tarayya mai suna PM-JAY don kula da mutane mafi talauci kimanin kashi 40% na al'ummar ƙasar.
Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa hana mutum kulawar likita a halin buƙatar gaggawa, keta 'yancin tsarin mulkin Indiya ne da ke tabbatar da 'yancin rayuwa.
Duk da haka asibitocin gwamnati a Indiya ba su wadata ba, kuma suna fama da ƙarancin kuɗi, lamarin da ya jefa su cikin ƙaƙa-ni-ka-yi ta fuskar ƙarancin kuɗin tafiyarwa da ƙarancin likitoci da ma'aikatan jinya.
Indiya tana kashe kashi 2% da kaɗan na kuɗin da take samu daga duk abin da ta sarrafa a cikin gida (GDP) a ɓangaren lafiya, shi ne ɗaya daga cikin mafi ƙaranci a duniya. Mafi yawan mutane sai sun biya kimanin rabi na kuɗin asibiti - musamman wajen sayen magunguna - daga aljifansu.
Likitocin asibitin kuɗi da sha-ka-tafi da asibitoci su ne suke samo kashi 80% na jimillar kuɗin kula da lafiya da ake kashewa. Mutane fiye da miliyan 55 ne ke sake tsunduma cikin talauci duk shekara saboda "masifar" tsadar kuɗaɗen da ake kashewa wajen neman lafiya, abin da ke tasiri ga rayuwar 17% na magidanta, a cewar wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya.
Babu tantama, sanya farashi da biyan kuɗin, nauyi ne da suka rataya kan shirin inshorar lafiya na jiha, ko wata doka da ke bai wa mutane 'yancin samun kulawar likitoci. Dukkansu biyun suna da rikitarwa.
Kuɗin wani aikin tiyata, ga misali, a wani babban asibiti, na iya kai wa har ninki shida a kan abin da za a biya a wani gidan marayu.
Idan gwamnati ta zaɓi arha, akwai yiwuwar asibitocin kuɗi za su riƙa korar marasa lafiyan da suka je neman a yi musu tiyata a ƙarƙashin inshora ko kuma a nemi su yiwo ciko. Idan gwamnati ta zaɓi mai tsada, kuɗin shirin inshorar lafiya, zai ninka ninki-ba-ninki.
"Yadda za ka sa farashi da yadda za a biya asibitoci kuɗinsu, wani ɓangare ne na samun ɓangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu su shigo harkar," kamar yadda Farfesa Jishnu Das na Jami'ar Georgetown ya faɗa mini.
Waɗannan abubuwan damuwa ne, wani nazari da Radhika Jain ta University College da ke London ya tsefe game da yadda biyan asibitoci da sanya farashi ke da tasiri kan halayyar asibitocin kuɗi da ƙwazonsu a wani shirin inshorar lafiya na gwamnati a Indiya.
Farfesa Jain ta dubi buƙatu fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari shida na neman a biya kuɗi da kuma marasa lafiya dubu ashirin a wani shirin inshorar lafiya na gwamnati a jihar Rajasthan wanda ke biyan asibitoci wani ƙayyadajjen farashi ga ayyukan gwaje-gwaje, da ba da magunguna da kuma kuɗin asibiti.
Ta gano cewa asibitoci masu zaman kansu na neman a biya su kuɗin da ya zarce farashi, kuma ana biyansu kudi fiye da na ayyukan da suka yi, haka zalika, sukan karɓi kuɗi a hannun maras lafiya ga ayyukan lafiyar da suka kamata a ce kyauta ne a ƙarƙashin shirin inshorar, da sauransu.
Wannan na nuna cewa akwai "rarraunan sa-ido" kuma jami'an asibitoci masu zaman kansu da ke neman riba ido rufe cikin dabara suna yin biris da dokokin inshorar lafiya don ƙara yawan kuɗin shigarsu, inda suke ci da gumin gwamnati da kuma marasa lafiya".
A ɓangare ɗaya kuma, likitocin asibitin kuɗi da ke zanga-zanga a Rajasthan na da 'yan hanzari ƙalilan.
Abu na farko, ta yaya ake tantance buƙatar kulawar gaggawa, da gwamnati za ta biya kuɗi? "Tana iya kamawa daga bugun zuciya har zuwa ga duba wani yaro da aka kai asibiti da ciwon ciki," wani likita ya faɗa wa wata jarida.
Abu na biyu kuma, ta yaya za a gane asibitocin da ke samar da kulawar gaggawa? (Wani nazari ya yi ƙiyasin cewa kashi 65% na asibitocin kuɗi a Indiya 'yan ƙananan cibiyoyi ne masu cin gado 11 - 50.)
Bayan zanga-zangar, gwamnatin jihar ta amince ta cire daga cikin dokar, asibitocin kuɗi masu gadajen kwanciya ƙasa da 50 da kuma waɗanda ba su samu rangwamen gwamnati wajen kafa cibiyoyin lafiyarsu ba.
Da wannan togaciya biyu, a ƙalla "kashi 98% na asibitocin kuɗi" a jihar Rajasthan ba za su yi aiki da wannan doka ba, cewar Dr Sunil Chugh, wani babban jami'i a wata ƙungiyar likitoci.
Idan kuwa gaskiya ne, wannan wani gagarumin abu ne.
Gwamnatin Rajasthan ta ce sabuwar dokar za ta zaburar da ita wajen ingantawa da kyautata cibiyoyin lafiya na gwamnati, abin da kuma kowa zai yi maraba da shi.
Sai dai kamar yadda nazarin Farfesa Jain ya nuna, sai an ɗauki tsawon lokaci kafin mutane su amince da asibitocin gwamnati - kashi 75% na buƙatar neman biyan kuɗin inshora a shekara huɗu na farkon shirin inshorar lafiya na Rajasthan sun fito ne daga asibitocin kuɗi.
Mawuyacin halin da Surendra Meghwal, ɗan shekara 44 mazaunin Rajasthan yake ciki, yana kuma ba da ƙarin haske na wani wagegen giɓi tsakanin alƙawurra da kuma abin da ake gani a zahiri.
Har yanzu, yana biyan bashi na kuɗin maganin da ke kansa bayan kulawar da likitoci suka bai wa ƙanwar matarsa wadda ta rasu dalilin cutar korona shekara biyu da ta wuce, a wani asibitin kuɗi da ke lardin Karauli. Dangi ne suka kai maras lafiyar asibitin kuɗi saboda babu gado a asibitin gwamnati.
Mr Meghwal ya ce mutane a ƙauyuka na rige-rigen zuwa ƙananan asibitocin kuɗi da ke larduna a lokacin buƙatar kulawar gaggawa saboda babu isassun asibitocin gwamnati.
"Idan gwamnati a yanzu ta cire waɗannan ƙananan asibitoci daga jerin cibiyoyin samun kula da lafiya, to ina kuma za mu je?
Za mu ci gaba da shan wahala," in ji shi.
Kafa sabuwar doka, na nufin kotuna da gagarumin aikin bin diddigi za su shigo ciki, cewar Farfesa Das. (Ya ba da misali da al'amarin Columbia, inda masu hali suka riƙa cika kotuna neman a ba su damar samun kulawar asibiti mai tsada a ƙarƙashin dokar lafiya.)
Ya yi tunanin Rajasthan kaɗai za ta buƙaci masu aikin bin diddigi 6,000 da za su riƙa sa ido kan buƙatun neman a biya aikin kula da lafiya da almundahana da rigingimun shari'a da ƙorafe-ƙorafen abokan hulɗa da ƙalailaice bayanai.
"Wani abu mai kyawu game da dokar shi ne, ta ce har yanzu muna son ci gaba da zuba kudi a harkar kula da lafiyar al'umma, sai dai wani ɓangare da ba a ce uffan ba, shi ne mutane na da zaɓin su je asibitocin kuɗi," in ji shi.
Ƙungiyoyi masu rajin inganta asibitocin gwamnati sun yi imani Rajasthan na buƙatar dokar farko ta Indiya kan 'yancin samun kula da lafiya.
Wani rahoton 2021 a kan "jihohi masu ƙoshin lafiya" daga Niti Aayog, wata cibiyar zurfin nazari ta ma'aikatar lafiya ta tarayya a Indiya da Bankin Duniya ya sanya Rajasthan a matsayin ta 16 cikin manyan jihohin ƙasar 19.
Tana da yawan mace-macen ƙananan yara - mutuwar jarirai 'yan ƙasa da shekara ɗaya. Wani abin damuwa kuma, shi ne tana da likitoci kaɗan idan an kwatanta da yawan jama'arta.