You are here: HomeAfricaBBC2021 08 29Article 1343980

BBC Hausa of Sunday, 29 August 2021

    

Source: BBC

Rikicin Afghanistan: Wace ƙungiya ce Isis-K?

ISKP wani reshe ne na ƙungiyar IS a ƙasashen Afghanistan da Pakistan ISKP wani reshe ne na ƙungiyar IS a ƙasashen Afghanistan da Pakistan

Isis-K - ko kuma ma'ana Daular Islama a lardin Khorasan (ISKP) - wani reshe ne na ƙungiyar IS a ƙasashen Afghanistan da Pakistan.

Ƙungiyar ita ce mafi hatsari tsakanin manyan ƙungiyoyin da ke da'awar jihadi na Afghanistan.

An kafa ta ne a watan Janairun 2015 a lokacin da IS ke iƙirarin kafa daula a Iraƙi da Syria, kafin ƙawancen da Amurka ke jagoranta ya karya lagonta.

Ta samu mayaƙa ƴan Afghanistan da Pakistan, musamman waɗanda suka ɓalle daga ƙungiyar Taliban waɗanda suke ganin ƙungiyar na da sassauci.

Ya tsananin tsattsauran ra'ayinta?

Isis-K ana zarginta da kai munanan hare-hare a shekarun baya bayan nan, sun fi kai hari kan makarantun ƙananan yara da asibitoci musamman ɗakin masu haihuwa inda rahotanni suka ce sun harbe mace mai ciki da kuma ma'aikatan jinya.

Saɓanin Taliban, wacce manufarta ta fi karkata ga Afghanistan, amma Isis-K reshe ne na ƙungiyar IS da ke da'awar kai wa ƙasashen yammaci hari da jami'an agaji.

A ina take?

Isis-K tana gudanar da ayyukanta ne daga gabashin lardin Nangarhar, kusa da inda ake shige da ficen miyagun ƙwayoyi zuwa Pakistan.

An ƙiyasta cewa ƙungiyar tana da yawan mayaƙa 3,000 - amma an kashe mayaƙanta da dama a artabu da dakarun Amurka da na Afghanistan, da kuma Taliban.

Ko tana da alaƙa da Taliban?

A takaice tana da alaƙa, amma ta hanyar ƙungiyar Haƙƙani.

A cewar masu bincike, akwai babbar alaƙa tsakanin Isis-K da ƙungiyar Haƙƙani, wacce ke kud da kud da Taliban.

Mutumin da ke kula da tsaron Kabul, shi ne Khalil Haqqani wanda aka ɗora wa ladar dala miliyan biyar

Dr Sajjan Gohel daga gidauniyar Asia Pacifi ya daɗe yana sa ido da bincike kan alaƙar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Afghanistan.

Ya ce "hare-hare da dama da aka kai tsakanin 2019 zuwa 2021 an kai su ne ta haɗin guiwa tsakanin Isis-K da Taliban ɓangaren Haƙƙani da sauran ƙungiyoyi a Pakistan."

Lokacin da Taliban ta ƙwace mulki a ranar 15 ga Agusta, ƙungiyar ta saki fursunoni da dama a gidan yarin Pul-e-Charki, waɗanda rahotanni suka ce sun ƙunshi mayaƙan IS da al-Ƙa'ida.

Amma Isis-K tana da bambanci da Taliban, inda ta zarge su da yin watsi da da'awar jihadi da kuma fagen daga saboda tattaunawar sulhu da take a Qatar.

Mayaƙan IS yanzu sun kasance babban ƙalubale ga gwamnatin Taliban mai zuwa, wani abu da ke gaban shugabannin Taliban da kuma jami'an leƙen asiri na ƙasashen yammaci.

Read full article