You are here: HomeAfricaBBC2022 09 20Article 1627223

BBC Hausa of Tuesday, 20 September 2022

    

Source: BBC

Ronaldo ne mafi tasiri a tsakanin 'yan kwallo kafa a Instagram

Cristiano Ronaldo Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya sha gaban Lionel Messi da Neymar da Kylian Mbappe a matakin mafi tarin jama'a tsakanin 'yan kwallon kafa a Instagram.

Ya samu karin mabiya sakamakon Gasar Kofin duniya da za a yi a cikin Nywamba da Qatar za ta karbi bakunci a 2022.

Kyaftin din tawagar Portugal ya samu karin mutane da ke bibiyarsa kaso 48 cikin 100 tun daga shekarar da ta gabata.

Wani bincike da Nielsen Gracenote ya gudanar ya ce dan wasan na Manchester United kan samu matsakaicin kudi da ya kai $3.5m a duk sakon da ya rubuta.

Takwaran Ronaldo, dan kwallon Manchester United, Jadon Sancho shi ne kan gaba a Ingila, yayin da Gavi ya samu karin mabiya kaso 5,165 cikin 100.

Nielsen ya auna wannan cigaban kan ma'aunin da ya tantance yawan magoya baya da karin mabiya da dan wasa ke samu da yadda ake bbiyar shi da kudin da dan kwallo ke samu a duk lokacin da ya wallafa abu a Instagram.

An kuma dora ma'aunin kan 'yan wasan da za su wakilci kasashensu a gasar kofin duniya da za a yi cikin watan Nuwamba.

Ronaldo yana da mabiya miliyan 480 a Instagram, kyaftin din Argentina, Messi ne ke biye da shi mai mabiya miliyan 360, wanda ya samu karin kaso 38 cikin 100 - mai karbar $2.6m a duk sakon da ya wallafa a kafar sada zumunta ta Instagram.

'Yan wasan Paris St German da suka hada da Messi da Neymar da Kylian Mbappe ne ke biye da Ronaldo a mataki na biyu da na uku da kuma na hudu.

Sauran 'yan wasa biyu daga PSG kan karbi matsakaicin kudin da ya kai $1m a duk sakon da suka wallafa a Instagram.

Cikin jerin 10 farko mafiya mabiya a Instagram tsakanin masu taka leda, dan wasan Brazil mai wasa a Real Madrid, Vinicius Junior ne kan gaba.

Ya samu karin tarin mabiya tun daga lokacin da Real ta doke Liverpool ta lashe Champions League na 14 jumulla a kakar da ta wuce.

Read full article