BBC Hausa of Thursday, 14 September 2023
Source: BBC
Wasu daga cikin kafofin yaɗa labaru na na shafin intanet sun rinƙa yaɗa labarun ƙarya domin samun kuɗi ta hanyar tallace-tallace.
BBC ta gano cewa an buɗe shafukan intanet gab da babban zaɓen Najeriya na 2023, waɗanda ake amfani da su wajen isar da labaran ƙarya ga dubun dubatar mutane.
Kuma yawaitar tallace-tallace a shafukan na nufin cewa suna amfani da yaɗa labaran ƙarya wajen samun riba.
Sukan rinƙa cakuɗa ƙarya da gaskiya a labarunsu na siyasa da nishaɗi da kuma wasanni - inda wasu kan wallafa labaran da suka kai 700 a cikin wata guda.
Sukan kuma nuna goyon baya ko kuma su soki wasu ƴan siyasa.
Kimanin wata bakwai bayan zaɓen wanda ya yi zafi, har yanzu kawunan ƴan Najeriya na a rarrabe, kamar yadda aka gani bayan hukuncin da kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta sanar a makon da ya gabata.
Akwai alamun cewa labarun ƙarya da waɗannan kafafe suka rinƙa yaɗawa sun bayar da gudumawa wajen rarraba kawunan ƴan ƙasar.
Wata lauya, Mojirayo Ogunlana ta ce za ta iya tuna yadda aka riƙa yaɗa labarai gabanin babban zaɓen ƙasar a shafukan tuwita daga wasu shafukan labarai waɗanda ba ta taɓa sanin su ba. Da yawa daga cikin irin waɗannan labaru an riƙa yaɗa su a guruf-guruf na manhajar WhatsApp.
Ta ce yawan labarun ƙarya da aka riƙa yaɗawa sun yi muni. "Da wuya a wayi gari ba ka ga labaran ƙarya na yawo a shafukan sada zumunta ba. Abin ya riƙa sanya min wasuwasi," in ji Ms Ogunlana.
Mai bincika kan yaƙi da labarun ƙarya, Mayowa Tijani ya bibiyi yadda shafukan suka riƙa bunƙasa.
Ya ce sun yi "tasiri ƙarara" kasancewar sun haifar da muhawara a faɗin ƙasa kan zaɓe. Kuma suna ci gaba da yaɗa waɗannan labaru na ƙarya, in ji shi.
"Yanzu idan ɗaya daga cikinsu ya wallafa labarin ƙarya, wasu shafukan za su ɗauka su yaɗa kuma ta haka sai abin ya yi tasiri a shafukan sada zumunta.
Sukan taimaka wajen ƙara yaɗa shi har zuwa cikin al'umma, sai ka ga batun ya yi kaka-gida a tsakanin al'umma," in ji shi.
Ɓangaren yaƙi da labaran ƙarya na BBC ya yi nazari kan uku daga cikin waɗannan shafuka:
Podium Reporters, shafi ne da aka yi wa rajista a 2021, Reportera kuma an masa rajista ne a watan Yulin 2022, sai kuma Parallel Facts, wanda aka yi wa rajista a watan Mayun 2023.
Mr Tijani ya ce akwai dalilin da ya sa aka ƙirƙire su a lokacin da aka ƙirƙire su.
Da farko, a cewarsa, alamu sun nuna cewa shafukan sun yi ƙoƙari ne wajen ganin an zaɓi wani ɗan takara. Amma ya yi amannar cewa waɗanda suka ƙirƙire suna da aniyar samun kuɗi ta hanyar shafukan.
Mun tattauna da wani masani kan kafofin yaɗa labaru kan ko nawa irin waɗannan shafuka kan iya samu ta fannin kuɗi.
Masani kan fasahar sada zumunta ta zamani da talla a intanet, Yusufudden A Yusuf, ya ce za su iya samun kuɗin da ya kai tsakanin dalar Amurka 100 zuwa 10,000 a kowane wata.
"Idan aka shiga shafukan nasu da yawa na nufin masu karatu za su yi tsokaci sosai, wanda hakan ke nufin za su samu kuɗaɗen talla da yawa." in ji shi.
To amma wani masani kan harkar hulɗa da jama'a a kafofin yaɗa labaru na zamani, Adebayo Ilupeju, ya ce da yiwuwar waɗannan shafuka ba za su rinƙa samun kuɗi sosai ba saboda sabbi ne. "Tamkar zuba jari ne," a cewarsa.
Mun yi ƙoƙarin tuntuɓar kafafen na Podium Reporters, da Reportera da Parallel Facts, amma ba su ba mu amsar wasiƙar email da muka tura musu ba, inda muka tambaye su game da labaran ƙarya da ake yaɗawa a shafukansu da kuma kuɗin da suka samu.
An wallafa labarai wadanda ba na gaskiya ba a kan dukkanin manyan ‘yan takarar shugaban kasa uku a shafukan da muka yi nazari a kai.
Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ne ya lashe zaben bayan samun kashi 30 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
Har yanzu ‘yan takarar jam’iyyun adawa da suka zo na biyu da na uku, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP na ci gaba da kalubalantar nasarar tasa a kotu.
A makon da ya gabata kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa ta yi watsi da kararrakinsu, sai dai sun ce za su daukaka kara zuwa kotun koli.
‘Yan siyasa ma sun rika yada labaru daga shafukan, abin da ya taimaka wajen kara fito da su.
Misali, Festus Keyami, wanda shi ne ministan sufurin jiragen sama na yanzu, ya yada labarai da dama daga kafar Podium Reporters a lokacin harkokin zabe.
Shi kuma Peter Obi ya shiga tattaunawar da ake yi kai-tsaye ta shafin tuwita na kafar Parallel Facts, daya daga cikin irin wannan tattaunawa ta bunkasa yadda ake ambaton kafar a shafin tuwita daga sau 10,000 zuwa 40,000, tsakanin watannin Mayu zuwa Yulin 2023.
Kingsley Izuchukwu Okafor ne ya mallaki kafar.
A shafukansa na sada zumunta ya bayyana kansa a matsayin wanda ke son abubuwan da suka shafi kirkire-kirkire, da hulda da jama’a da kuma kyamar “mummunan shugabanci.”
Ya taba wallafa hoton Peter Obi, tare da cewa “Obi ne wanda ya cancanta.”
Kafar tasa na da take kamar haka: “Babu farfaganda kuma babu labaran karya”.
Sai dai binciken da muka yi ya nuna akasin haka.
A cikin tsawon wata daya, tsakanin 19 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuli, BBC ta kirga labaru da dama wadanda ke kunshe da karya, wadanda aka wallafa a shafin intanet na Parallel Facts.
Wani labarin da aka wallafa a ranar 27 ga watan Yuni ya yi ikirarin cewa shugaban hukumar zabe ta INEC, Mahmood Yakubu, na kokarin bin hanyoyin da ba su dace ba wajen bai wa jam’iyyar APC kuri’un da suka kai kashi 25% na yawan kuri’un da za a kada a yankin Abuja.
To amma babu wata hujja da ta nuna cewa hukumar Inec ko Mr Mahmood sun murde sakamakon zaben da aka gudanar a yankin birnin tarayya kamar yadda aka yi ikirari a cikin labarin.
Duk da cewa wasu kafofin yin bincike kan gaskiyar labarai sun karyata irin wadannan labarai, amma har yanzu suna nan yadda suke, ba a gyara bayanan da ke cikinsu ba.
Reortera ma wata kafar yada labarai ce ta intanet wadda ta karkata ga jam’iyyar LP.
A babban sakonta da ta kafe a shafinta na tuwita, ta bayyana cewa ba ta amince da gwamnatin Bola Tinubu ba.
A tsawon wata guda, shafin intanet na kafar ya wallafa labaran karya guda hudu, ciki har da wanda ke ikirarin cewa shugaba Tinubu shi ne ya zo na uku a zaben da aka gudanar.
Ta kuma yi wa wani labarin BBC kan zaben karkatacciyar fassara.
A labarinta da ta wallafa a ranar 28 ga watan Yuni, Reportera ta yi ikirarin cewa BBC “ta gano hujja karara ta cewa an danne wasu masu kada kuri’a” tare kuma da cewa bai kamata a bayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara ba.
To amma gaskiyar batu shi ne babu wannan maganar a cikin labarin da BBC ta yi. Abin da ya nuna shi ne a wasu yankuna na jihar Ribas, an rage yawan kuri’un da jam’iyyar LP ta samu sannan aka kara yawan kuri’un da jam’iyyar APC ta samu.
Ta hanyar amfani da sakamakon da yake bayyane ga al’umma daga shafin intanet na Inec, BBC ta nuna a cikin labarinta cewar jam’iyyar LP ya ci a ce ta samu kuri’u mafi yawa a jihar, a maimakon Tinubu. Amma ba mu da wata hujja cewar hakan ya faru a wani yankin kasar na daban, saboda haka babu yadda za a yi mu ce bai kamata a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba.
Labarin ya ce Reportera ta yi “nazari”, ba tare da nuna yadda ta samo tata matsayar kan cewa Obi e ya yi nasara ba.
A maimakon haka, sai ta kafa hujja da kuri’ar jin ra’ayin al’umma da ta yi ta shafinta na sada zumunta na tuwita, inda kashi 93% na wadanda suka yi tsokaci, mutum 31,000 suka ce Mr Obi ne ya lashe zaben.
Bugu da kari a baya-bayan nan, wanda ya mallaki kafar, Nnamdi Ibezim, a cikin wani bayani ya amince cewar ya wallafa wani labari “bisa dogaro da jita-jita”. A shafin sada zumunta, Mr Ibezim ya bayyana kansa a matsayin dan kasuwa kuma mai ilimi daban-daban.
Wani labarin da kafarsa ta wallafa a intanet a ranar 6 ga watan Agusta, ya ce tsohon ministan ayyuka da gidaje na Najeriya, Babatunde Fashola na taimaka wa alkalan kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa wajen rubuta hukuncin kotun ta yadda za a bai wa APC nasara.
Daga baya Mr Fashola ya bayyana cewa ya rubuta korafi game da hakan zuwa ga Sufeta-Janar na ‘yan sandan Najeriya yana tuhumar kafar Repotera da “yi masa kage da barazana ga rayuwarsa a shafin intanet”.
Mr Ibezim ya bayar da rahoton cewa rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya, DSS ta kama dan’uwansa, Chike Ibezim a kan wannan labarin da suka wallafa, inda suka fitar da bayani suna cewa kamen da aka yi masa ya saba wa kundin tsarin mulki.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa ta kama Chike Ibezim.
A bangare daya kuwa, kafar labarai ta Podium Reporters ta rinka wallafa labarai ne da ke goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki.
A ranar 4 ga watan Juli, 2023, ta wallafa wani labari a kan kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra (Ipob), wata kungiyar ‘yan aware wadda gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Labarin na kunshe da bayanan karya da dama.
Misali, ta yi ikirarin cewa Ipob ta amince da takarar Peter Obi a kungiyance.
Alakanta Mr Obi da ‘yan kungiyar Ipob wani abu ne da ya zamo ruwan dare a labarun Podium Reporters - mun kirga irin wadannan labarai guda bakwai a cikin wata daya.
Sai dai Peter Obi da jam’iyyarsa ta siyasa sun sha musanta duk wata alaka da kungiyar, sannan kungiyar ba ta taba fitowa fili ta nuna goyon bayanta gare shi ba.
Ba mu iya gano ko wane ne ya mallaki shafin Podium Reporters ba.