BBC Hausa of Friday, 30 June 2023
Source: BBC
Jagoran masu busa, Chukwu Oba Kalu na kokarin ganin fatan da yake da shi kan salon busa na bagpipe tun yana karami ya samu karbuwa.
Mai shekara 46, Chukwu ya fara ganin ana amfani da abin busa na bagpipe ne tun lokacin yana da shekara 18, lokacin yana cikin kungiyar Boys Brigade a jihar Abia, da ke gabashin Najeriya.
Abin ya burge shi, kuma ya sha alwashin cewa zai koyi yadda ake yin irin wannan busa.
"Sautinta ya yi daban da saura. Sautinta na da kayatarwa...yana taɓa zuciya," kamar yadda ya shaida wa BBC.
A farko ya yi yunƙurin shiga Cibiyar koyar da badujala ta ƙasar Scotland, to amma ba ya da kuɗin da zai yi hakan.
Sai kuma ya yi ƙoƙarin ganin an kawo masa kakakin daga ƙasar waje, sai dai hakan ma ba abu ne mai sauƙi ba.
Ya tura saƙonni zuwa ga masu sayar da kayan koyon badujalar a Birtaniya da Amurka, to amma bai samu martani ba na tsawon lokaci.
Daga baya ya samu martani na farko, wanda hakan ya tabbatar masa da dalilin da ya sa bai samu martani ba tun farko.
Shagon sayar da kayan ya ce masa sun zata shi dan zamba ne wanda ke neman ya samu lambobin asusunsu na ajiyar banki.
Domin ya tabbatar cewa shi ba mazambaci ba ne, Chukwu ya tura tsabar kuɗin dalar Amurka zuwa California, inda ya jira isowar abin busarsa na farko.
"Na yi matuƙar murna a lokacin da ya iso. A lokacin da na karɓe ta na durƙusa da na gode wa Allah, na ce: a ƙarshe dai Allah Ya kawo min ɗauki."
Abin busar ya isa gare shi ne a 2009, shekaru da dama bayan ya tura saƙon email na farko.
Abin busar wata ƙaramar sarewa ce wadda ake amfani da ita wajen koyon busar - an kuma gargaɗi Chukwu kan ya bi ta a hankali kada ta ɓalle.
"Saboda haka ne na riƙa ririta ta kamar ƙwai, ba na son wani ya zo kusa da ni a duk lokacin da nake riƙe da ita."
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya wa Chukwu sha'awar mabusar bagpipe shi ne iyalinsa.
Kakansa ya yi aiki da sojojin Birtaniya a lokacin mulkin mallaka, lokacin da Najeriya ke ƙarƙashin mulkin turawan Burtaniya, inda a wancan lokacin ake kiran sa da 'Saje.'
Yakan rinƙa rera waƙoƙin yaƙi daga cikin ɗakinsa, kuma lamarin na burge Chukwu, sannan ya riƙa son ya fahimci ma'anar waƙoƙin.
Chukwu ya ce "wannan tamkar wani ruhi ne da ya sake dawowa."
"Ina da yaƙinin cewa sha'awar da kakana ke da ita a lokacin da ya yi aiki da sojojin Birtaniya, da ƴan mishan.....har yanzu abin na tare da ni a cikin jikina."
A lokacin da ya fara amfani da mabusar, ba da jimawa ba sai ga shi ya samar da tasa tawagar.
Ya kuma bincika wasu sassan Najeriya da nufin ko zai samu wasu masu amfani da irin wannan mabusa ta bagpipe domin su yi aiki tare.
A lokacin mulkin mallaka, turawan Scotland sun koya wa ƴan Najeriya yadda za su busa 'bagpipe, haka nan sojoji da ƴan sandan Najeriya sun riƙe busar a bayan samun ƴanci, sai dai an yi watsi da al'adar daga baya.
Hakan ta faru ne bayan da saboda tsufan da kayan busar suka yi sannan waɗanda suka ƙware a fannin suka yi ritaya.
Chukwu ya yi ƙoƙarin gano wasu daga cikin tsofaffin masu busar inda suka haɗa tawaga, sannan daga baya suka samo waɗanda suka shiga tawagar.
A yanzu akan ɗauki akan ɗauki tawagar tasa domin su yi irin wannan busa a wuraren bukukuwan aure da jana'iza da kuma sauran taruka.
To amma duk da haka burinsa bai kammala ba.
"Burina ba kawai na farfaɗo da busar bagpipe da kuma yin wasa a wurin taruka ba ne kawai."
Chukwu ya rubuta takardar buƙatar horas da sojoji masu busa badujala na sojojin ƙasa da na sama.
Babban hafsan dakarun sama na Najeriya ya amince da batun, inda aka shirya wata horaswa ta wata guda ga sojoji. An yaye ɗaliban busar na farko ne a shekarar 2019.
Baya ga wannan ya kuma bayar da shawarar kafa tawagar masu badujala ta shugaban ƙasa, wadda ta samu amincewar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Chukwu na sa ran ci gaba da horas da masu busar badujalar bagpipe a rundunar sojin da kuma sauran hukumomin tsaro na Najeriya.
Ya ce "Ina murna cewa lamarin na samun ci gaba, kuma zai ci gaba da bunƙasa."
"Da yaradar Allah ina sa ran zuwa Scotland a wannan shekarar, idan na samu hali, domin ban taɓa zuwa Scotland ɗin ba."