You are here: HomeAfricaBBC2021 08 16Article 1334380

BBC Hausa of Monday, 16 August 2021

    

Source: BBC

Samuel Kalu: Dan wasan Bordeaux na cikin koshin lafiya, bayan faduwa a filin wasa

Samuel Kalu ya fadi afilin wasa ayayin da Bordeaux ke was da Marseille a Faransa Samuel Kalu ya fadi afilin wasa ayayin da Bordeaux ke was da Marseille a Faransa

Dan kwallon Bordeaux, Samuel Kalu ya murmure, bayan da ya fadi a cikin filin Stade Velodrome a karawar da suka yi 2-2 da Marseille ranar Lahadi in ji abokin wasan sa Remy Oudin.

Dan Najeriya, mai shekara 23, ya samu agajin gaggawa a lokacin da ya fadi a cikin filin a minti na shida da fara tamaula.

Ya mike da kafafunsa minti daya tsakani, sannan ya rike jakar kankara da ya kara a kansa.

Kalu ya ci gaba da wasa, amma daga baya aka sauya shi, bayan da aka fuskanci jiri na jan shi.

"Mun firgita kuma har yanzu a tsora ce muke, '' in ji Oudin, wanda ya maye gurbin Kalu a minti na 14.

"Kamar yadda likita ya fada ya dan samu buguwa,.'' Muna taya Kalu murna, komai dai lafiya lau, kuma shine mafi mahimmaci,'' in ji Oudin.

Tsohon dan wasan Tottenham, Eriksen ya fada a cikin filin a cikin watan Yuni a lokacin da zuciyar sa ta daina bugawa a karawar da Denmark ta yi da Finland a Euro 2020.

Read full article