You are here: HomeAfricaBBC2022 03 12Article 1488803

BBC Hausa of Saturday, 12 March 2022

    

Source: BBC

Shekaru biyu da ayyana korona a matsayin annoba: Abubuwa biyar da muka koya

Cutar korona ta saka duniya a mawiyancin hali shkarun baya Cutar korona ta saka duniya a mawiyancin hali shkarun baya

Shekaru biyu ke nan tun bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana cutar korona a matsayin annoba a hukumance.

Tun daga wannan rana ta 11 ga watan Maris din shekarar 2020 duniya ta sauya cikin sauri - daga yanayin yadda muke aiki zuwa hanyoyin kiwon lafiyar da muke da su.

Ga abubuwa biyar da muka koya tun bayan barkewar annobar:

1. Ruwan allurar rigakafin MRNA na aiki kana za a iya kirkirar su cikin sauri

Kusan tun daga lokacin da annobar ta barke, masu bincike suka fara ruguguwar samar da ruwan allurar rigakafin da zai bai wa mutane kariya daga kamuwa da kwayar cutar da korona.

Wasu daga cikin wadannan kamfanonin harhada maguguna sun yanke shawarar amfani da irin fasahar zamanin da ba a taba aiki da ita ba wajen samar da ruwan rigakafi don amfani a kan bil adama - mRNA.

Kwalliya ta biya kudin sabulu bisa kasadar da aka yi wajen samar da allurar. Ba iya saurin samar da ruwan rigakafin korona kadai kamfanin Pfizer (daga bisani Moderna) ya yi fiye da ko wane kamfani ba ta hanyar amfani da mRNA, amma a yayin yin hakan, ya sake bude hanya ga duka hanyoyin samar da magungunan ta hanyar amfani da fasahar zamani iri daya.

Hanyoyin sun yi aiki ta hanyar daukar wani karamin tsarin kwayoyin halitta da ake kira mRNA, tare da saka shi a cikin kitse. Ta hakan ne kwayoyin halittar za su tsotse shi, da zai kuma yi amfani da ita kamar wasu umarnin samar da sabon abu.

A cikin ruwan rigakafin korona mRNA kan bai wa kwayoyin halittarmu umarni su samar da wani karamin bangare na kwayar cutar korona.

Wadannan guntattaki da ta samar, ba su da illa amma kuma garkuwar jikinmu za ta iya koya tare da gane ta don saboda ta shirya kai farmaki kan kwayar cutar korona ta gaskiya idan ka kamu da ita.

Amma kuma mRNA na da abubuwan da za a iya amfani da su ta hanyoyi da dama.

Baya ga samar da ruwan rigakafin cututtuka kamar su HIV, da mura, da Zika, za a iya amfani da shi wajen horar da garkuwar jikin mutum wajen kai hari kan kwayoyin halittun cutar kansa; wajen samar da sinadaran gina jiki na proteins da suka yi karanci a jikin mutanen da ke da matsalar cutar da ke lalata kwayoyin halittar wasu sassan jikin mutum.

An shafe shekaru da dama ana gudanar da bincike kan amfani da rigakafi ta hanyar mRNA, amma ruwan rigakafin korona su ne karon farko aka nuna sun yi aiki a yayin da ake kirkiro su.

Nasarar da aka samu ka iya kara karfin gwuiwar cigaba da gudanar da binciken da ka iya sauya rayuwar miliyoyin mutane.

2. Kwayar cutar korona na yaduwa ta cikin iskar shaka fiye da yadda da farko muka yi tunani

Kusan watanni hudu bayan sanar da barkewar annobar korona, Hukumar Lafiya ta Duniya ta wallafa a shafinta na Tuwita cewa: "FACT: #COVID19 is NOT airborne", da ke nufin cewa cutar korona ba wacce ke yaduwa ta iskar shaka ba ce.

"Babu wata tabbatacciyar shaidar da ta nuna cewa saka takunkumi da yawa na da wani tasiri," in ji babban daraktan shirin gaggawa na WHO Dakta Michael Ryan.

"Ba ma bayar da shawarar amfani da takunkumin fuska muddin ba kai kanka ne ba ka da lafiya ba," Maria Van Kerkhove, ta tawagar Covid-19 Technical Lead.

Amma abubuwan da aka koya tun bayan barkewar annobar sun sauya wadannan tunani. Yanzu WHO na cewa ya kamata mutane "su mayar da saka takunkumin fuska wani bangarensu na rayuwa a cikin sauran mutane."

Hakan na faruwa ne saboda ana samun karin shaidun cewa cutar korona ba tana yaduwa kawai ba ne daga yawu ko majina mai tarin yawa da ke cikin iskar da muke shaka na dan tsawon lokaci bayan wani ya yi tari ko atishawa, ko kuma gurbataccem wuri.

Yanzu WHO ta bayyana cewa "watakila za ta kuma iya yaduwa ta hanyar abubuwan feshi" - fiye da kananan abubuwan da za su kasance a cikin iskar da muke shaka na tsawon lokaci.

3.Da yawan mu yanzu na aiki daga gida, kuma hakan zai cigaba

An mayar da miliyoyin mutane a fadin duniya zuwa gida daga ofisoshinsu da wuraren aiki a lokacin annobar kana aka fada musu su rika aiki daga gida.

Abu ne da tunani ba zai taba dauka ba a shekarun baya kadan da suka gabata, amma cutar korona ta nuna cewa abubuwa kamar kiran waya ta bidiyo na da saukin yi ga mutane da dama.

Ya yi kama da cewa zai iya sauya yanayin yadda miliyoyinmu ke gudanar da aikinmu.

Wata kuri'ar jin ra'ayoyin kamfanoni 1,200 daga cibiyar bincike kan kasuwanci ta nuna cewa yawan ma'aikata a fadin duniya da ke aikin dindindin daga gida zai ninka a shekarar 2021.

Abin da su ma ma'aikata da dama ke son ganin ya tabbata ne.

4. Annobar ta kama mutanen da suka fi fuskantar hadari a cikin al'umma sosai

Duniya wani wuri ne marar daidaito sannan abin damuwar shi ne yadda barkewar annobar korona ta kara nuna cewa annobar za ta sa hakan ya kara muni.

A Birtaniya, wani bincike da masana suna gudanar a ya nuna cewa akasarin wadanda ke bangaren kasar da ba a kulawa da shi sosai, kashi 11 da digo hudu na mutane sun kamu da cutar korona a yayin da yankunan da ke dan samun kulawa alkaluman suka gaza hakan- wato kashi 7 da digo takwas bisa dari.

Tawagar ta kuma gano mutane daga kabilu 'yan tsiraru su ma annobar da shafe su fiye da kima, wani abu da har ila yau ya faru a Amurka.

A birnin New York, bayanan da aka tattara daga shekarar 2020 sun nuna cewa an samu mutuwar mutanen Sifaniya da bakaken fata daga cutar korona da suka hada da kashi 34 bisa dari da 28 bisa dari na yawan al'ummar.

A kasashe da dama, babu ingantattun cikakkun bayanan da aka tattara game da tasirin annobar korona, amma a fadin duniya daya daga cikin gagarumin bambanci yana tattare da alkaluman yin allurar rigakafi.

A kasashe matsakaita, da masu karfi, kusan kashi 70 bisa dari na mutanen an yi musu cikakkun alluran rigakafin, kamar yadda bayanan binciken Our World in Data ya nuna.

5. Muna da karancin tabbaci kan ta yaya, ko shin annobar korona za ta kawo karshe

Herd immunity - Idan mutane da dama suka samu garkuwa daga kamuwa da kwayar cutar korona, ko ta hanyar kamuwa da cutar ko rigakafi, kwayar cutar takan rage karfin barazana.

Hakan na kara zama da matukar wahala a cimma nasara. Ya zamana cewa yanayin garkuwar jikinmu na kara raguwa zuwa wani lokaci da ya sa kasashen da za su iya, kan gudanar da babban shirin allurar rigakafin.

Kamar yadda Shabir A Madhi, shugaban Sashen Kimiyyar Kiwon Lafiya kan allurar rigakafi a Jami'ar Witwatersrand a Afirka ta Kudu ya bayyana, abubuwan da garkuwar jiki ke yi bayan kamuwa da cuta ko rigakafi na kai wa zuwa akalla watanni shida zuwa tara.

A yayin da ruwan allurar rigakafin ke da karfin bayar da kariya daga duka wata cuta mai tsanani, ko da wadanda suka fi inganci ne ba sa iya hana mutane kamuwa da cutar korona ( duk da cewa mutanen da suka kamu da cutar ka iya nuna alamun kamuwar) tare da yada wa sauran mutane.

"Duk da irin ruwan rigakafin da muke da shi, ko da sun rage yaduwa, batun nan na herd immunity bai yi wata ma'ana ba,'' Dakta Salvador Peiró, na cibiyar bincike ta FISABIO a kasar Sifaniya ya shaida wa BBC.

Kana kwayar cutar ta yi ta saurin sauya kamanni zuwa sabbin nau'uka, wasunsu da aka gano cewa sun fi saurin yaduwa kana za su iya kasancewa mafi wuyar jin maganin rigakafin.

Nau'ukan sun kuma nuna cewa watakila dole mu koyi rayuwa da kwayar cutar a yayin da take karuwa, ta hanyar sabunta ruwan allurar rigakafin akai-akai don sabawa da sabbin nau'ukan kwayar cutar.

Read full article