You are here: HomeAfricaBBC2023 04 03Article 1743116

BBC Hausa of Monday, 3 April 2023

    

Source: BBC

'Siyasar Obi da Jam'iyyar LP ta mutu murus, saura jana'izarta'

Peter Obi Peter Obi

A Najeriya, cacar-baki ta kaure tsakanin `yan jam`iyyar APC mai mulkin kasar da na jam`iyyar Labour tun da aka ji wata tattaunawar waya tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar Labour, Peter Obi da Bishop David Oyedepo na majami`ar Living Faith Church.

A karshen mako ne jaridar People Gazzete ta wallafa wannan murya da aka kwarmata, tsakanin Peter Obi da babban Bishop David Oyedepo.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a kasar, musamman ma yadda aka ji dan takarar yana rokon malamin addinin kiristan ya taimaka wajen nema masa goyon bayan mabiya addinin kirista da ke shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da kuma shiyyar arewa ta tsakiyar kasar

Ya dai alakanta siyasar da takararsa tamkar fafutuka da suke yi yaki ne na addini, har ma ya tattabar masa cewa ba za su yi da-na-sanin goya masa baya ba.

`Yan jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya sun yi caa a kan dan takarar shugaban kasar suna cewa asirin sa ne ya tonu, kuma zargin da suke yi cewa siyasar sa ta addini da kabilanci ce ya tabbata.

A hirarsa da BBC, Mallam Ali M Ali, daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya ce 'yar manuniya ta nuna kan zargin da suka yi tun da farko na salon yadda dan takarar LP ke amfani da addini a gangamin yakin neman zabe.

''Kurunkus, siyasar Peter Obi da jam'iyyar Labor ta zo karshe, sai dai aje a yi jana'izarta watakila hakan zai zama izna ga masu amfani da banbancin addini domin raba kan al'uma, ta tabbata salon yakin neman zabensa na da nasaba da raba kawunan jama'a ta amfani da addini, domin mulkarsu.''

Tuni dai kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam iyyar Labour, Peter Obi, wato mista Kenneth Okonko ta tabbatar da gaskiyar maganar tattaunawar, amma ya ce an yi mata mummunar fahinta.

Sai dai kuma ba a je ko`ina ba, Dr Yunusa Tanko, wanda shi ma ke magana da yawun gangamin yakin neman zaben Mista Obin ya ce sautin tattaunawar da jaridar People Gazzete din ta fitar yarfe ne kawai, saboda a iya sanin su ba a yi wannan tattaunawar ba.

Shi ma Bishop Oyedepo a wani martani da ya mayar bai ce ya yi tattaunawar nan da Msita Peter Obi ba.

Kazalika bai musanta ba. Amma wasu rahotanni sun ambato shi yana cewa shi bai taba y iwa wani dan siyasa ko jam`iyya kamfe ba. Hakja kuma ba bu wanda ya taba fada masa abin da zai ce wa mabiyansa.

A Najeriya, an yi gwagwagwa da batun siyasar addini a babban zaben da ya gabata, inda jam`iyyar Labour ke yi wa APC kallon duma, ita kuma na yi Labour kallon madaci.

Yayin da wasu magoya bayan jam`iyyar Labour ke sukar APC da tsaida musulmi da muslmi a matsayin dan takaran shugaban kasa da mataimaki, wasu magoya bayan APC kuma na caccakar Labour kyamar tsarin APC saboda addini alhali kundin tsarin mulkin kasar bai hana ba.

Read full article