You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798577

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

    

Source: BBC

Sojojin Israila sun fara janye farmaki kan Falasdinawa a Jenin

Wani sojan Israila a Jenin Wani sojan Israila a Jenin

Sojojin Israila sun fara janyewa daga sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, a cewar majiyoyin tsaro.

Wannan ya kawo karshen gagurumin farmakin kwanaki biyu da aka kashe falasdinawa 12.

An ci gaba da jin karar harbe-harben da fashe-fashe a daukacin Jenin a lokacin da labarin ya bayyana.

Jami'an kiwon lafiya sun ce an harbe wani Bafalasdine yayin da rahotani sun ce hare-hare da aka kai ta sama sun jikkata mutum uku.

Tun da farko kungiyoyi mayaka masu fafitukar kwato 'yancin Falasdinu sun ce harin da aka kai da mota da wuka a Isra'ila martani ne kan farmakin.

Mahukutan Isra'ila sun ce mutane 7 ne suka jikkata a kan wani titi da ba ya rabuwa da rububin mutane a Tel Aviv kuma maharin Bafalasdine ne daga gabar yammacin Kogin Jordan

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce: "|Duk wanda ke tunanin irin wannan harin zai kawo cikas a yaƙin da mu ke yi da ta'adanci, to ya yi kuskure".

Ya kuma tabbatar da cewa sojojin Isra'ila "suna gab da kamala farmakin" da suka kai wa Jenin, amma ya yi gargadin cewa wannan ba aika ba ne da za a kammala a cikin kwana ɗaya.

Da safiyar ranar Linitin ne sojojin Isra'ila suka kaddamar da farmakin a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin tare da hare-hare ta sama daga jirgin sama mara matuki wadda ta ce ya kai hari a wata matattarar zaratan mayakan Jenin Brigades, wadda wata runduna ce da ta kunshi mayaka daga kungiyoy daban-daban ciki harda Hamas.

Jiragen sama mara sa matuka sun kuma kai hare-hare ta sama yayin da sojoji suka farwa sansanin inda suka yi bata-kashi da mayakan Falasdinu da ke ciki.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce farmakin ya maida hankali wajan kwato makamai tare da tarwatsa ɓangaren da mayaka ke amfani da shi a matsayin mabuyarsu a cikin sansanin

A wani taron manema labarai da ta kira a birnin Geneva a ranar Talata mai magan da yawun ofishin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ta ce "sun damu dangane da girmar famakin da ya kunshi hare-hare ta sama da kasa.

Ta ce ma'aikatar kiwon lafiya Falasdinu ta tabbatar cewa yara uku - samari biyu masu shekara 17 da wani matashi mai shekara 16 na cikin wadanda aka kashe kuma ta yi gargaɗin cewa ababen more rayuwar da aka lalata na nufin cewa galibin sansanin a yanzu babu ruwan sha da wutar lantarki.

Read full article