You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798601

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

    

Source: BBC

Steven Gerrard ya zama sabon kocin Al-Ettifaq ta Saudiyya

Tsohon ɗan wasan Ingila da Liverpool Steven Gerrad ya zama sabon kocin Al-Ettifaq Tsohon ɗan wasan Ingila da Liverpool Steven Gerrad ya zama sabon kocin Al-Ettifaq

Tsohon ɗan wasan Ingila da Liverpool Steven Gerrad ya zama sabon kocin Al-Ettifaq.

A watan Yuni ne mai shekara 43 ya ce an gayyace shi ƙasar domin tattaunawa kan aiki, sai dai bai karbi aikin ba a lokacin.

Tun bayan korar da Aston Villa ta yi wa Gerrad a watan Oktoban bara ya zama ba shi da aikin yi.

Al-Ettifaq ita ce ta yi ta bakwai a cikin ƙungiyoyi 16 na gasar Saudiyya a bara, ta gama da maki 35 tsakaninta da gwarzuwar gasar Al-Ittihad.

Komarwar tsohon ɗan wasan Ingilan Saudiyya na zuwa ne daidai lokacin da manyan 'yan wasan Turai ke komawa gasar Saudiyyan, ciki har da Cristiano Ronaldo, sakamakon kuɗi da aka zuba wa gasar.

Tsohon ɗan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema da Ruben Neves tsohon ɗan wasan Wolves da 'yan wasa uku na Chelsea Kalidou Koulibaly da N'Golo Kante da kuma Edouard Mendy dukka na cikin waɗanda suka koma Saudiyya.

Rahotanni sun ambato cewa kocin Fulham Marco Silva ya ƙi amincewa da tayin da ƙungiyar Al-Hilal ta yi masa na ya zama kocinta kan fan miliyan 17.

Burin shugabannin gasar shi ne mayar da gasar Saudiyya ta biyar cikin manyan gasannin da ake da su na duniya.

A 2016 ne Gerrad ya yi murabus daga buga kwallo, kuma ya fara aikin horaswa ne a kungiyar Rangers ta Scottland.

Ya an shi aikin aikin Ibrox a 2018, ya kuma sanya ƙungiyar ta lashe gasar Premier ta na farko cikin shekara 10 a 2020-21.

Daga baya Gerrad ya zam kocin Villa a watan Nuwambar 2021, ya yi nasara a wasa 13 cikin 40 da ya jagoranta.

Read full article