BBC Hausa of Monday, 4 September 2023
Source: BBC
Koci, Jose Santos Peseiro bai gayyaci Ahmed Musa a karawar da Super Eagles za ta yi da Sao Tome, a wasan neman shiga gasar kofin Afirka ba.
Ranar Lahadi 10 ga watan Satumba, Najeriya za ta karɓi baƙuncin Sao Tome a wasan rukunin farko da za su fafata a Uyo.
A wasan farko da Super Eagles ta ziyarci Sao Tome, ta ci ƙwallo 10-0.
A cikin waɗanda aka gayyata dai akwai William Ekong da Tyronne Ebuehi da Semi Ajayi da kuma Wilfred Ndidi.
Sauran sun haɗar da Frank Onyeka da Moses Simon, da Victor Osimhen da kuma Taiwo Awoniyi.
Haka kuma Peseiro ya gayyaci masu tsaron raga uku da suka haɗa da mai taka leda a gida Olorunleke Ojo da 'yan wasan baya takwas da masu buga tsakiya huɗu da masu zura kwallaye a raga su takwas.
A karon farko an gayyaci Peseiro Jordan Torunarigha da Victor Boniface da kuma Gift Orban, yayin da aka kira Bruno Onyemaechi da kuma Raphael Onyedika.
Najeriya mai maki 12 da ke jan ragamar teburin farko bayan karawa biyar, tuni ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a buga a Ivory Coast cikin 2024.
Guinea Bissau ce ta biyu da maki 10, wadda za ta karɓi baƙuncin Saliyo.
'Yan wasan da Najeria ta gayyata a karawa da Sao Tome
Masu tsaron raga:
Francis Uzoho (Omonia FC, Cyprus); Olorunleke Ojo (Enyimba FC); Adebayo Adeleye (Hapoel Jerusalem, Israel).
'Yan wasan baya:
Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England); Tyronne Ebuehi (Empoli FC, Italy); Jordan Torunarigha (KAA Gent, Belgium); William Ekong (PAOK FC, Greece); Semi Ajayi (West Bromwich Albion, England); Calvin Bassey (Fulham FC, England); Jamilu Collins (Cardiff FC, Wales); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal).
Masu buga tsakiya:
Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Joe Ayodele-Aribo (Southampton FC, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England).
Masu cin ƙwallaye:
Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Samuel Chukwueze (AC Milan, Italy); Moses Simon (FC Nantes, France); Ademola Lookman (Atalanta FC, Italy); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Taiwo Awoniyi (Nottingham Forest, England); Gift Orban (KAA Gent, Belgium); Victor Boniface (Bayern Leverkusen, Germany)