BBC Hausa of Monday, 27 March 2023
Source: BBC
Tawagar Najeriya ta je ta doke ta Guinea Bissau da ci 1-0 a wasa na hudu a rukunin farko da suka kara ranar Litinin a Bissau.
Sun buga wasan a Estadio 24 de Setembro, domin neman gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024.
Najeriya ce ta fara cin kwallo ta hannun Moses Simon a bugun fenariti a minti na 30 da take leda.
Ranar Juma'a Guinea Bissau ta doke Super Eagles da cin 1-0 a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, Najeriya.
Da wannan sakamakon Super Eagles ta koma ta daya da maki tara, bayan da ta ci Guinea Bissau da Saliyo da kuma Sao Tome.
Guinea Bissau ce ta biyu da maki bakwai, bayan da ta yi nasara a kan Super Eagles a Najeriya da cin Sao Tome da canjaras da Saliyo.
Saliyo maki biyar ne da ita a mataki na uku da Sao Tome ta karshe mai maki daya.
A cikin watan Yunin 2023 rukunin farko zai buga wasa na biyar-biyar, inda Saliyo za ta karbi bakuncin Super Eagles.
Ita kuwa Guinea Bissau za ta kai ziyara Sao Tome, sannan su buga wasannin karshe a rukuni cikin watan Satumba.
Ranar 9 ga watan Yunin 2022, Super Eagles ta doke Saliyo 2-1 a gida, sannan ta je ta dura 10-0 a ragar Sao Tome ranar 13 ga watan Yunin 2022.