You are here: HomeAfricaBBC2023 01 03Article 1689863

BBC Hausa of Tuesday, 3 January 2023

    

Source: BBC

Tasirin da Ronaldo ya jawo wa kulob-kulob a kafafen sada zumunta

Cristiano Ronaldo Cristiano Ronaldo

Bayan kasancewarsa wanda ya fi kowanne mutum a duniya yawan magoya baya a Instagram, ya ke kuma da kimanin mabiya miliyan 158 a Facebook, tasirin Cristiano ya kara bayyana bayan komawarsa kungiyar Al-Nassr da ke Saudiyya.

Kiyasi ya nuna dan wasan duniyar na da magoya baya masu yawan gaske da suke binsa babu dare babu rana sama da kungiyoyin da yake taka leda cikinsu.

Ronaldo mai shekara 37 da ya babewa da Manchester United, a karshe ya samu wata sabuwar kungiya a gabas ta tsakiya kuma ita ce Al-Nassr.

Gabanin neman da aka yi masa, kungiyar Al-Nassr na da magoya baya kimanin dubu 860, amma da sanarwar komawarsa kungiyar sai magoya bayanta suka karu cikin sa'o'i kalilan.

Ya zuwa yanzu da muke bayyana wannan rahoton kungiyar na da magoa baya miliyan bakwai da dubu dari shida, sun karu da kusan kashi 90 cikin 100.

Ba dai wannan ne karon farko da kididdiga ta nuna yadda magoya baya ke bin Cristiano ba a kafafen sada zumunta.

Lokacin da Ronaldo ya koma Juventus a kan fam miliyan 100, kungiyar ta samu karuwar mabiya a duka kafafen sada zumunta, sa'annan Real Madrid da ya baro ta yi asarar mabiya sama da miliyan cikin awa 24 kamar yadda rahoton jaridar Tifo ya bayyana.

Hakan ya yi matukar tasiri inda Juventus ta samu karuwa da kusan kashi 25 na magoya baya.

A duka shafukanta na sada zumunta kungiyar ta samu sabbin mabiya miliyan shida, wani gagarumin sauyi a gareta.

A lokacin magoya bayan sun karu zuwa miliyan 35 a Facebook, a Twitter sun kai miliyan 6.2, yayin da a Instagram suka kai miliyan 15.3.

Duk da cewa ana ganin kamar dan wasan na samun koma baya a kwallon kafa a zahiri, amma a shafukan sada zumunta har yanzu shi ne ke da wannan sarautar.

Irin wannan biyayyar da mabiya ke yi, suka nuna wa dan wasan lokacin da yake shirin komawa Manchester United.

Kuma rikicin shi da kungiyar ya haifar da koma bayan mabiya gareta a kafafen sada zumunta.

Da komawar da ya yi Al-Nassr dan wasan zai rika daukar dala miliyan 200 a duk shekara.

Dan wasan ya zama wanda za a fi biyan kudi a duk shekara a fagen kwallon kafa a duniya.

Ga jerin mutum biyar da suka fi daukar kudi a duniya:

1. Cristiano Ronaldo $214

2. Kylian Mbappe $63

3. Lionel Messi $41

4. Nyemar $37

5. Andrés Iniesta $31


Ronaldo ya isa Saudiyya a ranar Talata domin sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu, kuma tuni ɗumbin magoya baya suka yi dafifi domin yi masa maraba.

Read full article