You are here: HomeAfricaBBC2022 03 16Article 1491656

BBC Hausa of Wednesday, 16 March 2022

    

Source: BBC

Taswirar abin da ya faru cikin kwana 20 na yaƙin Ukraine

Dakarun Rasha na ci gaba da fuskantar turjiya daga takwarorinsu na Ukraine Dakarun Rasha na ci gaba da fuskantar turjiya daga takwarorinsu na Ukraine

Dakarun Rasha na ci gaba da fuskantar turjiya daga takwarorinsu na Ukraine tare da yi musu barna da dama yayin da suke kokarin zagayewa tare da mamaye Kyiv.

Ga wasu bayanai game da yakin bayan kwashe kwanaki 20 da fara shi:

  • An ji wasu fashe-fashe da suka girgiza babban birnin Ukraine na Kyiv yayin da Rasha ke ci gaba da rushe gine-gine da manyan wuraren tattalin arziki.


  • An kwashe sama da mutum 4,000 daga manyan biranen da ake yaki a Ukraine a ranar Litinin, yayin da ake shirin ci gaba da kwashe mutane.


  • Mafi yawan sojin Amurka na zaune ne a tantuna duk da tashin bamai-baman da ake samu, in ji wani babban jami'in tsaron Amurka.


  • Rasha ta kaddamar da harinta na kusan awa daya a ranar 24 ga watan Fabrairu daga kusurwa uku, arewaci da kudanci da kuma gabashi.

    An rika kai hare-hare a wurare da dama ta kasa da sama da kuma ruwa.

    Sojin ruwan Rasha sun yanke wa Ukraine duk wata hulda ta kasuwanci ta cikin ruwa yayin da ta karbe iko da ruwan nata, in ji Ministan tsaron Birtaniya.

    Rikicin da ake yi a Kyiv

    Dakarun Rasha na kokarin zagarewa tare da murkushe babban birnin Ukraine, yayin da suke kara tunkarar birnin ta ko wacce kusurwa.

    An kashe mutane biyu a wani harin sama da Rasha ta kai da ya dira cikin wani gida a kudu maso yammacin Kyiv. An kuma ruguza wasu gine-gine a Svyatoshinsky sakamakon hare-haren da aka kai, kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta fada.

    Manyan sojojin Ukraine sun ce suna wannan yaki domin fatattakar dakarun Rasha daga birnin.

    Sojojin Rasha sun kai hare-hare masu yawa a arewa maso yammacin birnin a ranar Litinin kusa da Buchan and Irpin, amma sun gaza tsallakawa kogin Irpin, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

    Injiniyoyin Rasha sun gaza gina wata kwarya-kwaryar gada da za su bi su tsallaka kogin. Sojojin Ukraine ne suka rushe gadar da ta hada Irpin da Kyiv a farkon wannan yaki domin hana dakarun Rasha tsallakawa.

    Babu dai wani yunkuri na kaddamar da hari daga dakarun Rasha a gabashin Kyiv, inda manyan sojojin Ukraine suka yi ammanar cewa an kebe wurin daga hare-hare.

    Tafiyar wahainiyar dakarun Rasha zuwa arewacin Ukraine

    Duk da cewa dakarun Rasha sun kara matsawa zuwa wasu kauyukan wajen Kyiv, mamayar da suke yi wa kudanci na tafiyar wahainiya ba kamar yadda suka yi a kudanci ba.

    Gagarumin shirin mamayar zuwa babban birnin ya fara ne daga Belarus zuwa yammaci.

    Dakarun Rasha na fuskantar matsalar kayan aiki, yayin da mai ke karewa daga motocinsu, ga kuma turjiya da suke fuskanta daga dakarun Ukraine.

    Dakarun Rasha sun yi wa birnin Sumy kawanya, sun rushe manyan ababen more rayuwa tare da katse lantarki. Gwamnan yankin ya ce za a bude kofar kai kayan agaji da zai ba da damar mutane su fice daga yankin a ranar Talata.

    Hare-hare igwa kan yankunan da mutane ke zaune a Kharkiv sun zama laifukan yaki bayan masu gabatar da kara na Majalisar Dinkin Duniya sun gudanar da bincike a kansu.

    Babban kamun da Rasha ta yi a kudanci

    Cikin gaggawa dakarun Rasha suka mamaye wurare da yawa a kudancin kasar, inda kuma suke dannawa cikin gabashi da yammacin Crimea.

    A kudu maso gabashi, ana fargabar cewa an yi wa dubban mutane gadar-zare a birnin Mariupol da ke gabar teku, wanda dakarun Rasha suka yi wa kawanya duka suka yi wa luguden wuta.

    Hakan ya janyo gagarumin tsaiko, yayin da sannu a hankali dakarun Rasha ke cin razafin mutane.

    Za a shiga birnin ne domin kai kayan agaji a ranar Talata, "za a kai dubban tan na ruwa da magani da abinci" ga kuma mutanen da aka tsare da kayan agaji cikin yanayin sanyi da ake ciki. Akalla motoci 160 suka bar garin a ranar Litinin, in ji rahotannin cikin gida.

    Rundunar sojin Ukraine ta ce ta yi kokarin dakile Rasha na yunkurin kame birnin da ke kusa da teku.

    Wakilin BBC kan harkokin tsaro Frank Gardner ya ce burin Rasha shi ne ta mamaye wannan tashar ruwa yadda hakan zai hana Ukraine samun damar karasawa Baharul Aswad.

    Dakarun Rasha na kutsawa gabashi

    Ana ci gaba da yaki a yankin Donetsk. Rasha na ci gaba da mamaye yankin cikin ruwan sanyi kamar yadda rahotanni suka ambato.

    Gwamnan yankin Donetsk ya ce an bar kusan komai a birnin sakamakon hare-haren Rasha.

    A yankin Luhansk da ke makwabtaka, an rawaito dakarun Rasha ba su yi nasara ba a wasu jerin hare-hare a Severodonetsk.

    Dubbai sun tsere ta iyakokin tudu

    Tun lokacin da aka fara wannan kutsen, kusan miliyan uku ne suka tsere daga Ukraine, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

    Wannan ne adadi mafi sauri da aka gani sakamakon yaki a nahiyar Turai tun yakin Duniya na biyu.

    Hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin rabin adadin yara ne da kuma matasa.

    Rahoto daga David Brown, Bella Hurrell, Dominic Bailey, Mike Hills, Lucy Rodgers, Paul Sargeant, Mark Bryson, Zoe Bartholomew, Sean Willmott, Sana Dionysiou, Joy Roxas, Gerry Fletcher, Jana Tauschinsk and Prina Shah.

    Game da wannan taswira

    Hukumar ta American Enterprise Institute's Critical Threats Project da kuma ta Institute for the Study of War sun ce suna sanya wadannan bayanai ne kullum saboda a san ina ne ke karkashin ikon Ukraine da kuma ikon Rasha.

    Tun daga 2 ga watan Maris wadannan bayanan da ake wallafawa kullum "na daddale yankunan Rasha da ke karkashin ikon Ukraine" da kuma "Yankunan Ukraine da Rasha ke iko da" ga kuma inda Rasha ke ikirarin tana kai wa hari.

    Domin nuna yankunan da aka mamaye kuma muna amfani da na ma'aikatar tsaron Birtaniya da kuma shafin BBC da ke bincike.

    To min kuma nuna inda aka kai wa hari ko aka samu fashe-fashe muna amfani da rahotannin da BBC ta tabbatar da su.

    Read full article