BBC Hausa of Monday, 3 April 2023
Source: BBC
Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne aka bar wa wuƙa da nama don ya yanke shawara game da lokacin cire tallafin man fetur a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar mai jiran gado, Abdul'aziz Abdul'aziz ne ya tabbatar da haka a wata hira da BBC Hausa.
Ya ce wannan mataki ne da gwamnatin Najeriya take ɗauka a yanzu saboda wa'adin mulkinta ya kusa zuwa ƙarshe. "Yau, ƙasa da kwana sittin," kenan ta miƙa mulki.
Gwamnatin Najeriya ƙarƙashin Shugaba Buhari mai barin gado ta faɗa a watan Janairu cewa a cikin wannan wata na Afrilu ne za a fara cire tallafin man fetur.
Ministar kuɗin ƙasar, Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a cikin watan Janairu, yayin wani taron tattalin arziƙi a Switzerland.
"Abin da ya fi shi ne wataƙila, wannan gwamnati ta fara cire tallafin man fetur a farkon zangon shekara na biyu, saboda zai fi nagarta idan aka cire a hankali maimakon a jira lokacin da za a cire shi gaba ɗaya," in ji ministar.
Sai dai, ga alama yanzu gwamnati mai barin gado ta tattara ta bar wa gwamnati mai jiran gado wadda za ta zo nan da ƙasa da wata biyu, don ta yanke shawara a kan lokacin cire tallafin.
A cewar Abdul'aziz Abdul'aziz, ba abin mamaki ba ne da wannan labari yake fitowa yanzu.
Duk da yake, in ji shi, bai san dalilan gwamnati mai barin gado na mayar da batun hannun shugaban ƙasa mai jiran gado ba.
A baya-bayan nan dai, ƙungiyar ƙwadogo ta TUC a Najeriya ta gargaɗi gwamnati a kan ta guji janye tallafin man fetur, daidai wannan lokaci da ta ce talakawan ƙasar na cikin mawuyacin hali da matsin rayuwa.
Ƙungiyar na ganin matuƙar gwamnati ta janye tallafin man fetur, to hakan zai ƙara wa jama'ar ƙasar ɗumbin wahalhalu da kuma ƙuncin rayuwa.
Abin da kuma ita ƙungiyar ta TUC ke cewa ba za ta amince da shi ba.
Sai dai, Abdul'aziz Abdula'aziz ya ce duk da yake, da ma can matsayin Bola Ahmed Tinubu tun lokacin yaƙin neman zaɓe, shi ne cewa za a cire tallafin man fetur, amma dai ba zai yi hakan ba, sai an yi dogon nazari.
"Na tabbata gwamnatin da za ta shigo, ba za ta yi wannan abin da ka ba, dole za a duba a gani".
"Ko da an cire tallafin man fetur, duk da ba wai ina tabbatarwa za a cire ba ne, amma idan matakin ya tabbata, to za a yi ne, ta hanyar da abin, ba zai ƙara ƙuntata wa rayuwar talakan Najeriya ba," a cewar Abdul'aziz.
Ya ce zaɓaɓɓen shugaban ƙasa lokacin da yake yaƙin neman zaɓe ya sanar cewa maƙudan kuɗin da ake kashewa da sunan tallafin man fetur sun yi yawa, kuma man ya ƙi samuwa, ga shi har yanzu ana sayensa da tsada a wasu wurare.
Rahotanni sun ce a cikin watan Yuni ne, kuɗin da aka ware don biyan tallafin man fetur da ake sha yanzu a ƙasar zai ƙare.
Ana dai ta nuna fargaba game da shirin gwamnati na janye tallafin man, yayin da ake hasashen cewa farashin man fetur a Najeriya zai iya kai wa har fiye da naira 700 a kan lita ɗaya, matuƙar aka cire tallafin.
Sai dai Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce shugaba mai jiran gado ba zai yanke wannan shawara kan tallafin ma fetur ɗin da zarar an rantsar da shi ba.
Wannan batu ne da ba za a iya yanke shawara a kansa a ranar da aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu ba, ba shawara ta mako ɗaya ko biyu ba.