BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023
Source: BBC
Tottenham ta nada Ange Postecoglou a matakin sabon kocinta kan yarjejeniyar kaka hudu.
Postecoglou mai shekara 53, ya bar Celtic, bayan lashe kofin babbar gasar tamaula ta Scotland karo biyu a jere a kaka biyu da ya yi a kasar.
Shine koci na hudu da Tottenham ta dauka tun bayan da ta kori Mauricio Pochettino, wanda ya kai kungiyar wasan karshe na gasar Champions League a 2018-19.
Daga nan ta dauki Jose Mourinho da Nuno Espirito Santo da kuma Antonio Conte dukkansu ba su kai kungiyar gurbin da take bukata ba.
Tottenham ta dade tana neman sabon wanda zai horar da ita tun bayan da ta raba gari da Conte cikin watan Maris.
Daga lokacin ta nada Cristian Stellini da kuma Ryan Mason a matakin rikon kwarya, inda Tottenham ta kare a gurbin da ba za ta samu buga gasar zakarun Turai a badi ba.
AC Milan ce ta fitar da Tottenham a Champions League din bana.
Postecoglou - shine dan asalin kasar Australia na farko da zai horar da tamaula a Premier League - ya koma kungiyar ta Ingila, bayan da ya lashe kofi uku a bana a gasar Scotland.
Kocin ya dauki kofi biyar daga shidan da ya kamata Celtic ta lashe a kaka biyun da ya ja ragamar kungiyar.
Yana daga cikin masu horar da tamaula biyar da suka lashe kofi uku a Celtic da ya hada da Jock Stein da Martin O'Neill da Brendan Rodgers da kuma Neil Lennon.
Tottenham ta dauki mako 10 tana neman wanda zai maye gurbin Conte, bayan da aka yi ta alakanta Julian Nagelsmann da Luis Enrique da Arne Slot da Graham Potter da Julen Lopetegui da Brendan Rodgers da kuma Pochettino da aikin.