You are here: HomeAfricaBBC2021 11 23Article 1407598

BBC Hausa of Tuesday, 23 November 2021

    

Source: BBC

Tsofaffin gwamnoni hudu da ke neman shugabancin jam'iyyar APC

APC ne jam'iyya da ke rike da mulki a Najeriya APC ne jam'iyya da ke rike da mulki a Najeriya

Tun bayan kammala zabukan shugabannin babbar jam'iyyar hammaya ta PDP a Najeriya hankula suka karkata kan jam'iyya mai mulki, APC, domin ganin yaddaa za ta kaya.

Hakan baya rasa nasaba da kurar da rikicin da ya barke a wasu jihohi bayan zabukan da jam'iyyar ta APC ta gudanar kamar yadda aka gani a jihohi irin su Kano da Zamfara da Kwara da dai sauransu.

Sai dai a yayin da jam'iyyar take fama da matsalolin da suka faru sakamakon zaben cikin gida, a gefe guda kuma tuni wasu manyan 'yan siyasa suka soma fafutikar ganin sun samu shugabancinta a mataki na ƙasa.

Kawo yanzu dai mutanen da aka fi jin amonsu sun hada da wasu tsofaffin gwamnoni hudu wadanda suka fito daga bangaren Arewaci.

Hakan na da alaƙa da hasashen da wasu 'yan jam'iyyar masana harkokin siyasa da ma suke yi cewa dan takarar shugabancin kasar na APC za zai fito ne daga Kudancin ƙasar.

Masu nazari kan harkokin siyasa na ganin cewa APC na bukatar kwararre, gogagge kuma jajurtaccen shugaba domin dinke barakar da ke cikin jam'iyyar.

Gwamnonin sun hadar da tsohon gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Abubakar Yari da George Akume tsohon gwamnan Jihar Benue da kuma Umaru Tanko Al-Makura, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa.

Bari muyi duba a takaice kan duka wadannan 'yan siyasa:

Abdul'aziz Abubakar Yari

Abdul'aziz Abubakar Yari, mai shekara 53, gogaggen dan siyasa ne, wanda sau biyu yana zama gwamnan Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya. Ya zama gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayun 2011 ya kuma kammala wa'adinsa na biyu a 2019. Ya taba rike shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, kafin nan ya taba riƙe shugaban jam'iyyar ANPP a jihar Zamfara.

Bayan kammala wa'adin mulkinsa na gwamna, Abdul'aziz Yari ya yi takarar Sanata a zaben shekarar 2019 kuma ya ci, amma rikicin cikin gida na jam'iyyarsu ta APC ya sa Kotun Kolin kasar ta ruguza zaben ta bai wa PDP nasara. Sai dai Abdul'aziz Yari ya ci gaba da taka rawa a bayan fage a jam'iyyar.

Ali Modu Sheriff

Ali Modu Sheriff fitaccen ɗan siyasa ne da ya fito daga Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Yana da shekara 66 a duniya.

Modu Sheriff ya riƙe mukaman siyasa daban-daban.

Tun a jamhuriya ta uku Modu Sherrif ya rike mukamin Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya karkashin jam'iyyar UNCP lokacin mulkin Sani Abacha. A 1999 lokacin jamhuriya ta hudu an kara zabar sa a wannan matsayi karkashin jam'iyyar ANPP.

A 2003, an zabi Modu Sherrif a matsayin gwamnan Jihar Borno karkashin ANPP, an sake zabensa a 2007.

Fitaccen ɗan siyasar ya sauya jam'iyyu da dama - ya fara siyasarsa ne a karkashin jam'iyyar ANPP a 2003, har zuwa 2013 amma daga bisani gamayyar wasu jam'iyyu da suka hada da CPC da ACN da kuma ita ANPP din suka dunkule suka kafa APC inda shi ma ya koma cikinta a 2014.

Daga wannan shekarar ya koma PDP har zuwa 2018, inda a PDP ya rike mukamin shugaban kwamitin zaben shugabannin jam'iyyar a 2016.

Ya samu kansa a cikin turka-turkar shugabancin jam'iyyar PDP a 2017, sai dai daga bisani Kotun Daukaka kara da ke jihar Rivers ta yi watsi da ikirarinsa na shugabancin jam'iyyar.

George Akume

Akume babban dan siyasa ne daga Jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya, wanda yake da shekara 67. Yanzu haka yana rike da mukamin Ministan Ayyuka na musamman da kuma harkoki tsakanin bangarorin gwamnati.

Ya rike matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijan Najeriya a 2011 zuwa da 2015. An zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Benue ta Arewa maso Yamma a 2011 har zuwa 2015 da aka kara zabarsa, amma a 2019 sai ya gaza kai bantensa, inda ya sha kashi a hannun dan takarar jam'iyyar APC.

Gabanin haka a 1999 lokacin da za a fara jamhuriya ta hudu, ya fito takarar gwamnan kuma ya yi nasara, inda ya kwashe shekara takwas a kan mulki.

Bayan ya fadi zabe ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da sunansa cikin wadanda za a bai wa muƙami, an kuma ba shi matsayin Ministan Ayyuka na musamman da kuma harkoki tsakanin bangarorin gwamnati.

Umaru Tanko Al-Makura

Al-Makura tsohon dan gwagwarmayar siyasa ne domin kuwa tun a 1980 ya riƙe matsayin shugaban matasa na jam'iyyar NPN lokacin karkashin tsohuwar Jihar Filato. Bayana haka, ya rike mukamai da dama na siyasa da wakilci.

Yana cikin jiga-jigan da suka kafa jam'iyyar PDP a 1998. Ya zama gwamnan Jihar Nasarawa har sau biyu inda aka zabe shi a 2011 karkashin jam'iyyar CPC sai dai daga bisani ya CPC ta dunkule cikin jam'iyyun da suka kafa APC inda ya ci gaba da jan zarensa a cikin jam'iyyar.

Masana harkokin siyasa dai na ganin za a fafata sosai wajen zaben shugabasn jam'iyyar ta APC, kuma da alama an kama hanyar zaben bayan da shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, ya sanar da cewa a watan Fabrairun 2022 za a gudanar da babban taron jam'iyyar.

Read full article