BBC Hausa of Wednesday, 25 August 2021
Source: BBC
Tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre ya rasu ranar Talata yana da shekara 79, a cewar Ministan Shari'a na Senegal, Malick Sall.
Mista Habre ya rasu ne a asibiti yayin da yake zaman gidan yari a Senegal bisa aikata laifukan yaƙi a ƙasarsa da kuma lalata rayuwar 'yan Adam.
Wata kafar yaɗa labarai ta Senegal ta ce ya rasu ne sakamakon cutar korona, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.
A lokacin da ya mulki Chadi tsawon shekara takwas, shugaban ya dinga murƙushe 'yan adawa, abin da ya jawo mutuwar mutum fiye da 40,000, a cewar masu bincike.
A shekarar 2016 ne wata kotu ta musamman - wadda ƙungiyar haɗin kan Afirka (AU) da Senegal suka kafa - ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
An zargi Habre da aikata fyaɗe da bautarwa da kuma bayar da umarnin kisa a lokacin da yake kan mulki daga 1982 zuwa1990. Sai dai ya musanta zarge-zarge.
Wata hukumar bincike da aka kafa a Chadi bayan an kifar da gwamnatinsa a 1990 ta ce gwamnatin tasa ta aikata kisan da ke da alaƙa da siyasa 40,000 da kuma azabtar da mutum 200,000 cikin shekara takwas.