BBC Hausa of Wednesday, 21 June 2023
Source: BBC
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, Uefa ta dakatar da kocin Roma, Jose Mourinho wasa huɗu.
Hakan ya biyo bayan ƙalubalantar alƙalin wasa, Anthony Taylor da ya yi a wasan ƙarshe na Gasar Europa League.
Lamarin ya faru ne a filin ajiye motoci, bayan tashi daga karawar, inda Mourinho, mai shekara 60 ya riƙa furta kalaman cewa Taylor ya yi kuskure da yawa a fafatawar.
Tun ana buga wasan a Budapest, Taylor ya bai wa kocin ɗan ƙasar Portugal katin gargaɗi, inda Sevilla ta lashe kofin a bugun fenareti, bayan da suka tashi 1-1.
An hukunta kocin ne bisa faɗar kalaman da ba su dace ba.
An kuma tuhumi ƙungiyoyin biyu wato Roma da Sevilla da laifin kasa tsawatarwa magoya bayansu a lokacin karawar.
An kuma hana Roma sayar da tikiti ga magoya bayanta a wasa ɗaya da za ta buga a waje yayin da aka fara wasannin kaka mai zuwa.
An kuma ci tarar ƙungiyar fam 47,300, bayan an tuhumi magoya bayan Roma da jefa abubuwa cikin fili da kunna abubuwan tartsatsi.