BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023
Source: BBC
Manchester United za ta buga wasan sada zumunta da Leeds United a Oslo, domin gwada 'yan wasan da za su buga mata kakar badi ta 2023/24.
Za su kara ranar 12 ga watan Yuli a filin Ullevaal a Oslo, kuma na farko da za su fuskanci juna a Norway.
Haka kuma karawar dama ce ga United, domin shirin buga wasanni hudu a Amurka, duk domin tsare-tsaren yadda za ta taka rawar gani a badi.
Wannan shi ne karo na hudu da United za ta kece raini a filin Ullevaal, bayan wasan sada zumunta a 2017 a Valerenga da 2019 a Kristiansund.
Kungiyar ta Old Trafford ta kuma kece raini da Atletico Madrid a 2022.
Wasannin sada zumunta da United za ta yi:
12 Juli da Leeds United a filin Ullevaal a Oslo
19 Juli da Olympique Lyonnais a filin BT Murrayfield a Edinburgh
Karawar da United za ta yi a Amurka:
Ranar 22 Juli da Arsenal a filin MetLife a New Jersey
Ranar 25 Juli da Wrexham a filin Snapdragon a San Diego
Ranar 26 Juli da Real Madrid a filin NRG a Houston
Ranar 30 Juli da Borussia Dortmund a filin Allegiant a Las Vegas