BBC Hausa of Wednesday, 26 April 2023
Source: BBC
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce an gano wasu tarin jabun magungunan tari da Indiya ta yi a tsibirin Marshall da ke Micronesia.
WHO ta ce gwajin maganin tarin mai suna Guaifenesin TG wanda kamfanin haɗa magunguna na QP Pharmachem Ltd da ke Punjab ya yi ya nuna yana ɗauke da "haramtattun sinadaran diethylene glycol da ethylene glycol".
Duka sinadaran na da illa ga bil adama kuma suna iya janyo asarar rai idan aka sha.
Sanarwar ta WHO ba ta bayyana ko an samu wanda ya kamu da rashin lafiya ba.
Gargaɗin na baya-bayan nan ya zo watanni bayan da WHO ta alaƙanta mutuwar yara a Gambia da Uzbekistan da sauran magungunan tari da aka haɗa a Indiya.
Sudhir Pathak, daraktan gudanarwar kamfanin na QP Pharmachem, ya shaida wa BBC cewa kamfanin ya fitar da maganin kwalba har 18,346 zuwa Cambodia bayan da ya samu dukkan amincewar hukumomi. Ya ce bai san yadda aka yi maganin ya kai tsibirin Marshall da Micronesia ba.
"Ba mu aika waɗannan kwalaben maganin zuwa yankin Pacific ba kuma ba a amince a yi amfani da su a can ba. Ba mu san ta yadda aka yi maganin ya tsinci kansa a tsibirin Marshall da Micronesoia ba," in ji shi, inda ya ƙara da cewa kamfanin ya tura sanarwa zuwa ga kamfanin da ya fitar da magungunan zuwa Cambodia.
Sanarwar ta WHO ta ce maganin, wanda ake amfani da shi wajen warkar da cushewar ƙirji da alamomin tari, hukumar da ke tabbatar da ingancin magunguna ta Australiya, Therapeutic Goods Administration, ta yi gwaji akansa.
Kamfanin Trillium Pharma da ke da mazauni a jihar Haryana ne ya tallata maganin.
BBC ba ta samu tuntuɓar wakilin Trillium ba a waya. Gwamnatin Indiya kuma ba ta ce komai ba game da gargaɗin na yanzu.
Sanarwar ta ƙara da cewa "babu guda cikin kamfanin haɗa maganin da mai tallata shi da suka bai wa WHO tabbaci kan ingancin magungunan".
Indiya ce kasa mafi girma a duniya wajen fitar da magunguna na yau da kullun, tare da biyan yawancin bukatun lafiya na kasashe masu tasowa.
Sai dai a watannin baya-bayan nan, kamfanonin Indiya da dama na fuskantar bincike saboda ingancin magungunansu inda ƙwararru ke bayyana damuwa game da hanyoyin da ake bi wajen haɗa waɗannan magungunan.
A watan Oktoba, WHO ta fitar da wata sanarwar gargaɗi a duniya inda ta danganta wasu magungunan tari guda huɗu da kamfanin Maiden Pharmaceuticals ya haɗa da mutuwar yara 66 sakamakon matsalar ƙoda a Gambia.
Gwamnatin Indiya da kamfanin na Maiden Pharmaceuticals sun musanta zarge-zargen.
A watanm Maris, Indiya ta soke lasisin wani kamfanin haɗa magunguna wanda aka danganta maganin da yake haɗawa na mura ga mutuwar yara 18 a Uzbekistan.
A farkon watan nan, Hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta Amurka (FDA) ta ce ta gano cewa kamfanin na Indiya da ke haɗa maganin ciwon ido na da alaƙa da mutuwar mutane uku a Amurka wanda kuma aka gano ya saɓa da ƙa'idojin tsare lafiya.