BBC Hausa of Sunday, 2 July 2023
Source: BBC
Abubuwa da dama sun faru a Najeriya a makon da ya gabata, ciki har da bukukuwan Babbar Sallah da kuma miliyoyin 'yan ƙasa da suka faɗa cikin taluci sakamakon tsadar rayuwa.
Wannan maƙala ta duba wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon.
Duk da tsadar rayuwa 'yan Najeriya sun yi layya a bikin Babbar Sallah
Larabar nan ne aka gudanar da Sallar Layya, a sassan duniya daban-daban, bayan miliyoyin Musulmin da suka je aikin Hajji sun yi hawan Arafa a jiya Litinin, tare da yin dawafin hajji ranar Laraba.
Wani muhimmin abu yayin wadannan bukukuwa shi ne yin layya.
Bayan kammala sallar idi Musulmai masu hali suka yanka dabbobin da suka tanada don yin layya.
Biki ne da ake gudanarwa sau daya a shekara, inda jama'a ke dafa abinci, a ci a sha a yi hani'an, a kuma ziyarci 'yan uwa da abokan arziki.
Hatta wadanda ba su samu yin layya ba kan yi watanda, wato a hada kudi a sayi wata dabba don a yanka a raba.
Wasu kuwa da Ubangiji bai huwace masu ba sukan samu kyautar nama daga 'yan uwa da abokan arziki don suma su gurje bakinsu, tun da kamar yadda Hausawa kan ce ne, Sallah biki daya rana.
Baya ga rabon naman da aka yanka na layya, akan kuma yi girki na gani na fada, a kuma yi ta aika wa 'yan uwa da abokan arziki albarkacin wannan rana.
Ga cikakken labarin a nan:
Ƙarin 'yan Najeriya miliyan huɗu sun shiga talauci - Bankin Duniya
Ƙarin 'yan Najeriya kimanin miliyan hudu ne suka sake auka wa ƙangin talauci a cikin wata biyar na farkon wannan shekara saboda tsadar rayuwa, in ji Bankin Duniya.
Babban masanin tattalin arziƙi na bankin a Najeriya, Alex Sienaert, ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a Abuja yayin wani nazari kan tattalin arziƙin Najeriya a cikin rabin shekara.
Katafariyar cibiyar hada-hadar kuɗin ta yaba da sauye-sauyen da Najeriya ke yi ciki har da cire tallafin man fetur da dunƙule kasuwannin canji da shugaba Bola Tinubu ya yi a baya-bayan nan, wanda ta ce zai iya alkintawa ƙasar kuɗi kimanin naira tiriliyan 3.9 ($5bn) a bana kaɗai.
Babban Bankin ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙin na da muhimmanci wajen sake farfado da tattalin arzikin Najeriya wanda tuni ya galabaita, ko da yake matakan na iya gigita al'amura cikin gaggawa ta hanyar haddasa ƙarin hauhawar farashi da tsadar rayuwa.
A cewar Hukumar ƙididdiga ta ƙasar, sama da ‘yan Najeriya miliyan 130 ne wato fiye da rabin al’ummar ƙasar ke fama da talauci a halin yanzu.
An sauya wa mahajjatan Najeriya 10,000 matsuguni a Saudiyya
Hukumomi a Saudiyya sun kammala shirin mayar da alhazan Najeriya 10,000 zuwa wani yanki a Mina saboda ƙorafi a kan rashin isassun tantunan maniyyatan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa, an gudanar da sabon tsarin ne bayan tattaunawa da jami’an Muttawwif, waɗanda ke da alhakin kula da jin dadin alhazan Afirka da ba Larabawa ba a masarautar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa alhazan Najeriya da ke gudanar da aikin Hajjin bana sun rasa abin yi a Mina, wurin da mahajjata ke zama kafin su wuce Dutsen Arafat.
Ta ambato jami'in NAHCON, Mousa Ubandawaki, na cewa matakin ya zo ne bayan ƙorafin da aka kai wa Muttawwif wanda ya haɗa da rashin isasshen abinci da kuma jinkirin ciyar da alhazai.
“Muttawwif yayin da yake ba da haƙuri kan abin da ya faru ga mahajjatan Najeriya, ya yi alkawarin mayar da alhazan zuwa filin wasa na Turkiyya wanda zai iya daukar kimanin mahajjata 10,000 cikin sauki.”
Ba za mu bari a ƙara kuɗin man fetur a Najeriya ba - 'Yan fafutuka
Wata gamayyar ƙungiyoyin fararen hula ranar Juma'a ta ce za ta bijire wa shirin ƙara farashin man fetur da ake zargin ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya (IPMAN) na ƙoƙarin yi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ambato wata sanarwa da haɗin gwiwar, Dr Basil Musa da Mallam Haruna Maigida suka fitar na cewa za su bijirewa yunƙurin IPMAN, na ƙara farashin litar man fetur zuwa N700 ta hanyar rufe gidajen man IPMAN da ke faɗin Najeriya.
Ƙungiyoyin dai sun haɗar da Oil and Gas Transparency and Advocacy Group da Civil Society Coalition for Economic Development (CED), da Centre for Citizens Rights da Centre for Good Governance Advocacy da kuma Action against Corruption in Nigeria, da sauransu.
Sun dai zargi IPMAN da zama kishiyar gwamnati da ƙara tsanani a kan talakawan Najeriya, ta hanyar ƙarin farashin man fetur su kaɗai.
Gamayyar ƙungiyoyin ya ce shirin ƙara farashin man abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da IPMAN daga abin da ta yi zargin cewa ci da gumin talakawan Najeriya ne.
Sun kuma ce matakin wani zagon ƙasa ne ga tattalin arziƙin ƙasar don kuwa ya zo ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya har yanzu ke ƙoƙarin farfaɗowa daga halin gigitar da suka shiga bayan ƙara farashin man fetur na ranar 29 ga watan Mayu.
Rikici kan kujerar shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattijai
Sanatocin jam'iyun adawa sun sha alwashin kin amincewa da duk wani yunkuri na kawo cikas ga shugabancin marasa rinjaye a majalisar dattawa.
Manyan mukamai hudu da aka ware wa jam'iyyun adawa a Majalisar Dattawa su ne shugaban marasa rinjaye da mataimakinsa da mai tsawatarwa da kuma mataimakinsa.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da sanatocin suka fitar, sun ce ɓangaren marasa rinjaye na majalisar dattawan za su zaɓi shugabanninsu bayan tuntubar jam'uyyunsu ba tare da katsaladan daga wurin wasu da ke adawa da tsarin mulkin dimokuradiyya ba.
Sun nanata cewa har yanzu babu wani sanata da aka amince da shi ko aka zaɓa a matsayin wanda za a bai wa waɗanan mukamai.
Sanatocin da suka saka a hannu a cikin sanarwar sun haɗa da Mohammed Adamu Aliero da Henry Seriake Dickson da Aminu Waziri Tambuwal da Abdul Ningi da Patrick Abba Moro da Ezenwa Francis Onyewuchi da Kawu Sumaila da kuma Ifeanyi Ubah.
Sanata Kawu Sumaila ya yi ikirarin cewa wasu ne suke son su raba kawunan 'yan majalisar dattawan amma ba za su lamunta da shi ba.
Karanta cikakken labarin a nan:
Alƙawarin da Nuhu Ribadu ya ɗauka bayan kama aiki a matsayin mai bai wa Tinubu shawara kan tsaro
Mallam Nuhu Ribadu, mataimakin babban sufeton 'yan sanda (mai ritaya) a hukumance ya karɓi aikin Mashawarcin Tsaron Ƙasa a Najeriya daga Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).
Yayin wata ganawa ranar Litinin a Abuja, Ribadu bayan kama aiki, ya yi alƙawarin zage damtse don cika burin da 'yan Najeriya ke da shi da kuma tabbatar da tsaron ƙasar daga duk wani nau'in rashin tsaro kama daga ayyukan ta'addanci da 'yan fashin daji da satar mutane don neman kuɗin fansa da sauransu.
“Za mu daidaita al'amuran ƙasar nan, za mu tabbatar da tsare ƙasar nan kuma mu tabbatar da zaman lafiya a Najeriya saboda mun yi imani lokaci ya zo da ƙasar nan za ta ci moriyar zaman lafiya da dawo da kwanciyar hankali da zaman doka kamar dai kowacce ƙasa a duniya,” Ribadu ya ce a cikin jawabinsa.
“Tsaron ƙasa, al'amari ne da ake ci gaba da ginawa. Za mu yi nazari a kan ƙoƙarin da aka rigaya aka yi kuma mu ɗora a kai.
“Shugaban ƙasa ya ɗauki babban nauyi na tabbatar da tsaron duk wani taku na ƙasar mu. Za mu yi aiki da duk wani mai ruwa da tsaki don tabbatar da ganin an cika wannan buri.
“Wannan gagarumin aiki na tabbatar da tsaron ƙasarmu, nauyi ne a kan duk ɗan Najeriya da ma dukkan abokan ƙawancen Najeriya,” ya faɗa a cikin wata sanarwa daga ofishin Mashawarcin tsaron ƙasar.
Ma'aikatan Jihar Benue sun samu albashi karon farko cikin wata bakwai
Ma’aikata a jihar Benue sun nuna matuƙar farin ciki bayan sun karbi albashin wata daya daga gwamnatin jihar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito wasu ma’aikatan gwamnati a Makurdi, babban birnin jihar, na cewa albashin ya fara shiga asusun ajiyarsu ne tun ranar Lahadi bayan sun kwashe wata takwas ba tare da an biya su ba.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta kasa reshen jihar Binuwai, Terungwa Igbe, ya tabbatar da cewa an biya ma’aikatan gwamnati albashin wata daya.
Amma a halin da ake ciki wasu rukunin ma'aikata da suka haɗar da malaman makaranta da ’yan fansho sun ce har yanzu ba su ga albashinsu ba.
Mafi yawan malaman da aka zanta da su, sun bayyana cewa su ma, suna sa ran cewa za a biya su nan ba da jimawa ba.
An yi tir da kisan wanda ake zargi da yin kalaman ɓatanci a Sokotog
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su tabbatar an gurfanar da wadanda suka kashe wani mutum a jihar Sokoto bisa zargin kalaman ɓatanci, a gaban kuliya.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta yi Allah-wadai da kisan, ta kuma buƙaci gwamnati da ta binciki lamarin wanda ta bayyana a matsayin ‘mai ban tsoro’.
A cewar sanarwar, “Ƙaruwar kashe-kashen batanci na buƙatar ganin hukumomi su tashi tsaye wajen tabbatar da doka da mutunta haƙƙoƙin bil’adama, wadanda suka hada da ‘yancin yin addini, ra’ayi da fadin albarkacin baki.”
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa Ahmad Rufa'i mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Sakwato ya ce, a ranar Lahadi 25 ga watan Yuni ne wasu fusatattun matasa suka kashe mutumin mai suna Usman Buda, bisa zargin sa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu.
ASP Ahmad Rufa’i, ya ƙara da cewa da isar su waɗanda suka ƙona shi suka tsere daga wurin tgare da barin mutumin, inda ya rasu bayan an kai shi a asibiti.
A martanin da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya mayar, "ya yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu da bin doka da oda a kowane lokaci."