You are here: HomeAfricaBBC2021 08 29Article 1344025

BBC Hausa of Sunday, 29 August 2021

    

Source: BBC

Wane ne Shugaban Jam'iyyar PDP a yanzu?

Uche Secondus (hagu) da Yemi Akinwonmi Uche Secondus (hagu) da Yemi Akinwonmi

A makon nan ne wata babbar kotu a Jihar Ribas da ke kudancin Najeriya ta dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na kasar Uche Secondus.

Tun bayan dakatar da Mista Secondus ne ƴayan jam'iyyar suka shiga rububi domin ganin yadda za a ci gaba da tafiyar da jam'iyyar.

Kwanaki kaɗan bayan kotun ta dakatar da Mista Secondus, sai jiga-jigan jam'iyyar ta PDP suka tabbatar da Elder Yemi Akinwonmi a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyyar.

Sai dai wasu na kallon Elder Yemi a matsayin wanda ba zai iya jagorantar jam'iyyar ba, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita ta shanyewar ɓarin jiki wanda hakan ya sa ya gaza halarta wani taron kwamitin gudanarwar da jam'iyyar ta kira, inda nan take ɗayan mataimakin jam'iyyar daga arewa, Sanata Sulaiman Nazif ya jagoranci zaman kwamitin.

Kwatsam kuma a ranar Alhamis sai wata babbar kotu a Birnin Kebbi ta yanke hukunci bayan wasu mutum uku sun shigar da jam'iyyar PDP da Uche Secondus ƙara, inda a halin yanzu kotun ta bayar da umarnin mayar da Uche Secondus a matsayin shugaban na PDP.

Wannan lamari dai ya jawo ruɗani inda ake tababa kan ko wane ne shugaban PDP a halin yanzu.

A yanzu dai ga Uche Secondus kotu a Ribas ta dakatar da shi, wata kotu a Birnin Kebbi kuma ta dawo da shi, ga kuma muƙadashin jam'iyyar wanda aka ba riƙo wato Elder Yemi Akinwonmi ba shi da lafiya wanda hakan ya sa aka samu wani sabon shugaba daga arewa ya wakilce shi a wani taro.

To ko wane ne shugaban jam'iyyar a yanzu?

Matsayar PDP

Da alama dai har yanzu akasarin jiga-jigan jam'iyyar PDP ba su amince da wannan sabon hukuncin na kotun birnin Kebbi ba.

Domin kuwa, a tattaunawar da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi a ranar Juma'a da ƴan jarida, ya bayyana cewa har yanzu jam'iyyarsu ba ta samu takarda a rubuce daga kotun Birnin Kebbi ba kan batun sake mayar da Uche Secondus, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sakatare Janar na PDP Umar Ibrahim Tsauri ya ce tsarin mulkin jam'iyyar ya ba da damar idan shugaba baya nan wa zai maye gurbinsa.

"Kotuna biyu sun ba da mabambantan hukunci, amma lauyoyi sun ce mana a irin wannan yanayi na umarnin kotun duka babu wanda zai zama laifi idan an bi shi."

Ya ƙara da cewa a yanzu an bai wa lauyoyi dokar da Mista Secondus ya kawo wacce kotu ta yanke, yanzu ana jira su bai wa jam'iyya shawarar abin da za ta yi.

"Kotu ba ta warware matsalolin siyasa, kullum siyasa ita ke warware matsalolinta. Yanzu so ake a samu matsaya a cikin gida don warware matsalolin da suke gaban kotun ba sai an je kotu ba," kamar yadda ya ce.

Me masana shari'a ke cewa?

Bisa wannan lamari, BBC ta tuntuɓi Barrista Al Zubair Abubakar, wanda lauya ne a jihar Kaduna kuma inda ya ce a halin yanzu, hukuncin da PDP ya kamata ta yi amfani da shi shi ne hukuncin farko wato wanda kotun Ribas ta yi.

Inda ya ce hakan ne ma ya sa aka damƙa shugabancin ga wasu, kuma hukuncin na kotun Ribas ɗin ya sa an kori Mista Secondus din daga mazaɓarsa.

Barrista Al Zubair ya ce da a ce kotun ɗaukaka ƙara ce ta yanke wannan hukunci na biyu, da sai a ce uwar jam'iyyar PDP ta bi sabon hukuncin da aka yanke, amma a cewar Barrista, duka kotunan biyu wato ta Ribas da ta Birnin Kebbi matsayinsu ɗaya.

"Kotun Fatakwal za a bi kafin kafin a samu daidaito tsakanin kotuna biyun," in ji Barrista.

Ko da BBC ta tambayi Barrista me ya sa ake samun hukunce-hukunce daban-daban daga kotuna irin waɗannan masu karo da juna sai ya ce, "Babu mattara ɗaya da ake ajiye shari'un da muke da su wato central registry, watakila alƙalin zai iya cewa bai san da hukuncin ba amma kuma lauyoyin da su waɗanda suka yi ƙarar sun sani, domin ba za su ce ba su sani ba".

Read full article