You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848692

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

    

Source: BBC

Wane zaɓi ya rage wa Abba Kabir Yusuf a Kano?

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf

Tun bayan da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta soke zaɓen da aka yi wa Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan jihar Kano mutane ke tantamar wane zaɓi ne ya rage masa?

Kotun dai ta ce tsohon mataimakin gwamnan, Nasir Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC ne ya lashe zaɓen, bayan soke ƙuri'un da aka bayyana a matsayin na aringizo daga ɓangaren jam'iyyar NNPP.

Mataki na gaba da Gwamna Abba Kabir da jam'iyyar NNPP za su iya ɗauka shi ne na ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.

Daga nan ma duk wanda hukuncin bai masa daɗi ba zai iya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli.

Mene ne matsayin Abba Kabir a yanzu?

Abba Kabir Yusuf zai ci gaba da kasancewa a muaƙaminsa na gwamnan jihar Kano har sai an kai ƙarshen ƙarar, idan shi, ko jam'iyyar NNPP ta yanke shawarar ɗaukaka hukuncin da aka yanke.

Wani ƙwararren lauya a Najeriya Dr. Sulaiman Santuraki ya ce "Abba zai ci gaba da zama gwamna har sai an ɗaukaka ƙara, kuma ba zai ajiye muƙaminsa ba har zuwa lokacin da za a kai ƙarshen shari'ar a kotun ƙoli."

Mene ne matsayin Nasir Gawuna?

Dr Santuraki ya ce "yanzu Nasir Gawuna na a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano wanda kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta tabbatar."

"Sai dai ba za a rantsar da shi ba har sai idan an kammala sauraron ƙara a kotuna na gaba."

Sai dai kuma ya ce za a iya rantsar da Nasir Gawuna nan da kwana 21 idan har gwamna Abba Kabir Yusuf ko jam'iyyarsa ta NNPP ba su ɗaukaka ƙara ba.

Shari'ar ta zaɓen gwamnan jihar Kano ta ja hankalin al'umma sanadiyyar hamayya mai ƙarfi da ke tsakanin jam'iyyun biyu (APC da NNPP) da kuma rawar da iyayen gidansu ke takawa a siyasar Najeriya.

Kano ce jiha ta biyu mafi yawan masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya.

Abba Kabir Yusuf dai ya kayar da Nasir Yusuf Gawuna ne a zaɓen da aka gudanar a watan Maris na shekara ta 2023.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa ta ce Abba ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Yusuf Gawuna ya samu ƙuri'a 890,705.

Read full article