You are here: HomeAfricaBBC2023 04 28Article 1757177

BBC Hausa of Friday, 28 April 2023

    

Source: BBC

Wasan kwaikwayon Somalia da ya fito da matsalolin da ba a iya magana a kansu

Hoton alama Hoton alama

Shin wa zai naɗi wasan kwaikayo mai dogon zango na Talabijin mai kashi 10 a birnin da ya fuskanci rikicin shekaru 30, da matasan da ba su taɓa shiga fim ko wasan kwaikwayo ba?

Amsar ita ce Ahmed Farah.

Shi ne daraktan wasan kwaikwayo na Arday ko "Ɗalibi", wanda aka naɗa a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, kana aka kaddamar a ranar Alhamis a tashar talabijin na Bile na kasar.

Ya yi fito-na-fito da wasu daga cikin abubuwa mafi cike da ce-ce-ku-ce a ƙasar, da suka haɗa da fina-finan batsa, da fyade, da miyagun kwayoyi da kuma ‘yan daba ‘yanmata – duka haramtattun abubuwa a kasar ta Somalia.

Ko wane kashi mai mintuna 25 na wasan kwaikawyon na mayar da hankali ne kan wasu ɗaliban makarantun gaba da sakandare da yadda suke fama da ƙalubalen duniya a yayin da suka girma cikin ta.

Farah ya samu kwarin gwiwar rubuta labari bayan kallon matasan Somalia a manahajar TikTok.

"Wadannan su ne abubuwan da suke magana a kai,’’ ya ce. ‘’ Wannan shi ne ainihin gaskiyarsu kuma ina son ba su damar magana.

"Matasa a Somalia ba a gani ko jin muryoyinsu. Kashi saba’in cikin dari na yawan al’ummar Somalia ‘yan ƙasa da shekaru 30 ne amma kamar ba sa nan,’’ a cewarsa. ‘’ Taurarinmu su ne ‘yan siyasa. Sun kankane komai.’’

An fito da wata tauraruwar wasan kwaikwayo na Arday, mai shekaru 21 Shukri Abdikadir fili zuwa idanuwan jama’a.

Tana aiki a wani gidan cin abinci a birnin Mogadishu, kafin ta samu aikin wasan kwaikwayo.

"Ba yi min wani gwaji ba,’’ ta ce.

"Na raka ƙawayenna ne da ake yi musu gwajin shiga wasan kwaikwaayon lokacin da daraktan ya hango ni. Ya ce ya ga wani abu a tare da ni, ya nemi in shiga ciki, ya ba ni wani ɓangare mafi cike da ce-ce-ku-ce, mace ‘yar banga.’’

Farah, wanda ya shirya fim ɗin Ayaanle cikin harshen Somalia da gagarumar nasara, ya samu gagarumin karfin gwiwar naɗar duka fim ɗin a birnin Mogadishu da matasan da ba su goge ba daga tsakanin shekaru 16 zuwa 21.

An biya ‘yan fim din 60 alawus na watanni ukun da ya shafe kafin a kammala naɗa, kamar yadda Farah ya horar da matasan Somalia 18 a matsayin ma’aikata.

Fim din mai dogon zango na tsakiyar farfaɗo da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Somalia da a baya ta bunƙasa, wacce yaƙin da aka shafe shekaru ana gwabzawa ya ɗaiɗaita – fitattun gidajen sinima sun ruguje sakamakon harbe-harbe da lugudan wuta babu kakkautawa.

Yaƙar cin zarafi ta hanyar naɗar bidiyon batsa

Daya daga cikin jigon labarin shirin shi ne bai wa wata budurwa miyagun kwayoyi da yi mata fyade a wani wurin dabdala.

Abokan karatunta ne da suka yi ƙoƙarin yi mata barazanar yaɗa shi a shafin intanet muddin ba ta biya su wasu kuɗi.

Kamar a sauran wasu wuraren a duniya, yaɗa bidiyon matan da aka ci zarafi ta hanyar lalata wata babbar matsala ce da ke ƙaruwa a Somalia.

Maza kan biya kuɗi don su riƙa kallon fina-finan da aka saka a tashoshin Telegram. An ɓata rayuwar waɗanda lamarin ya shafa. Ba za su iya yin aure ba. Yakan tilasata wa wasu daga cikinsu shiga shan miyagun kwayoyi.

"Iyayenmu da al’ummarmu ba sa son mu riƙa magana game da waɗannan abubuwa,’’ a cewar Badria Yahya, ɗaya daga cikin taurarin fim din na Arday.

"Amma muna yi ne don mu fargar da su zuwa gaskiyar abubuwan da ke faruwa.’’

Mai shekaru ashirin da ɗaya Badria ta daɗe yana son ta shiga wasan kwaikwayo. ‘’ Na kan riƙa gwada wasan kwaikwayo da kannena,’’ ta ce. ‘’ Na yi matuƙar shakku da fina-finan Bollywood na Indiya da ya sa a yanzu haka ina yi magana da harshen Indiyanci.’’

Ita da Abdikadir sun fuskanci adawa mai zafi daga iyayensu kan amincewa da shiga cikin shirin.

Wasu iyalai sun haramta wa ‘yayansu yin duk wata mu’amala da shi baya da suka kalli sakamakon farko na nadar fim din.

‘’Wasu sun tsane ni saboda shirya wannan wasan kwaikwayo. Suna kira na da sunan mai cin amanar ƙasa, wanda ƙasashen Yamma suka biya don in lalata al’adunmu,’’ in ji Farah.

Wannan shi ne karon farko da aka naɗi fim mai dogon zango na kasar Somalia a manyan titinan birnin Mogadishu.

"Babban tashin hankali ne," a cewar Farah.

"Mutane basu taɓa ganin abu irin wannan ba. Naɗar fim wani babban ƙalubale ne. ‘Yan Somalia masu wucewa kan riƙa magana da ƙarfi don haka akwai, har da su kiran sallah daga masallatai a wasu lokutan ma har da ƙarar harbe-harben bindiga.’’

Da yawan al’ummar birnin Mogadishu sun saba jin ƙarar bindiga, shi yasa da dama ba su cika damuwa ba idan suka ji ƙarar bindigogin bogin da ake amfani da su lokacin naɗar fim.

"Dole sai muna amfani da bindigar gaskiya tare da harbawa a sama don su natsu,’’ a Farah.

Ɗaya matsalar ita ce faɗa tsakanin ‘yan fim ɗin, musamman matasa mata.

"A wasu lokutan su kan fara dukan juna tare da jan gashin juna,’’ in ji Farah. "Na yi barazanar cire su muddin suka ci gaba da fadan. Hakan ya wadatar wajen dakatar da wasu daga cikinsu amma dole sai da na cire wasu saboda sun ƙi jin magana.

"Idan na shirya fim a kan yadda aka naɗi wannan shirin zai samu kasuwa.’’

'Ya fi kyau ka yi rayuwa kamar zaki’

A birin da mutane ba su san ko za su dawo gida a raye da yamma ba, inda za su iya cin karo da harin mayaƙan al-Shabab ko harbi a shingen binciken ababan hawa, a wasu lokuta naɗar fim kan haifar da damuwa.

A yayin naɗar wani bangare na fim inda wata budurwa ta haɗu da wasu samari na kallon bidiyon batsa a wurin cin abinci na makaranta, ta ci gaba da kuka sosai har sai da fim din ya tsaya.

"Samarin su ma sun yi ta kuka,’’ in ji Farah. "Sun shafe tsawon minti 30 suna kuka bayan da muka kashe kyamarorin. Wani bangare ne na yin gwaji a gare su.’’

Taurarin fim ɗin su ma sun gaza tsayawa naɗar bangaren fim ɗin harin ƙunar baƙin wake.

A watan Oktobar bara, wasu taurarin fim din sun tsallake rijiya da baya a wani gagarumin harin bam na mota. Ya faru ne mintoci kaɗan bayan da suka karbi tufafin wasan fim ɗin daga wani gini a wurin da fashewar ta auku wanda ya hallaka akalla mutane 100.

Arday ya kuma shawo kan matsalar cutar taɓin hankali, ɗaya daga cikin haramtaccen abu a Somalia.

Ɗaya daga cikin ‘yan wasan a cikin fim ɗin likita ce a fannin halayyar ɗan adam da ke aiki a makarantar.

Ɗaliban sun bayyana mata abin da ke ran su. Wasu daga cikinsu sun riƙa magana da ita tun kafin kyamarori su dakatar da naɗar fim ɗin.

Yanzu ta fahimci abinda ke faruwa a ciki, a matsayinta na mai aiki a gidan binci a baya, yanzu Shukri Abdikadir ba za ta tsaya ba har sai ta cimma burinta na zama tauraruwar fina-finai duk da cewa naɗar fim din ya fito da abubuwa na sosa rai haɗe da nuna adawa daga iyalai.

"Idan hanya kadai da ta rage da zan iya shiga fim ita ce a sararin samaiya, zan yi,’’ ta ce, idanuwanta na kiftawa a yayin da ta ke kallon taurari a sama. ‘’Ya fi kyau ka yi rayuwa a matsayin zaki na rana daya a maimakon ka yi rayuwar kwanaki 1,000 a matsayin mage.’’

"Sai na ganki a fina-finan Hollywood," na bayyana a lokacin da ta ke tafiya a cikin duhun daren birnin Mogadishu. Ta juyo ta yi min wani irin wawan kallo.

"Ba Hollywood ba, Sollywood," ta ce.

Read full article