You are here: HomeAfricaBBC2023 04 14Article 1749269

BBC Hausa of Friday, 14 April 2023

    

Source: BBC

Wasu jerin 'yan kulob daya da suka bai wa hammata iska

'Yan wasan Bayern Munich guda biyu, Sadio Mane da Leroy Sane 'Yan wasan Bayern Munich guda biyu, Sadio Mane da Leroy Sane

Ranar Laraba Sadio Mane da Leroy Sane suka yi fada a dakin hutun 'yan wasa, bayan tashi daga Champions League, kamar yadda wasu jaridu suka wallafa.

Manchester City ce ta doke Bayern Munich 3-0 a wasan farko zagayen quarter finals a gasar zakarun Turai a Etihad.

Kamar yadda Bild da Sky da wasu jaridun Jamus suka wallafa, 'yan wasan biyu sun bai wa hammata iska, bayan tashi daga karawar har sai da aka shiga tsakaninsu.

Bild cewa ta yi Mane ya naushi Sane tsohon dan kwallon City a fuska, har lebensa ya dan tsage.

Ba wannan shine karon farko da aka yi fada tsakanin 'yan kungiya daya ba, ko dai a wajen atisaye har a filin wasa ko bayan an kammala gasa.

Wasu lokutan sai ka tsaya ka yi tunani me zai sa 'yan kungiya daya su yi fada a tsakaninsu har da dukan juna.

Ga jerin wasu daga fada da aka yi tsakanin 'yan kungiya daya:

Ibrahimovic da Onyewu

Zlatan Ibrahimovic ya yi kaurin suna wajen fada da abokan taka ledarsa, ya taba yi wa Rafael van der Vaart barazanar zai karya masa kafa a Ajax ya kuma naushi Jonathan Zebina a fuska a Juventus.

To sai dai wanda ya fi mune shine wanda ya yi a AC Milan, inda ya yi fada da Oguchi Onyewu, wanda ke taka leda aro a Newcastle United daga kungiyar Italiya.

Batty da Le Saux

Blackburn Rovers ta kasa taka rawar gani a Champions League, bayan lashe Premier League.

A lokacin ta ziyarci Spartak Moscow a wasa na biyar a cikin rukuni, bayan kasa yin nasara a fafatawar rukuni.

A Rashan an ci Blackburn 3-0 a wasan ne David Batty da Graeme Le Saux suka dunga dukan juna da kyar aka raba su.

Drinkwater da Jota

Ba za ka taba cewar 'yan wasan da suka yi zaman benci za su bai wa hammata iska ba, abin da ya faru tsakanin Drink Water da Jota kenan a wajen atisaye.

Kwana daya tsakani da Aston Villa ta ci Leicester City 4-0 - 'yan wasan Leicester da ba su buga karawar ba na atisaye a Bodymoor Hearth - sai cece kuce ya barke tskanin Drinkwater da Jota, inda 'yan wasan Ingila suka yi wa kansu gwarai, sai da aka shiga tsakaninsu.

Lloris da Son

Tottenham ta yi nasara a kan Everton da cin 1-0 a Yulin 2020, amma batun da ya fi jan hankali bayan hutu shine rigima tsakanin Gugo Lloris da Son Heung-min.

Golan Tottenham ya tuhumi Son da kin dawowa ya tare kwallo - daga baya suka barke da kokawa har sai da Giovani Lo Celso da Harry Winks suka shiga tsakini, da aka tashi daga wasan sun rungumi juna.

Bayan tashi daga wasan koci, Jose Mourinho ya ce abin da ya faru abin ban sha'awa ne.

Akwai karin bayanai.........

Read full article