You are here: HomeAfricaBBC2023 01 20Article 1698896

BBC Hausa of Friday, 20 January 2023

    

Source: BBC

Wolves za ta dauko Dawson daga West Ham

Craig Dawson Craig Dawson

Wolves ta amince da yarjejeniyar fiye da fan miliyan uku domin daukar dan kwallon West Ham Craig Dawson.

Dan shekaru 32, Dawson ya nuna sha'awarsa ta koma wa buga kwallo a kungiyar ta Wolves.

A watan Oktoban 2020 ne, Dawson ya koma West Ham daga kungiyar West Brom da farko a matsayin aro kafin ya koma Hammers din gaba daya.

Ya buga wasa 87 a West Ham inda ya ci kwallo biyar.

A wani labarin kuma dan kwallon Portugal, Goncalo Guedes ya bar Wolves domin koma wa Benfica a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasan bana.

A bara ne Guedes ya kulla yarjejeniya da Wolves bayan ta dauko shi daga Valencia.

Read full article