You are here: HomeAfricaBBC2022 06 21Article 1566389

BBC Hausa of Tuesday, 21 June 2022

    

Source: BBC

World Cup 2022: Yaushe ne gasar Kofin Duniya kuma me ya sa aka zaɓi Qatar?

Wani dan Qatar mei goyon bayan garin a kwallon kafa Wani dan Qatar mei goyon bayan garin a kwallon kafa

Yanzu mun san wace ƙasa ce za ta kara da wata a gasar Kofin Duniya na wannan shekarar bayan kammala wasannin neman shiga gasar a Qatar da aka yi a birnin Doha na Qatar.

Gasar wadda za a fara a watan Nuwamba mai zuwa, za ta zama ta farko da za a gudanar a nahiyar Gabas ta Tsakiya kuma ta farko a irin wannan lokacin na shekara.

Sai dai, matakin da aka ɗauka na zaɓar Qatar ya tayar da jijiyoyin wuya.

Yaushe za a fara Kofin Duniya na 2022 kuma wane irin yanayin zafi za a fuskanta?

Za a buga wasannin matakan ƙarshe daga 21 ga Nuwamba zuwa 18 ga Dasamba - lokacin da yanayin zafi ke kaiwa 25C a ma'aunin celcius a Qatar.

Da a ce za a buga wasannin a tsakanin Yuni zuwa Yuli, kamar yadda aka saba, za a buga su ne cikin tsananin zafin da ke kaiwa fiye da maki 40C har zuwa 50C.

Tun farko Qatar ta nemi ta gudanar da gasar a lokacin bazara kuma a rufaffun ɗakunan wasa masu na'urar sanyaya wuri, amma daga baya sai aka watsar da batun.

Mece ce matsalar yin gasar a lokacin sanyin hunturu?

Watannin Nuwamba da Disamba cike suke da hada-hada a gasannin ƙasashen Turai ta kulo-kulob kuma 'yan wasa da yawa za su amsa kira don buga wa ƙasashensu wasannin Kofin Duniya a Qatar na 2022.

A gefe guda kuma, gasannin ƙasashe kamar Premier League na Ingila, da La Liga ta Sifaniya, da Serie A ta Italiya, za su dakatar da wasanni mako ɗaya kafin fara gasar. Sai an kammala gasar za su ci gaba da nasu wasannin.

Me ya sa aka zaɓi Qatar a matsayin ƙasar da za a yi Kofin Duniya?

A 2010 ne Qatar ta yi nasarar samun damar karɓar baƙuncin gasar ta hanyar lashe zaɓen da Fifa ta shirya tsakanin mambobinta 22. Ta doke ƙasashen Amurka da Japan da Australia.

Ita ce ƙasar Larabawa ta farko da za ta karɓi baƙuncin gasar.

An zargi Qatar da bai wa jami'an tsaro cin hancin dala miliyan uku da dubu 700 don samun damar, amma an wanke ta bayan gudanar shekara biyu ana bincike.

Shugaban Fifa na lokacin, Sepp Blatter, ya goyi bayan buƙatar Qatar a lokacin amma ya ce da alama Fifa ta yi kuskure.

Yanzu haka Mista Blatter na fuskantar shari'a a kotu a Switzerland bisa zargin zamba da almubazzaranci da sauran tuhumar cin hanci da rashawa.

Kazalika, ƙungiyoyin kare haƙƙi na Amnesty International da Human Rights Watch na zargin Qatar da take haƙƙin ma'aikata 'yan ƙasar waje da ke aikin gina filayen wasannin gasar.

Waɗanne ƙasashe ne za su buga gasar kuma su wane ne ake sa ran za su lashe ta?

Tun shekara uku da suka wuce aka fara wasannin neman shiga Kofin Duniya.

Faransa mai riƙe da kofin a 2018, ta tsallake, amma Italiya mai riƙe da kofin gasar Turai ba ta samu grubi ba.

A wasannin ƙarshe na cancantar shiga gasar da aka buga, an raba tawagogin ƙasashe 32 zuwa rukunin tawaga huɗu. Tawagogin da suka fito daga nahiya ɗaya an raba su da juna - ban da ƙasashen Turai, inda ake iya haɗa ƙasa biyu a rukuni ɗaya.

Ƙasashen Brazil da Ingila da Sifaniya na cikin ƙasashen da ake sa ran za su cinye gasar.

Me magoya bayan ƙwallo za su tsammata a Qatar?

Qatar mai yawan al'umma miliyan 2.9 na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya arziki a duniya saboda arzikin man fetur da gas da take da su.

Ta gina sabbin filayen wasa bakwai kawai saboda gasar, da kuma wani sabon birni da za a buga wasan ƙarshe a cikinsa.

Ana gina sabbin otel sama da 100, da sabuwar tashar jirgin ƙasa da wasu tituna.

Kwamatin shirya gasar ya yi ƙiyasin cewa ana sa ran mutum ɗaya da rabi ne za su halarce ta.

Qatar ƙasar Musulmi ce mai bin addini sau da ƙafa. An gargaɗi magoya baya da su kasance masu ɗa'a.

Akwai dokokin hana shan giya. Ana iya saya ne a manyan otel-otel kawai. Kofi ɗaya na giya kan kai dala 13 - kwatankwacin naira 5,000.

Sai dai masu shirya gasar sun ce za a iya sayar da giyar a wasu keɓantattun wurare na 'yan kallon gasar.

Yaya Qatar ke kallon 'yan luwaɗi da maɗigo?

Luwaɗi da maɗigo haramun ne a Qatar.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin 'yan luwaɗi da maɗigo na ta kiran gwamnatocin ƙasashensu da "su tabbatar musu da kariya", yayin da wasu 'yan kallo daga Wales suka ce za su ƙaurace wa gasar bayan ƙasarsu ta samu gurbi.

Masu gasar Kofin Duniyar sun ba da amsa cewa "ana maraba da kowa", amma Qatar ba za ta sassauta dokokinta ba kan luwaɗi da maɗigo.

Read full article