BBC Hausa of Monday, 30 January 2023
Source: BBC
A ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 ne za a daina amfani da tsofaffin takardun naira na 200 da 500 da kuma 1000 a Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasar Muhammdu Buhari ya bai wa Babban Bankin Najeriya izinin ƙara wa’adin amfani da tsofaffin kuɗin, daga 31 ga watan Janairu, zuwa 10 ga watan Fabrairu.
Sai dai a bin da mutane da dama ba su sani ba shi ne ya za a yi da tsofaffin takardun kudin na Najeriya bayan an daina amfani da su?
Me zai faru da takardun kuɗin bayan 10 ga watan Fabrairu?
Dukkanin bankunan ajiyan kudi na Najeriya za su mayar da tsofaffin kuɗin da suka karba ga Babban Bankin Kasa (CBN), yayin da shi kuma CBN zai mayar masu da kwatankwacin abin da suka kai masa.
Wani masani kan harkar kudi a Najeriya, kuma mai hada-hada a kasuwar hannun jari ta kasar Qasimu Garba Kurfi ya ce “ba dole ne sai CBN ya mayar wa bankunan abin da suka mayar masa da tsabar kuɗi ba amma dai tabbas zai mayar masu da hakikanin jimillar kudin da suka kai.”
Kudaden da CBN ya mayar wa bankunan kasuwancin ne za a ci gaba da amfani da su suna zagayawa a tsakanin al’umma.
Mene ne CBN zai yi da tsofaffin takardun kudin?
Qasimu Garba Kurfi ya ce “bayan CBN ya karbi tsofaffin takardun kudin zai tattara su sannan ya lalata.”
A cewar masanin akwai matakai da babban bankin ke bi wurin ƙididdigewa domin tantance daidai yawan kudin da za a lalata.
"Bayan bin duk matakan da doka ta tanada, babban bankin zai kona ilahirin kudaden ta hanyar tsantseni da kiyayewa domin gudun kowace irin matsala."
A cewar Kurfi, hatta sababbin kudade da aka buga nau’in tsofaffin da za a daina amfani da su, wadanda ba su riga sun fita daga bankuna ba, to su ma wajibi ne a lalata su.
Ya ƙara da cewa a lokacin lalata irin waɗannan kuɗaɗe akan ɗauki matakan tsaro masu tsaurin gaske, ta hanyar amfani da jami’an tsaron sirri da na fili, kamar sojoji da DSS, domin a tabbatar cewa "koda Kobo ɗaya bai salwanta ba balle ya sake komawa hannun al’umma."
Ya ƙara da cewa "shi ya sa ba za a bari koda wani ɓangare na takardar kuɗi ya tsira ba, ba tare da an lalata shi ba."
Ko akwai yiwuwar sake sarrafa takardun kuɗin?
A halin yanzu akan iya sake sarrafa kuɗin da aka yi su da roba (polymer) ne kaɗai - in ji Mustapha Muhammad Garba, tsohon manajan ɗaya daga cikin ressan bankin Unity Bank, a Najeriya.
Ya ce "akan sake sarrafa takardar kuɗin Najeriya kamar naira 50, da 20, da 10, da kuma biyar, amma sauran, kamar naira 100, 200, 500 da kuma 1,000 ana lalata su ne kawai."
Mustapha Garba ya ce a al’adance Babban Bankin Najeriya kan kona kuɗaɗen da suka lalace ko kuma tsufa lokaci zuwa lokaci, kuma a cewarsa, su ma tsofaffin kuɗin da za a daina amfani da su a Najeriya, makomarsu ke nan.
Wane ne ke da alhakin lalata kudi?
Masanan biyu sun tabbatar da cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ne kaɗai doka ta bai wa alhakin kawar da duk wasu kuɗi da a hukumance aka tabbatar sun gama aiki.
Qasim Kurfi ya ce "duk wanda ya kona ko ya lalata kuɗi, in dai ba CBN ba ne to ya yi asarar kuɗinsa, domin CBN ne kawai doka ta bai wa alhakin lalata kuɗi tare da maye gurbinsu da wasu sababbi.’