You are here: HomeAfricaBBC2023 08 27Article 1832807

BBC Hausa of Sunday, 27 August 2023

    

Source: BBC

Yadda Musulmi suka adana kwafin Al-ƙur'ani mafi daɗewa a Afirka ta Kudu

Hoton alama Hoton alama

An gano wani Alƙur'ani da wani limamin ƙasar Indonesiya - da Turawan mulkin mallaka suka kora zuwa yankin kudancin Afirka - ya rubuta da hannu sama da shekaru 200 da suka gabata.

Lamarin ya kasance wani abin alfahari ga Musulman birnin Cape Town - waɗanda suka ci gaba da kula da shi a wani masallaci a gundumar Bo Kaap mai ɗimbin tarihi.

Wasu magina ne suka gano al-ƙur'anin a cikin wata jaka a masallacin 'Auwal' a lokacin da suke ruguza shi a wani ɓangare na gyaran masallacin da ake yi a tsakiyar shekarun 1980.

Masu bincike sun yi imanin cewa Imam Abdullah ibn Qadi Abdus Salaam,, wanda aka fi sani da Tuan Guru, ko 'babban malami' ne ya rubuta Al'qur'anin kafin a kore shi daga tsiburin Tidore zuwa birnin Cape Town a matsayin fursunan siyasa a shekarun 1780, a matsayin hukunci kan laifin goyon bayan kungiyoyin da ke adawa da mulkin mallakar Netherlands.

"Ya yi buɗu-buɗu da ƙura, kamar an yi fiye da shekara 100 ba a shiga masallacin ba," kamar yadda Cassiem Abdullah, mamba a kwamitin masallacin ya shaida wa BBC.

Maginan sun kuma gano wani akwati da ke ɗauke da rubuce-rubucen littafan addini.

''Wani abin mamaki shi ne Qur'anin - wanda ba shi da bango sannan ya ƙunshi wasu shafuka da suka ɓalle daga wuraren da suke - na cikin yanayi mai kyau idan ka buɗe shi'', in ji shi.

An yi amfani da baƙi da jan alƙalami wajen rubuta Alqur'anin.

Babban ƙalubale ga musulman birnin ke fuskanta wajen kare littafin da ya fi kowanne daraja a adininsu shi ne tabbatar da kowane ɓangare na alqur'anin an ajiye shi a wurin da ya dace.

Wannan shi ne aikin da tsohon shugaban majalisar musulmi ta Cape Town Marigayi Maulana Taha Karaan, tare da haɗin gwiwwar wasu malaman addini suka ɗauki lokaci mai tsawo suna yi.

Daga nan ne aka ajiye littafin a masallacin Auwal - wanda Tuan Guru ya gina a matayin masallacin farko a ƙasar Afirka ta Kudu a shekarar 1794.

Yunƙurin sace qur'anin da aka yi har sau uku ya tilasta wa kwamitin masallacin ɓoye shi a wani wuri na musamman da ke cikin masallacin shekara 10 da suka gabata.

Marubucin tarihin Guru, Shafiq Morton, ya yi amanna cewa malamin ya soma rubuta kwafi biyar na farko da hannunsa lokacin da ake tsare da shi a Tsibirin Robben Island - inda aka taɓa tsare fitaccen ɗan fafutukar yaƙi da wariyar al'ummar nan, Nelson Mandela, daga wajajen shekarar 1960 zuwa 1980 - daga ya ci gaba da yi har zuwa lokacin da aka sake shi da kurkukun.

Ana zaton an rubuta galibin waɗannan lokacin da ya ke ɗan tsakanin shekara 80 zuwa 90 da haihuwa, wannan ya zama babban abin al'ajabi ga aikin malamin kasancewa Larabci ba shi ne harshensa na asali ba.

A cewar Mista Morton an tsare Tuang Guru a tsibirin na Robben Islan har sau biyu - na farko a shekarar 1780 zuwa 1781, a lokacin bai wuce shekara 69 da haihuwa ba.

sai kuma a shekarar 1786 da kuma 1791.

"Na yi imanin ɗaya daga dalilan da suka sa shi rubuta kwafin littafin mai tsarki shi ne samar da hanyar ilmantar da mutanensa ilmin addinin musulunci da halin dattako", in ji Mista Murton.

"Idan ka duba ma'ajiyar kayan tarihi ka duba takardar da Turawan Holan suka yi amfani da ita wadda ta yi matuƙar kama da wadda Tuang Guru ya yi amfani da ita a nasa aiki. ko tantama babu iri daya ce.

"Daga itacen gora aka yi alƙalamin da ya yi amfani da shi wajen rubutun. Ita ma tawwadar [taddawa] da ya yi amfani da ita ba ta da wahalar samu daga hannun Turawan mulkin mallaka.

Shaykh OwaisiMalami ne a fannin tarihin Musulunci na Afrika ta Kudu da ya gudanar da bincike mai zurfi akan kwafin Al-ƙur'anin da aka rubuta hannu da a birnin Cape Town, ya yi imanin cewa kwaɗayin tabbatar da ɗorewar Musulunci tsakanin bayi da fursononi Musulmi suka ja hankalin Tuang Guru gudanar da wannan gagarumin aiki, tun a lokacin Turawan mulkin mallaka na Holan.

"Idan har suna yin wa'azi da littafin Bibul domin canzawa fursunonin addini, shi kuma Tuang Guruna can ya na rubuta kwafin littafin mai tsarki, tare da koyar da shi ga ƙananan yara da kuma sa su haddace shi."

"Yana koyar da labarin juriya tare da nuna zurfin ilmin da mutanen suka shiga da shi birnin Cape Town a matsayinsu fursunoni da bayi.

Read full article