BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023
Source: BBC
Idan ana magana ta mutanen da ke son tayar da ƙura a fagen siyasar Najeriya cikin 'yan shekarun nan, Nyesom Wike ba zai kasa shiga sahun gaba-gaba ba.
Tsohon gwamnan jihar na Ribas, wanda ɗan jam'iyyar PDP ne, yanzu haka ya karɓi muƙami a gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya daɗa yin fice a ƙarshen zamanin da yake gwamna, saboda matsayin da ya taka na ɗaya daga cikin manyan 'yan adawan da ke caccakar gwamnatin Buhari da kuma gwagwarmayarsa ta neman shugabancin Najeriya a babbar jam'iyyar adawar ƙasar, wato PDP.
Duk da kasancewarsa a jam'iyyar adawa, an yi imani cewa ya ba da gagarumar gudunmawa ga nasarar zaɓen Tinubu. Don haka, ba abin mamaki ba ne, saka masa da irin wannan babban muƙami.
A ranar Litinin ne, aka rantsar da tsohon gwamnan na jihar Ribas, tare da sauran takwarorinsa sabbin ministoci, kafin ya kama aiki, ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Sai dai, a yayin jawabinsa na fara aiki lokacin da yake ganawa da manyan jami'an ma'aikatarsa ta Babban Birnin Tarayya da kuma 'yan jarida, Wike ya fara sakin kalaman da suka yi matuƙar jan hankalin al'umma, musamman a shafukan sada zumunta.
Kalaman dai sun tunawa mazauna birnin da ayyukan tsohon ministan Abuja, Mallam Nasir El-rufa'i mai halin nuna ba sani, ba sabo, da ɓullo da matakai masu zafi waɗanda suka mayar da birnin kan matsayin da ake alfahari da shi.
Me Wike ya ce?
A lokacin jawabin, Nyesom Wike ya gargaɗi mutanen da suka yi gine-gine ba bisa ƙa'ida ba a babban birnin na Abuja, inda ya ce:
"Idan ka san cewa ka yi gini a inda bai kamata ba, za mu rushe shi. Ko kai minista ne ko ambasada, matuƙar dai ka yi gini a inda bai kamata ba, za mu rushe shi."
Haka kuma ya ce ma'aikatarsa ba za ta lamunci rashin gina filayen da aka saya ba, yana cewa:
"Mutanen da suka ƙi yin gini (a filaye) za su yi asarar filayen nasu."
Bugu da ƙari, sabon ministan na Abuja ya ce za su hana kiwon sake a birnin.
"Za mu haramta kiwon shanu a titunan Abuja, ciyawar da za su ci tana wajen gari, ba a nan ba."
Wike ya ce zai ɗauki waɗannan matakai, kuma babu abin da zai faru: "Zan yi haka, kuma babu abin da zai faru, sama ba za ta faɗo ba."
Tsohon gwamnan na Ribas ya bayyana cewa ya tuntuɓi jam'iyyarsa ta PDP kafin karɓar muƙamin na minista.
Me ƴan Najeriya ke cewa game da kalaman Wike?
Bayan kalaman nasa, ƴan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta sun riƙa tsokaci kan furucin da ya yi.
A nasa tsokacin a shafin X, @ShehuSani cewa ya yi:
The capacity and competence of the new FCT minister to deliver is without doubt.The possibility of getting himself and the President into serious political trouble by his utterances or actions is also without doubt.He will have to learn to walk in a minefield or be blown by it.
— Senator Shehu Sani (@ShehuSani) August 22, 2023
There is no plan for Abuja poor, I hope someone will have the courage to tell Wike that.
— b & 999 others... (@bellorian) August 22, 2023
Wike has taken his autocratic behaviour to Abuja. We will see how far he will go.
— Inibehe Effiong (@InibeheEffiong) August 21, 2023