BBC Hausa of Thursday, 14 September 2023
Source: BBC
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce gwamnatoci biyu da ke gaba da juna a Libya suna aiki tare wajen tsara aikin taimakon mutanen da mummunar ambaliyar ruwa ta faɗa wa a kwana huɗu da ya gabata.
Hukumomin biyu, wadda ke mulkin yammacin ƙasar da kuma mai mulki a gabashi inda bala'in ya afku sakamakon mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama da aka yi wa lakabi da Daniel, suna ta kira ga hukumomi da ƙasashen duniya su agaza.
Ana ta samun ƙaruwar waɗanda suka mutu, bayan sama da dubu biyar da aka tabbatar zuwa yanzu.
Jami'ai na ganin yawan waɗanda bala'in ya hallaka zai iya kaiwa kusan dubu uku.
A ranar Lahadi wannan bala'i na ambaliya da ke kama da Tsunami, ya afka wa ƙasar ta Libya a bangaren gabashi.
Ambaliyar ta haddasa ballewar madatsun ruwa da gadoji a birnin Derna inda lamarin ya fi ta'adi.
Hukumomin ƙasar biyu da ba sa ga maciji da juna, a yanzu sun kawar da wannan gaba inda suka zamanto kamar ciki ɗaya wajen tsara aikin agaji.
Gwamnatin da ke iko da gabashi wadda majalisar ɗinkin duniya ta amince da ita, na dafa wa abokiyar gabar tata da ke gabashi, inda bala'in ya afku.
Hukumomin biyu na ta kira ga ƙasashen duniya da su taimaka, yayin da teku ke ta angizo tarin gawarwakin mutanen da ambaliyar ta hallaka.
Masu aikin agaji na ta faman suturta su, bayan iyalai da 'yan uwa sun gane nasu, ana kuma binne su a manyan ƙaburbura na bai-ɗaya.
Kusan a ko da yaushe ƙaruwar alƙaluman waɗanda suka rasu ake yi, da bayyana ko gano wasu ƙarin gawarwaki, bayan sama da dubu biyar da ɗari uku da aka samu a birnin Derna.
Tauhid Pasha na hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi wa BBC bayani kan yadda gwamnatocin biyu na ƙasar ke aiki tare:
Ya ce, abin mamaki ne a ce, gwamnatocin biyu na kira ga hukumomin duniya suna neman taimako.
Ƙalubalen yanzu shi ne ƙasashen duniya su amsa yadda ya kamata ga buƙatu da kiran na gwamnatocin.’’
Yanzu taimakon ya fara isa a hankali-a hankali birnin Derna da ma sauran wuraren da bala’in ya afka wa.
Bayan aikin tattara waɗanda suka mutu da suturta su akwai na neman masu sauran numfashi, ga kuma waɗanda suka tsira amma ba muhalli.
Ƙungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya, ta Médecins Sans Frontières, ta ce tana fatan tura ayarin ma’aikatanta a ranar Alhamis.
Ƙasashe da hukumomi na ci gaba da alƙawarin taimakawa, yayin da buƙatar taimakon ke ƙara tsananta.
Libya na mia ƙoƙon bararta ga duniya kasancewar ma’aikatan agajin da take da su nata na gida wasu balai’in ya rutsa da su sun rasu.
Kuma ko ba komai girman bala’in ya fi ƙarfin ƙasar musamman ma yadda ake da rabuwar kai tun da farko wajen mulkin ɓangarorin ƙasar biyu na yamma da kuma na gabas.