You are here: HomeAfricaBBC2023 07 20Article 1808804

BBC Hausa of Thursday, 20 July 2023

    

Source: BBC

Yadda cin amana ke rura wutar zanga-zangar Kenya

Wani mei zanga zanga a Nairobi Wani mei zanga zanga a Nairobi

Ƙasar kenya dai ta jajirce wajen gudanar da zanga-zangar adawa kan tsadar rayuwa da ƙarin haraji, lamarin da ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka kashe akalla mutum 24 a ƴan watannin nan.

A lokacin zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a bara, James Wainaina, direban tasi a Nairabo babban birnin ƙasar, ya zaɓi William Ruto, wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗan takarar abin da ya kira 'ƙasar da take fafutika da harkar tattalin arziki'.

Amma yanzu Mista Wainaina yana jin an ci amanarsa kuma yana goyon bayan zanga-zangar.

Tun lokacin da shugaba Ruto ya hau karagar mulki, farashin kayayyaki ke ci gaba da hauhawa yayin da kuma gwamnatinsa ta ƙara haraji.

Mista Ruto ya ce gwamnati na buƙatar ƙarin kuɗi domin biyan basussuka da kuma samar da ayukan yi. To amma ƙarin harajin ya ƙara tsananta rayuwa ga talakawan Kenya.

Diyar Mista Wainaina, wadda dalibar makarantar sakandare ce, ta zauna a gida na tsawon makonni uku kwanan nan saboda ya kasa biyan kudin makaranta shilling 14,000 ($100; £75).

Mista Wainaina ya ce kasuwancinsa ya ragu saboda matsalar tsadar rayuwa.

Cinikinsa ya ragu kuma kusan duk abin da yake samu yanzu yana shiga wajen tabbatar da lafiyar motarsa.

Shekaru biyar da suka gabata, yana iya samun kudi har 4,000 a rana, wanda zai iya biyan bukatunsa na yau da kullun, ciki har da kudin makaranta, in ji shi.

Ya koka da cewa akwai lokacin da yake komawa gida da kudi 500 kacal - wadda ba za ta ishe sayen man fetur da zai saka wa motarsa washegariba -bayan ya sayi wasu abubuwa.

"Wannan lokaci ne mai tsanani gare mu," in ji shi. Gwamnati, ya kara da cewa, ba ta kawo sauki ga kananan ‘yan kasuwa ba, musamman masu “fafutuka” .

Mista Wainaina ya ce karya aka yi musu.

“Da alama abubuwa ba za su gyaru ba, saboda Shugaban kasa ya yi mana karya, ana zaluntarmu, al’amura suna ƙara tabarbarewa, idan kudin man fetur ya tashi, farashin komai zai hau, hatta wutar lantarki, Al'amura suna kara ta'azzara."

Hatta wadanda har yanzu ke goyon bayan gwamnati suna bayyana "mummunar rashin jin dadin yadda al'amura ke gudana", a cewar wani sabon bincike da wani kamfanin zabe na kasar, Tifa ya yi.

Binciken da ta yi ya nuna cewa kashi 56% na ‘yan Kenya na tunanin cewa kasar na tafiya ta hanyar da ba ta dace ba.

Binciken ya sake nuna cewa rashin jin dadin jama’a na iya janyo goyan bayan zanga-zangar da jam’iyyar adawa ta Azimio ta kira karkashin jagorancin Raila Odinga, wanda Mista Ruto ya kayar da shi a bara.

Alkaluman gwamnati sun nuna cewa farashin wasu muhimman kayayyakin abinci ya tashi sosai a cikin watanni 12 zuwa watan Yuni - inda kayan abinci - masara, hatsi da fulawa - ya karu da kashi 30, shinkafa da dankali da kusan kashi 20%, sukari ya kai kusan da kashi 60.

Duk da haka, a cikin kudirin dokar kudi wanda ya zama doka a ranar 1 ga Yuli, gwamnati ta ninka harajin karin kudin man fetur daga kashi 8% zuwa 16%, sannan ta gabatar da harajin gidaje na kashi 1.5 kan ainihin albashin ma'aikata.

Ya kamata harajin ya je wani asusu don gina gidaje ga marasa galihu yayin samar da ayyukan yi.

Bayan haka, harajin tallace-tallace ya ninka sau uku zuwa kashi 3 cikin ɗari na ƙananan ƴan kasuwa, kuma an ɗaga harajin kuɗin shiga na ma'aikata masu karbar albashi mai tsoka daga kashi 30% zuwa 35%.

Gwamnati na kare sabbin harajin - wanda a yanzu kotu ta dakatar da shi na wani dan lokaci - kamar yadda ya cancanta saboda yawan basussukan da ke kan kasar.

An zargin gwamnatin da ta shude da kara yawan basussukan kasar ta hanyar kashe makudan kudi kan ayyukan samar da ababen more rayuwa wadanda ba su taimaka wa talakawan kasar Kenya ba.

Mista Ruto dai ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin da ta gabata, sai dai ya nisanta kansa da ita bayan da ya samu sabani da shugaba Uhuru Kenyatta na lokacin.

Shi da jami’an gwamnati sun shaida wa ‘yan Kenya cewa biyan harajin ‘ sadaukarwa’ ne na gajeren lokaci domin makomar kasar.

Amma Mista Wainaina bai gamsu ba. Hakazalika, Edwin Simiyu, direban babur a garin Kiambu da ke kusa da babban birnin tarayya ya yi nadamar zaben gwamnati mai ci.

“Shugaban kasa ya ce mu ba shi shekara guda sannan mu ga sauye-sauye masu kyau, yanzu da ya fara mulki sai ya canza wakar ya ce mu jira shekaru kafin abubuwa su daidaita, muna shan wahala, an ci amanar mu gaba ɗaya, an manta da mu,” in ji shi.

Charles Kaindo yana aiki tuƙuru a gari ɗaya yana siyar da kayan sawa a kan titi.

Dan kasuwar ya shaida wa BBC da cewa abin takaici ne gwamnati ta karya alkawuran da ta dauka.

Ya ce akwai lokacin da mutane za su ce "ya isa" - yana mai bayanin cewa masu aiki tukuru za su koma aikata laifuka wasu kuma "na iya kashe rayukansu idan wahala ta yi yawa".

Amma ba kowa ba ne ke tunanin cewa ƙarin haraji abu ne mara kyau.

Jane Njeri, wata akanta a kamfanoni masu zaman kansu, ta ce ba ta kishin gwamnati - wadda ke bukatar kudin don biyan dimbin basussukan da ƙasar ke bi.

Shilling na Kenya yana kara yin rauni idan aka kwatanta da dalar Amurka a 'yan watannin nan, abin da ya sa farashin biyan basussukan ya fi yawa.

"Ba zai zama abu na ƙwatsam ba, muna cikin wani yanayi mara dadi, farashin shilling yana ƙasa, ga basussuka da kuma rashin aikin yi," in ji ta.

Tashin hankali a Kenya ya samo asali ne daga alƙawarin saukaka tsadar rayuwa da aka sayar a lokacin kamfen sai kuma aka ga karin haraji akan kayayyakin yau da kullum", a cewar Ken Gichinga. , babban masanin tattalin arziki a kamfanin ba da shawara kan harkokin kasuwanci Mentoria Economics.

Ya ce maimakon mayar da hankali kan harajin da ke ƙara tsadar rayuwa, kamata ya yi gwamnati ta kara kaimi wajen habaka ci gaban kamfanoni masu zaman kansu.

Yana mai cewa ayyukan gidaje na gwamnati da sabon harajin ke biya, yana mai cewa da wuya a warware matsalar gidaje ko kuma matsalar rashin aikin yi.

"saukaka kuɗin ruwa, ƙananan haraji, da sassauta ƙa'idodi. Idan akayi waɗannan ukun, dukan tattalin arzikin za su iya samar da ayyukan yi."

Sai dai mai sharhi kan tattalin arziki Odhiambo Ramogi ya ce yana da yakinin cewa manufar shugaban kasa mai kyau ce - amma hanyoyin da ya bi ne"ba daidai ba".

Ya ce ya kamata gwamnati ta fara rage almubazzaranci kafin ta nemi talakawan Kenya su kara biyan kudade.

Gwamnati ta amince da wannan batu - David Ndii, babban mashawarcinta kan harkokin tattalin arziki, ya amince a shafin Twitter cewa gwamnatin ta yi "barna".

Ndindi Nyoro, shugaban kwamitin kasafin kudin majalisar, ya shaida wa BBC cewa shirin gwamnati na biyan haraji shi ne tabbatar da cewa gwamnati ba ta tona wani babban ramin bashi ta hanyar karbo basassuka ba. Ya ce an fi mayar da hankali ne kan samar da daidaito don tabbatar da abin da "zai kawo sauyi da ci gaba ka 'yan Kenya.

Sai dai da yawa daga cikin 'yan ƙasar ba sa tunanin wannan matakin yana aiki ba wadda hakan yasa suka fito kan tituna don bayyana ra'ayinsu.

Read full article