BBC Hausa of Wednesday, 25 October 2023
Source: BBC
Gargaɗi: Wannan labari na ɗauke da bayanan da za su iya tayar da hankalin mai karatu.
A asibitin Al-Aqsa da ke tsakiyar birnin Gaza, ana fama da ƙarancin likkafanin suturta gawawwaki.
An ajiye gawawwakin a wajen asibitin, a gefe ɗaya ana yi wa mamata sallah, a ɗaya ɓangare kuma iyalai ne ke ta yanke jiki su faɗi da yin jimami.
A cikin asibitin, likitoci na cikin wahala na yi wa waɗanda suka jikkata magani da ceto rayuwarsu - sai dai ana ci gaba da fama da ƙarancin magunguna da kayan buƙatun yau da kullum.
Wakilin sashen Larabci na BBC ya ga wani ɗaki a asbitin cike da mutanen da suka jikkata, inda likitoci ke ta ƙoƙarin kammala jinyar wasu domin zuwa kan wasu da ke jira.
Wasu hotuna da suka fito daga asibitin a ranar Lahadi ba su da kyawun gani.
Yara - ciki har da jarirai biyu - na cikin waɗanda suka mutu.
"Muna nan tun asubahi kuma gawawwaki sun cika ko'ina a wajen asibitin, ƙari ga gawawwakin da ke cikin firiji, ciki da wajen ginin asibitin," a cewar wani jami'in asibitin.
"Ba mu da isasshen likkafanin da za mu suturta gawawwaki saboda suna da yawan gaske. Gawawwakin na zuwa ne sassa-sassa, da kuma gunduwa-gunduwa. Ba za mu iya gane su ba saboda sun lalace."
Ya kwatanta lamarin da "mai tsanani", inda ya ƙara da cewa: "Duk da irin abubuwan da muka gani da farko, ba mu taɓa ganin irin na yanzu ba."
Ana ci gaba da fuskantar irin wannan lamari a sauran asibitoci da ke faɗin yankin yayin da yaƙin Isra'ila da Gaza ya shiga mako na uku.
A asibitin al-Quds da ke yankin Tel al-Hawa na birnin Gaza, bama-bamai sun faɗa kusa da wani gini lokacin da tawagar likitoci 23 da malaman jinya ke yi wa mutum sama da 500 magani, a cewar wani sako daga wani likita a asibitin da aka aika wa BBC.
Marasa lafiya da fararen hula da ke zaman mafaka a asibitin na rayuwa "cikin fargaba", a cewar wani sakon murya da wani likita wanda ba ya so a ambaci sunansa ya aika wa BBC.
Ya kwatanta yanayin da ɓangaren lafiya a yankin ya shiga da "balai," inda likitoci kan yanke shawarar wanda za su fara yi wa magani. Yayin da sauran kuma za su shiga layi.
"Yawancin waɗanda suka jikkata na jira na kwanaki da dama domin duba su," in ji likitan. Wani likitan ƙasar Norway ne kuma ɗan gwagwarmaya, mai suna Mads Gilbert, na tawagar bayar da agaji a ƙasar, ya aiko da sakon muryar likitan.
Jami'an kiwon lafiya sun ce yanayin ya kusa ya fi ƙarfinsu - inda aka kashe wasu yayin da saura kuma suka kasa isa wurin. Ma'aikatan da suka rage yanzu na rayuwa da ƴan gudun hijira 1,200 waɗanda ke zaman mafaka bayan raba su da muhallansu da yaƙin ya yi.
"Akwai mutum 120 da suka samu raunuka daban-daban a nan, mutum goma na ɗakin bayar da kulawa ta musamman, sannan muna da marasa lafiya da suke fama da cutuka guda 400 a asibitin," in ji likitan.
"Akwai kusan mutum 1,200 da yaƙin ya ɗaiɗaita a nan - ba abu ne mai sauki ba ɗaukar mutanen zuwa wani wuri, don haka muka yanke shawarar kula da su a nan."
Isra'ila ta sha nanata gargaɗinta ga illahirin mutane a arewacin Zirin Gaza da su fice zuwa kudancin Wadi Gaza, wani ziri da ke faɗin yankin domin kare lafiyarsu.
Birnin Gaza yana arewacin Wadi Gaza, yayin da birnin Deir al-Balah kuma ke kudanci.
Dubban ɗaruruwan mutane sun tsere zuwa kudancin Gaza, sai dai ƙarin wasu dubbai na ci gaba da zama a gidajensu a arewacin Gazar.
Ma'aikatar lafiya a Gaza da Hamas ke iko, ta ce an kashe gomman mutane a wani sabon hari ta sama na cikin dare a ranar Lahadi.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan wurare sama da 320 a cikin kwana ɗaya da ya wuce, ciki har da wuraren ɓuya da sansanoni da ƙungiyar Hamas da ƙawayenta ta Islamic Jihad ta Falasɗinawa ke amfani da su.
Asibitoci a faɗin Gaza na buƙatar magunguna cikin gaggawa. Tuni ayarin motocin agaji na uku ya samu damar shiga Gaza.
Kafin soma yaƙin, kusan motocin agaji 500 ke shiga Gaza kowace rana, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar agaji ta ActionAid a Falasɗinu.
Duk da cewa ana samun damar kai wasu kayan abinci da magunguna, amma babu man fetur da ya samu shiga tun soma yaƙin.
Asibitoci na samun wuta ne ta hanyar dogaro kan injunan bayar da hasken wutar lantarki.
A ranar Lahadi, Unicef ta yi gargaɗin cewa jarirai 120 da aka saka cikin kwalabe - ciki har da bakwaini 70 da ke ɗakin bayar da kulawa ta musamman - na dogaro ne kan na'urorin da ke amfani da injunan bayar da hasken wuta da ke fitowa daga Isra'ila wanda kuma yanzu ke a katse.
"Muna da jarirai 120 da aka saka cikin kwalabe yanzu, inda muke da bakwaini 70 da ke ɗakin bayar da kulawa ta musamman, kuma a nan ne muke da damuwa matuka," a cewar kakakin Unicef Jonathan Crickx.
Manyan jami'ai cikin dakarun tsaron Isra'ila sun yi iƙirarin cewa Hamas na ɓoye da man fetur domin amfaninta maimakon sanya mafi yawan sa don amfanin fararen hula.
Daraktar ƙungiyar bayar da agaji ta charity Medical Aid a Falasɗinu, Fikr Shalltoot, ta ce an haifi wasu bakwainin ne lokacin da ake tsaka da gwabza faɗa.
"A wani ɗaki da ke cikin asibitin, akwai wata jaririya ƴar makonni 32 wadda likitoci suka ceto bayan hari ya kashe mahaifiyarta," ta faɗa wa BBC. "An kashe mahaifiyar da ɗaukacin iyalansu amma an ceto rayuwar jaririyar."
Ta ce jaririyar da sauran yara da ke cikin ɗakin asibitin, za su iya mutuwa, muddin injunan bayar da hasken wutar lantarki suka daina aiki.
Akwai ƙarancin man fetur da zai sanya injunan su ci gaba da gudana.