BBC Hausa of Wednesday, 7 December 2022
Source: BBC
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, na ƙoƙarin dawo da martabarsa a ƙasar bayan da ɓarayi suka sace wasu maƙudan kuɗaɗe da aka zarge shi da ɓoye wa a gonarsa.
Ya nemi goyon bayan jam'iyyarsa a majalisar dokokin ƙasar, a yayin da tawagar alkalan ƙasar ke ƙoƙarin ƙaryata hujjojin da ƙwararru a fannin shari'a suka bayyana game da batun, a wani gagarumin binciken badaƙalar kuɗi da ya girgiza mulkin Ramaphosa.
Tsohon babban jami'in leƙen asirin ƙasar Arthur Fraser ne ya zargi mista Ramaphosa da masaniyar ɓoye kuɗaɗen sata a gonar tasa.
Mista Fraser ya zargi wani makusancin hadimin shugaba Ramaphosa mai suna Bejani Chauke, da shigo da 'maƙudan daloli' daga ƙasashen Saudiyya da Masar da Morocco da Equatorial Guinea, tare da ɓoye kuɗin a gidansa da ke wajen birnin Johannesburg, kafin daga baya ya ɗauki kuɗin zuwa gonar shugaba Ramaphosa tare da amincewa da kuma yardarsa''.
To amma a wani abu mai kama da fallasa, wasu ɓarayi waɗanda ake zargi na aiki tare da wani ma'aikacin gonar sun sace wasu daga cikin kuɗin.
Inda wasu majiyoyi suka ce abin da ɓarayin suka sata ya kama daga dala miliyan huɗu zuwa dala miliyan takwas.
Waɗannan kuɗaɗe ba komai ba ne, idan aka kwatanta da dala miliyan 20 da mista Fraser ya yi zargin cewa an kai wa wani ɗan ƙasar domin ya ɓoye su - wanda ya ambaci sunansa a lokacin da ya nemi 'yan sanda sun binciki shugaban ƙasar.
A yayin da wasu ke watsi da zarge-zargen da mista Fraser, ya yi wa shugaban ƙasar, tuni wasu hukumomin ƙasar takwas ciki har da babban bankin ƙasar suka fara bincike game da batun.
Mista Ramaphosa, dai ya musanta aikata ba daidai ba, kuma kwamitin ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan shari'a ya ce ba zai iya tabbatar da zarge-zargen ba, a yayin da shugaban ƙasar ke sukar hujjojin da ke ƙunshe a cikin bayanan mista Fraser da cewa shashi-faɗi ne kawai.
Haka shi ma hadimin makusancin shugaban ƙasar Mista Chauke ya musanta zarge-zargen.
A watan Fabrairun 2020 ne dai aka bayyana sace kuɗi kimanin dala 580,000 daga gonar mista Ramaphosa.
A yayin da mista Fraser ke cewa waɗannan kuɗi na daga cikin kuɗaɗen da yake zargin an ɓoye a gonar Ramaphosa, shugaban ya ce sam ba haka batun yake ba.
Domin kuwa a cewarsa wani ɗan kasuwa a Sudan ya zo gonar tasa ranar kirsimetin 2019 inda ya sayi bujimai 20 a hannun manajan gonar, kuma waɗannan kuɗaɗen ne aka sace.
To sai dai ana ci gaba da aza ayar tambaya game da yawan kuɗin da aka sacen, inda ɗaya daga cikin ɓarayin ya shaida wa masu bincike cewa yawan kuɗin da suka sata dala 800,000 ne.
Sannan kuma an ji sautin muryar ɗaya daga cikin masu binciken na cewa adadin kuɗin dala miliyan 20 ne.
Kwamitin da ke bincike kan badaƙalar ya ce "Adadin kuɗin da aka sace daga gonar ya zarta dala 580,000.
Kwamitin ya ce babban mai tsaron mista Ramaphosa Gen Wally Rhoode, ya shirya wata tawaga domin bin diddigin ɓarayin inda aka gano su su a birnin Cape Town a lokacin da suka tsallaka kan iyakar ƙasar zuwa Namibia.
Duk da haka babu wanda aka gurfanar a gaban kotu kan wannan batu, kamar yadda kwamitin da ke binciken ya bayyana.
Haka kuma kwamitin ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa mista Ramaphosa ya nemi taimakon takwaransa na Namibiya Hage Geingob domin kama ɓarayin, sannan Gen Rhoode ya je ƙasar a wani ɓangare na binciken lamarin.
Kwamitin ya ƙara da cewa fadar shugaban Namibiya ta fitar da sanarwa ga manema labarai a farkon wannan shekara tana musanta aikata ba daidai ba daga ɓangaren shugaban ƙasar, to amma ba ta musanta cewa mista Ramaphosa ya nemi taimakonsa ba.
Daɗin daɗawa kuma, kwamitin ya ce shugaban ya yi amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba wajen gudanar da binciken da kansa, tare da neman taimakon shugaban ƙasar Nambiya wajen kama masu laifin.
Kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa za a iya tsige shugaban ƙasar ne kaɗai idan zargin - da ake masa na saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar - ya tabbata.
Magoya bayan mista Ramaphosa dai na fatan cewa hukuncin da babban alkalin ƙasar zai yanke ya yi wa shugaban daɗi.
Kamar yadda a yanzu ba a san inda kuɗin suke ba, rahotonni sun ambato 'yan sandan Namibiya na cewa sun gano asusun ajiyar kuɗaɗen a bankuna da suka yi zargin an ɓoye kuɗin.
Sun kuma ce sun gano gidaje da ababen hawa da suke zargin an saya da kuɗaɗen.
A yayin da mista Fraser ya yi zargin cewa Gen Rhoode ya ƙwato kuɗi a Namibiya, duk kuwa da cewa babban mai tsaron shugaban ƙasar ya musanta batun bincikar kuɗin sata a ƙasar.