You are here: HomeAfricaBBC2022 05 19Article 1541984

BBC Hausa of Thursday, 19 May 2022

    

Source: BBC

Yadda 'mataimakin Shekau' ya mika wuya ga sojojin Najeriya

Abubakar Shekau Abubakar Shekau

Bayanai daga Najeriya sun ce wani jigon kungiyar Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād (JAS), da aka fi sani da ''Boko Haram'', Alhaji Ari-Dafinoma ya miƙa wuya ga jami'an tsaro da ke sintiri a arewa maso gabashin kasar.

Tun bayan mutuwar shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ne ake ta samun ƙaruwar ƴaƴan ƙungiyar da ke mika wuya ga sojojin Najeriyar.

Ana ci gaba da samun bayanai na baya-bayan nan game da batun miƙa wuya da sojojin Najeriya da ake cewa shi wannan jigo na Boko Haram ya yi.

Alhaji Ari-Dafinoma wanda shi ne mataimakin tsohon shugaban ƙungiyar Boko Haram marigayi Abubakar Shekau, ya yanke shawarar miƙa wuyan ne bayan da ƴaƴan ƙungiyar Boko Haram ko ISWAP fiye da 52,000 suka miƙa wuya ga sojojin Najeriya.

Wata majiya ta ce Alhaji Ari-Dafinoma ya miƙa wuyan ne ga dakarun birget na musamman na 21, da ke Bama a jihar Borno, ranar Lahadin da ta gabata.

Majiyar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tilasta masa fitowa daga maɓoyarsa, a wani ɓarin wuta da sojoji suka yi a inda ƴan ƙungiyar suka kafa tungarsu.

Sai dai kuma wata majiyar ta ce wa BBC ƴan ƙungiyar ta Boko Haram ne sun kashe Alhaji Ari-Dafinoma, yayin da suka farga yana aniyar miƙa wuya ga sojojin.

Tun bayan mutuwar jagoran ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ne ake ganin lagon ƙungoyar ya karye, kuma ruɗani ya kutsa cikinta, har wasu daga cikin ƴaƴanta da jigoginta suka shiga miƙa wuyta ga jigogin Najeriya

Amma kuma majiyoyi da dama sun yi ittfaƙi cewa, wani muhimmin dalili da ya tilasta wa Alhaji Ari Dafinoma yake shawarar miƙa wuya, shi ne saboda mummunan faɗan cikin gida da ake gwabzawa, tsakanin ƙungiyar Boko Haram da ɓangaren abokiyar hamayyarta wato ISWAP.

Wannan adadi ya ƙunshi mayaƙan ƙungiyar da mutanen da aka tilasta wa zama dakarun ƙungiyar da kuma iyalansu.

Read full article